page 17

81 4 0
                                    

🤳🏻

⏳🕹⏳🕹⏳🕹
нalιn dana ѕнιga...
⏳🕹⏳🕹⏳🕹

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*


💘 *17* 💘

بسم الله الرحمن الر حيم




Al'amuran sunci gaba da tafiya komai na zuws ya wuce yayinda akowanne lokaci rayuwa cikin jin daɗi da kwanciyar hankali shine abinda kowanne rai yake buƙata.

Tsayin shekaru uku kenan Abbanmu na cikin wannan hali na matsalar kwakwalwa, mu zuri'arshi tun abin na damunmu yana ɗaga mana hankali to zuwa yanzu dai mun saduda mun kwantar da hankali mun zubawa sarautar Allah ido.

*Hukuncin Ubangiji*

Misalin huɗu da rabi na agogon ƙasar da nake, na isa asibitin da mahaifina ke jinya, mun fara gaisawa da likitan da alhakin kulawa da Abbah ke dashi wanda kai tsaye na wuce ɗakin da yake..

Ɗakine ƙwatacce tamkar kana gidanka, an gyareshi da farin gado irin na asibiti, a shinfiɗe aƙasa kafet ne mai taushin gaske akwai ɗanƙaramin fridge da tv harda computer da drower aje kaya irin na abinci.

Da sallamata na shiga ɗakin, Abbana kishinɗe kan kafet yana fuskantar gabas, sallamata yasashi juyowa fuskarshi ɗauke da murmushi yana kallona, na ƙarasa inda yake na tsugunna gabanshi, tun kafin nai magana yace sannunda ƙoƙari Asiyah..

Maganar tashi tai matuƙar bani mamaki, domin tsayin shekarun da ya yi a asibiti bai taɓa magana ta hankali irin wannan ba, balle har ya gane waye ma ke tare dashi koko in mutane sunyi yawa awaje ya ban-bance waye wannan waye wancan, kai akwai lokacin dako mace da namiji baya bambamcewa amma wai yau harma ya gane ni ce Asiyah.
Nai saurin gyara zama agabanshi idona har ya kawo ruwa na kamo hannayenshi na ce ka ganeni ne Abbah ka tunani?.

Ya juya kai yana dariya na ganeki mana Asiyata, ya za'ayi na saka ganeki, wayyo daɗi kuka ya kufce min na kifa kai cinyarshi ina shirgar kukana wanda kai kanka mai karatu kasan kukan farin ciki ne.

Tsayin lokaci ina kuka na Abbah yana lallashina yana cewa aiba abin kuka bane Asiyah, ashe ba dariya zakiyi ba ki godewa Allah Abbanki ya sami lafiya, na girgiza kai Abbah farin cikine yai min yawa, Abbah harna rasa abinda zanyi, ya sake darawa yace sai aiwa Allah godiya..

Likitanshi ya shigo yanda ya ganmu yai dariya yace na yadda lallai in farin ciki yai yawa yanasa kuka musammam in an haɗu da 'ya'yan shagwaɓa irinki, na ɗago ina dariya na dubi likitan na ce Doctor farin ciki yau yasa harna rasa inda zansa kaina, ya sakeyin dariya saiki turashi ƙasan gado ya nuna gadon da gatse..

Har Abbah muka sanya dariya, na zauna sosai bayan Dr ya zauna gefen gado ina kallonshi na ce mun gaisa tun a waje amma maimakon ka fara bani labari mai daɗi saika ƙyaleni, dama naso na baki *Suprise* ne, mukai dariya nan ya soma bani labarin yadda abin ya kasance..

Ya shigo da daddare dan bashi magani da allurai sai ya tadda Abban zaune yana kalle-kalle, kamin likitan yai magana Abbah ya fara tambayarshi a ina yake, cikin mamaki yace mai kana asibiti ne Abbah yace asibiti me nakeyi?

Ka sami ƴar lalura ne likitan ya bashi amsa, sai Abban bai sake tambayarshi ba sai dai ya mayar da kai ƙasa alamar tunani yake, lokaci mai tsawo ya sake ɗagowa ya tambayi tun tsawon lokacin da yake tare dasu, ya bashi amsa shekara uku, yace, a ido Abbah ya nuna mamakin jin daɗewar da yayi sai dai bai sake magana ba har gama mashi allaura da bashi magani sukai sallama.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now