page 19

92 4 0
                                    

🤳🏻

⏳🕹⏳🕹⏳🕹
нalιn dana ѕнιga...
⏳🕹⏳🕹⏳🕹

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*


💘 *19* 💘

بسم الله الرحمن الر حيم




Rayuwa agida ta zamo abar birgewa agareni dan ina tafiyar da ita cikin kwanciyar hankali, bani tare da damuwa bani tare da matsala hankalina kwnace, na sake na wataya da iyayena da ƴan uwana, ga tallafin so ƙauna da nake samu daga abin sona, duk da cewa bamu tare amma akoyaushe ƙaunar junanmu naƙara zafafa ne azukatanmu.

Naso na fara zuwa aiki tun baifi wata ɗaya da dawowata ba amma Abbah ya hana wai sai agidan mijina ban damu ba da yace hakan musamman da naga har zuwa lokacin baifara matsamin akan na kawo miji ba..

Amma fa ako yaushe ahirarshi zaice in zan aurar da Asiyah ko yace auran Asiyah za'ayi abu kaza da kaza da dai ire-iren haka, wanda wannan alamace dake nuna cewa kwarai Abbah amatse yake yaga ya aurar dani, dan hakane nake cewa Ibraheem ina tsoranfa kar Abbah ya tasomin lokaci ɗaya da maganar kawo miji, nasan ba zaiji uzrina ba alokacin meyiwuwa ma yace zai bayar dani ga wanda yaga dama..

Ya kance insha Allahu kamin lokacin da hakan zai faru ina tare dake wanda ƙilama kina ƙarƙashin kulawata ne alokacin, na kanji daɗin kalamanshi na ce na damu da kai da yawa Ibraheem, ina ƙauna da burin kasancewa da kai..

Na fiki burin son ganin munkasance tare da juna, babban burina ace yau muna ƙarƙashin inuwa ɗaya muna kulawa da juna tare da...uhm naja numfashi da ƴar dariya..ina sonki da yawa Asiyah ina muraɗin kasancewa tare dake ina burin ace akoda yaushe nine kusa dake, kamar yadda nasan akoda yaushe nine manne cikin zuciyarki.

***

Da daddare ina tare dasu Hashim agidanshi ana gobe sunan ɗiyar da matarshi Saudatu ta haifa(haihuwarsu ta fari kenan) tare da ƴan uwan Saudat ɗin dani dasu Fareeda munata shirye-shiryen gobe suna.

Yaro ya shigo da sallama wai ana neman Asiyah awaje, na dubeshi da mamaki danni bansan kowa a Unguwar ba balle ace har ana nemana, na tambayi yaron me yace sunanshi?

Ya juya kai da faɗin bai faɗa ba, nai dum kmaar bana jeba amma ƴan wajen suka matsa akan na fita mana naga ko waye, Fareedah ta ɗora da cewa ƙilama wanda kika shekara da shekaru kina son gani ne, faɗar hakan ya faɗar min da gaba dan nasaɓ hakan na iya faruwa.

Nai saurin miƙewa na sami gyale ɓa rufa jikina nabi bayan yaron...

kallo ɗaya naiwa baƙon nasan cewa wannan ba Ibraheem ɗina bane, nan naji raina ya ɓaci kamar na juya sai naji yana cewa aimin adalci mana malama Asiyah, na tsaya ina kallonshi ya gyara tsayiwarshi gabana ya soma magana anatse.

Duk wanda ya biyoki har inda kike ya sanki kenan ya kuma damu da al'amarinki yana kuma burin ƙulla wani abu mai muhimmanci dake ne, dan haka karki mamakin ganina awajanki abinda kawai nake so dake ki fahimceni muyi magana irinta fahimta, kisan madosana nasan inda kika nufa...ina fatan kin fahimceni?

Na kalleshi kaɗan na ɗauke kai haka kawai naji ban iya mashi wulaƙanci dan haka na ɗage kai da faɗin ina jinka, ya gyara tsayiwa Asiyah banzo gareki da siffar wasa ba magana ɗaya ce takawoni ita ce ƙauna babban burina ayau naga na mallakeki ta hanyar aure, nai mashi wani irin kallo mai ɗauke da alamomi da yawa.

Bai damu da irin kallon da nake mishi ba yaci gaba da magana, kamin nazo gareki sai da na kama bincike da nazari akanki, na gamsu da halayenki na gamsu da ɗabi'unki na yadda da al'amuranki dan hakane tuni na gama yankewa kaina shawara kece abokiyar rayuwata ta din..din..din kece wacce na zaɓa ki zamo matata mai kare daraja da mutuncina mai kula da biyan buƙatuna, na kuma yadda dake ki zamo abokiyar sirrina mai riƙe amanata ki zamo Uwar 'ya'yana mai basu tarbiya ta gari...Asiyah ina da burin kasancewa tare dake cikin lokaci ƙanƙani...amma me kikace game dani?

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now