KOWANNE BAKIN WUTA

910 29 0
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*



    *93 to 94*




Shiru tayi dan haka ya sake cewa"

    Ko akwai abun  da kike so ne?

   A'a ta fada ahankali"

   OK to sai da safe"

  Kashewa tayi batare da ta amsa ba"

   Wayar yabi da kallo fuskan shi dauke da murmushi"

   Ga dukkan alamu akwai alamun nasara, tunuwa yayi da mgnr Mommy gaskiya inda ace Ummi tana kula dani yadda ya kamata bani da ra ayin tara mata barkatai, Nafisa ma dana ce zan aure tausaya mata nake kawai, ya zama lallai inyi auren kamar yadda Mommy ta fada, Dan Ita Ummi ta fiye son jikinta da yawa"

   Da wannan tunanin bacci ya kwashe shi"

    Washe gari bayan ya tashi aiki ya wuce gidan Su Ummi"

  Umma ya samu afalon bayan ya gaidata ya kara mata ta'aziyar Ahmad "

   Cikin sakin fuska ta amsa sannan taitamai godiya tare da sa mai Albarka"

   Zuwa can ta mike tana kwalawa Ummi kira"

   Ba jimawa ta fito suna hada ido tace"

  Sannu da zuwa yaya"

   Yauwa sannu Ummi ya gida, ya kuma karin hakuri"

  Alhamdulillahi"

   Ido ya zuba mata zuwa can yasake cewa"

   Yanaga kin rame kina tunani ko?

  Sunkuyar da kanta tayi kasa sannan tace"

Bana tunani yaya, zuciyata tafi jin dadi yanzun akan sadda yake garin nan, natsuwa ne dai kasan sai ahankali, karashe mgnr tayi cikin zubuwan hawaye"

   Ajiyan zuciya Abdulmajeed yayi sannan ya tashi ya koma dafda ita ya zauna tare da jawota jikin shi"

    Yana shafa bayan ta yake fadin kiyi hakuri kinji ko, komai mukaddari ne daga Allah, Allah yasa hakan shine mafi alheri"

   Kara fashewa tayi da kuka tana cewa"

  Shine ma yaya"

   Ya isa haka, ki daina kuka, wlh natsana inga kina zubar da hawayen ki, kisan abin da nakeji kuwa?

      Cikin sauri ta kalle shi , acikin zuciyanta tace"

  Gaskiya yaya mutum ne, samun me irin halin sa sai antona, abun da Yaya Abdulmajeed yayi min Mukhtar bazai iya yin irinsa ba, a da na jahilce shi ne kawai, matsalar sa kawai bashi da sakin fuska ne, kafin kaga dariyar sa da wuya, sabanin Mukhtar da ko da yaushe fuskan sa asake take"

   Tana tsaka da wannan tunanin ya dagota daga jikin shi ya kalleta tare da fadin"

   Dan Allah Ummi karki sake zubar da hawayen ki, kiji ko?

   Dakai ta amsa mai, sannan ya sake cewa"

    Wani abu na damun ki?, baki jin ko ina na miki ciwo?

    Kai ta sake daga mai alamar eh"

   Ki bude baki kiyi min magana mana"

    Ba inda ke min ciwo"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now