page 24

138 6 0
                                    

🤳🏻

🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*


🕳 *24* 🕳


بسم الله الرحمن الر حيم




*2009/2010*

{ *Sabon Salo*}

A cikin watan *December* ne na shekarar *2009* na shiga *social media* fannin *Facebook* da wata wayata *Nokia E-Series* mai ruwan makuba wato marron, shekaruna na haihuwa 28 da sauran kwanaki ma kafin su cike cif...

Zuwa wannan lokacin abubuwa masu tarin yawa sun faru sun wuce, cikinsu hadda tashin Anti Lubah daga kaduna sukayi ƙaura zuwa kano dan dama ƴan can ne, sai kuma auren ƙanwata Ruƙayya da akayi shekarar data wuce, Bashir da Abbas sunyi aure amma Abdul yana nan zaune har yau ba auren, har kuma zuwa yanzu ba jituwar kirki atsakanina dashi.

Ya yi magiyar ya yi roƙon na yafe mashi naƙi ko kulawa dashi, daga baya ma na taka mai birki da cewa yana sake kulani zan janyo mashi sharrin daba gidanmu kaɗai ba har garin sai ya gagareshi zama, ganin da gaske nake yasa ya shafa min lafiya muka koma zaman kowa tashi ta fissheshi...

Nayi kewar Anti Lubah naji rashin daɗin tashinta ba kaɗan ba, sai na sake komawa wata *so silent* dani, gashi Abbah ya hanani samun aiki wai duk ranar da nai aure in mijin ya yadda sai inyi...

Ni kuwa gashi abun kamar sihiri ba kowa mai nemana ahalin yanzu sai Abubakar daya zame min kamar wani ɗan'uwana dan mun shaƙu sosai duk da cewa age mate ɗina ne amma n asake dashi mun zama tamkar ƴan uwan juna.

Rashin jin daɗin rayuwar yasa na buɗe account da facebook, sai gashi kuma kamin kace me na samu friends masu tarin yawa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, kunsan maza su dai suka mace fara mai kyau to yanzun nan zasu rikice kowa yana son yayi mu'amula da kai, kowa su yake ace ya sanka ko ke ɗin friend ɗinshi ce, na samu farin jinin facebook fiye da zato na, shiyasa inna shige ɗaki na hau kan network sai na kwashe aƙalla awa biyar ina chatting da maza da matan.

Yau ma ina cikin chatting da wani ɗan ƙasar Qatar inata dariya ni ɗaya domin dai shi baijin turanci sosai haka nima bana jin larabci, sai dimiya muke duk mun kasa fahimtar juna, na gaji nace mai ina busy sai latter, har zan sauka cikin irin mutanen da ake watso maka in kana son adding as friend naga wani matashin namiji da aƙalla zai bani shekara takwas zuwa goma, kenan ba zai wuce irin talatin da shidda zuwa da takwas ba..

Fari ne ƙal siriri dogo mai dogon hanci da ƙaramin baki, sai kunnuwa fala-fala irin na nasara, nan da nan zuciyata ta harba naji wani irin abu ya ziyarci ilahirin jikina, domin dai irin namijin dana jima ina nema ne ido arufe, gashi fari mai kyau sannan kuma mai shekaru ba yaro ba..

Kawai sai na samu kaina da aika mashi da friend requst, sannna na shiga cikin profile ɗinshi ina kallon hotunan daya sanya, hotuna ne birjit tun daga na ƙasashen waje har zuwa nan gida Nigeria, da alama ma a ƙasar Malaysia yayi karatu, lokaci guda wata irin soyayyarshi ta shiga dukkan rayuwata, irin soyayyar da ban taɓa ji ba, ko Ibraheem banji haka daga gareshi, na kai dubana ga sunanshi naga ya sanya *Ahmed Ali* .

Ban tashi daga kan hotunanshi ba naga ya yi accepting ɗina as friend, dan haka haka na koma ta fannin massage na rubut mashi *"Thanks for accepting"* ya maido da amsar you're welcome, daga ƙananun fira ce muka shiga yi duk da cewa ba komai yake amsani ba, amma ni hakan ma ya yi mani, sannan kuma sam bana jin haujin hakan dan na riga na afka tarkonshi nayi tsunɗum..

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now