KOWANNE BAKIN WUTA page 7 to 8

2.2K 109 3
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido


                7-8


🔥"Sararawa Sadiq yayi da dariyar sannan yace"

   "Kai! amman wannan abu yamin dadi wallahi, kai da hadadun babys kebi kana musu yanga, yau sai kagaka kana makerketa, inda nasan hakane ma ai bazan baka magani ba wallahi, barinka zanyi kai tayi ina kwasan dariya"

     "Hmmm Majeed ya fada sannan ya kalli Sadiq yace"

    "Narasa yadda a kayi nafara son yariyar nan, hakanan na tsinci kaina ahaka"

" Murmushi Sadiq yayi sannan yace"

    Kasan Allah, mucire zancen wasa, tunda har kaji kanason yariyar nan kawai ka sameta  ka gaya mata kana sonta"

    Allah ya kiyaye wlh, bata isaba,, tayi kadan, inagaya maka gaban iyayen mu ta fashe da kuka tanacewa ita bata sona, dan me ni zan nace ina sonta?

   " Toh kar kace, ka xauna a daura mata aure da Mukutar din"

      "Wani irin kallo Abdulmajeed ya wurga mai, sannan yace karka sake kiramin wannan sunan, danji nake tamkar kana watsamin wuta wlh"

    "Bazan bariba, ai sunan kanina ne mukutar, ka isa ka hanani kira ne?

     "Tsaki Abdulmajeed yaja tare da fadin"

    "Tsaya na sauka, Abdulmajeed ya fada cikin fushi"

   " Banza dashi Sadiq yayi yacigaba da tukinsa dan haka Abdulmajeed ya kama sitiyarin motar"

   " Tangal2 suka fara atiti dan haka cikin rudewa Sadiq yace Abdulmajeed meye haka ?, wai kashemu zakayi?, ganin baya sauraranshi yasa ya matsa gefen hanya ya tsaya"

    "Budewa Abdulmajeed yayi ya fice, cikin tsanani fushi tare da yanayin dake nuna ya fusata sosai"

"Gaba yayi abinshi, ganin inda jikinshi ke rawa yasa Sadiq yaji bazai iya barinshi agurin ba, dan haka ya kara binshi da mota, sannan ya sakko tare da fadin"

        "Yi hakuri kazo mu karasa, kaga baka da Lafiya"

     "Bazan hauba, dan tsabar wulakanci ina gaya maka abin da nakeji  ajikina ka maida abin wasa"

    "Murmushi Sadiq yayi tare da fadin"

  " Shine nace ai kayi hakuri nabari ko?, hannun shi ya jawo sannan ya bude mishi motar ya zauna"

    "Har suka isa gida basu kara Magana ba, har cikin dakinsa yakaisa sannan ya koma Office"

    "  Hassana ce kema Momy gulman taga Sadiq ya dawo da yaya Abdulmajeed gida, kuma taga kamar bashi da Lafiya dan haka Momy ta nufi dakin"

     " Acikin bargo ta sameshi har yanzun jikin shi rawa yake yi"

     "Zama tayi abakin gadon tare da kiran sunan shi"

   " Amsawa yayi batare da ya fito da kansa ba, dan haka Momy ta jaye bargon daga fuskan shi tare da fadin"

   " Meke damun ka?

    " Zazzabi ne Momy"

    " Zazzabi kuma Majeed?, wani abu na damunka ne?

   " Girgiza kai yayi tare da fadin a'a"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now