page 30

120 9 4
                                    

🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*

🕳 *30* 🕳

بسم الله الرحمن الر حيم



Ɗakin Mami na shige nai zamana muna kallon *Sunnah tv* ana hasko wa'azin *Kabir Gwambe*, sai ƙarfe goma da rabi na koma ɗakina na kulle nai shirin kwanciya na baje a gado, wayata na ɗauko na kunna Data na hau whatsapp.

Kamar dama yana jirana sai kawai naga saƙon Labid, sallama yai mun kamar ko yaushe na amsa ya kuma tambayar bakiyi bacci ba?

Na ce yanzu dai nake shirin yi, muka ɗanyi shiru zuwa can yace, kiyi haƙuri fa da abinda ya faru ɗazu, bansan taya hakan ta kasance ba dan bada wannan niyyar na shigo ba, dan Allah kiyi haƙuri, naja numfashi na maida mai amsar ya wuce, amma da Allah kada wannan rainin ya sake faruwa..

Ni kayi mun yarinyata da irin wannan mu'amular gaskiya, yace hmmmm mubar maganar dai nace kiyi haƙuri, amma ina son ki gane wani abu Asiyah, ita mace komin girmanta bata ma namiji girma, namiji kuma baima mace yarinta, so pls ki cire wannan aƙidar aranki, in Allah ya nufa yaron zaki aura fa, yaron ma kuma tsaranki da kuke shekaru ɗaya ku....na yi salati ina neman tsari da kalamanshi.

Cikin ɓacin rai nace na lura ɓata mun rai kake neman yi cikin daren nan, ɗazu ka zo ka tsotse mun baki ka haɗa ƙirjina da wannan small ƙirjin naka dan rashin kunya, yanzu kuma kana man fatan auren ƙaramin yaro, ni sai da safe kaji zan kwanta bacci nake ji.

Ban jira ya bani amsa ba na sauka na kashe Data nai kwanciyata..

Tun daga ranar sai na fara sha mashi mur, babu dai wanda ya fahimce mu a gidan, in muna zaune gaba ɗaya a falo, suna fira mu kuma muna chattin da juna duk da cewa gaba ɗaya muna zaune a falon, inya faɗi wata kalmar sai na ɗago na fakaici idanuwansu Mami na banka mashi harara shi kuma ya yi murmushi kawai.

Ya rubutu mun kinsan wani abu Asiyah? Ban bashi amsa ba yaci gaba da cewa, ni fa wallahi na kasa mance wannan sumbar, yanzu haka ma kwaɗayin sake tsotsar bakinki nake, na ɗago ido na tsura mashi su cikin mamakinshi, ya kashe mani nashi na taɓe baki ban bashi amsa ba, ya kuma cewa inajin fa sai dai kiyi haƙuri wallahi kamar na kamu da sonki Asiyah.

Zuciyata tayi wani irin bugawa, kawai sai na kashe Data na aje wayar gefe muka soma firar film ɗin da muke kallo a falon, naƙi yadda ko ƙara kallonshi nayi, sai ya turo man text da cewa ki koma mana muci gaba da firarmu, na watsa mashi harara yayi murmushi kawai yana girgiza kai.

Tun daga lokacin sai Labid ya koma tsokanata da maganar so, dana fahimci tsokana ce sai na saki jikina muka koma kamar da.

Kwana huɗu da zuwanshi yai mun rakiya zuwa bakin kasuwar unguwar, aƙafa muke tafiyarmu da yamma munata firarmu cikin nishaɗi, nake bashi labarin Usman yace yana dawowa zai turo magabatanshi a fara maganar aure.

Labid ya kalleni cikin wani tashin hankali daya shiga alakacin jin maganata, amma kuma sai yai saurin dai-daita natsuwarshi, sai kawai naga yaja hannuna munyi gefen wani gida dake da wani dutse mai faɗi muka zauna, na kalleshi ina faɗin ka gashi da tafiya ko?

Ya ɗanyi murmushin yaƙe yace muɗan huta saimu ƙarasa, mun ɗanyi shiru muna kallon mutane masu wucewa duk da layin na ƴan gayu ne ba yawaitar jama'a sosai, Asiyah! Naji ya kira sunana cikin natsuwa.

HALIN DANA SHIGA...Donde viven las historias. Descúbrelo ahora