page 23

89 5 0
                                    

🤳🏻

🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*


💘 *23* 💘


بسم الله الرحمن الر حيم




Na fito falo bisa tirsasawar da Mami taimin, wanda harya kaita da nuna min ɓacin ranta ta hnayar yi mani kaca-kaca (faɗa), har da zagi aranar nan dukana ne kawai Mami ba tayi ba...

Ita duk cikin al'amarin bata ganin laifin kowa sai nawa, abinda ta rinƙa cewa wai da gangan na mayar da kaina sakarya har akemin irin haka, ta ɗora da cewa, in banda kina sakarya mara tunani mai zaisa anyi na farko kin gano shiri ne har kuma ki yadda aƙara shirya maki wani irinshi ki hau kai ki zauna.

Yanzu kuma danta bayyana irin wancan ne sai ki zo kisa mutane gaba da nukura kinajin haushinmu kamar mun kashe maki Uba..to wallahi ki kiyayeni ki cire wannan maganar aranki ki shiga cikin ƴan'uwanki, inba haka ba zanyi mugun saɓa maki acikin gidan nan.

Faɗan Mami shiya razana ni, dan ban saba jin irin haka daga wajenta ba, dan haka na fito falon duk da cewa ban sake ba amma na zauna acikinsu muna kallo wanda agareni babu abinda nake fahimta sai saƙe-saƙe nake cikin raina.

Abubakar ne ya kirani awaya yana faɗamin na sameshi awaje yana jirana, na miƙe tsam dama zaman falon ya isheni, na iskeshi jingine jikin mota amma bashi ɗaya bane su uku ne sauran ban sansu ba..

Ya kalleni da kyau yace meya sameki haka Asiyah kinga kau yadda kika koma ne? Uhm kawai nace mishi.

Ba dai maganar Saleem ke damunki ba ko?

Kawai sai naji hawaye sun zubo min [To tayama za ai ace ba zan damu da wannan *halin dana shiga ba*], ya matso kusa dani shima ga shiga damuwar yace banga abun tayar da hankali ba anan Asiyah, kamata yayi ki mance da antaɓa makamanciyar magana irin haka, inya so sai kiyi ƙoƙarin kiyaye gaba kar irin haka ta sake faruwa.

Amma ya ake so nayi da zuciyata Abubakar?

Yayi shiru yana kallona, naci gaba da faɗin anraunana min zuciyata Abubakar, ansamin damuwa irin wacce ba zata taɓa barina ba, kayi tunani kaga shekara nawa ina fama da abu ɗaya, kuma aƙarshe duk adawo acemin abun nan ba haka bane, saboda Allah ya akeso nayi da rayuwata ina ake so nasa kaina..

Ancika min zuciyata da son gaibu, ina ake son nakai zuciyata data cika sonshi Abubakar ka duba al'amarina mana..kuka yaci ƙarfina na kifa kai ajikin mota naci gaba da rera kukana, ni nama mance da cewa sam Abubakar bashi ɗaya bane awajen.

Gefen kunnena naji maganarshi hakan yasa na fahimci ya matso kusana sosai, yace ya isa haka mana Asiyah, na tada kai na kalleshi yanayinshi duk damuwa da tausayi sun cika fuskarshi, sai kuma ƴar kunya ta kamani ganin mutane biyu sun samin ido suna kallona da alamar tausayi, n agoge hawayen na gyara tsayuwata i a fuskantar Abubakar dake magana...

Dama Saleem ne ya matsa na kawoshi wajanki yai maki bayani akan abubuwan da suka faru tare da baki haƙuri, yaimin nuni dashi da hannu.

Na kafa mashi ido wanda tashi ɗaya naji duk duniya babu wanda na tsana irin Saleem, dalilin abinda yaimin alhalin bai sanni ba, bai taɓa ganina ba, baisan inda nake ba kawai...

Ya gama dogon bayaninshi wanda dama nasan daga ƙarshe *Abdul ne* ya sashi, amma duk da haka banajin zan iya yafe mashi tunda dashi aka haɗa baki aka cuceni.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now