page 28

87 8 0
                                    

🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*



🕳 *28* 🕳



بسم الله الرحمن الر حيم


*Halin dana shiga* kenan tsakani na da Ahmad, duk lokacin daya zo kaduna ya sauka a hotel ɗinshi zai kirani ya tumurmusa ya maido ni gida, anyi haka wajen sau huɗu kenan, ta biyar ɗince muna kwance kaina a ƙirjinshi nake ce mai, Ahmad wai sai yaushe zaka soma sona harka aure ni?

Wata bazawarar dariya ya yi yana shafa gashin kaina kafin yace, in Allah ya yi ke matata ce fa Asiyah babu makawa sai na aureki, amma maganar gaskiya ni bana hango yiwuwar aure na ahalin yanzu, akwai abubuwa masu tarin yawa agabana, sannn ko zan aureki sai bayan na auri Rahma tukunna, kici gaba da addu'a komai zai yi dai-dai da yardar Allah.

Daga haka ya miƙe ya shige kewaye domin wanka ya barni cikin dogon nazari da tunanin wannan rayuwar, yana fitowa nima na shige na kintsa kaina, lokacin dana fito yana tsaye gaban madubi cikin ƙananun kayan da sukayi matuƙar amsarshi, sai ya koma kamar wani balaraben lebonon, wata irin ƙaunarshi ta ɗinga fisgata naje nasha gabanshi kafin nasa hannu na rungumoshi muna kallon juna.

A hankali na furta ina ƙaunarka Ahmad, ina son ka irin son da zan kasance cikin ko wane irin hali inde kana tare dani, amma kuma duk nasan mafarki nakeyi ba zamu taɓa kasancewa tare ba, ya kawo fuskarshi kan tawa ya sumbaci lips ɗina yana faɗin ki daina ja da ikon Allah Asiyah...

Kika sani ko niɗinne mijinki, na girgiza kai hawaye na taruwa a idona, Ahmad zaka soni koba yanzu ba, da bakinka zaka gaya mun kana sona insha Allah, ni kuma nayi maka alƙawarin duk ranar dakace kana sona aranar zamu rabu rabuwa ta har abada, dariya ya yi yana jn hancina zumuwata kenan, kina da abin dariya, muje na maidaki gida kada yamma ta ƙara yi.

***

Bayan kwana biyu da yin haka Bashir ya zo da wani matashin saurayi wanda inajin shekarunmu ɗaya, wai ƙanin wani abokinshi ne wata ƴar hidima ce ta kawo shi garin, basu san kowa ba shine yai ma Abbah magana zai zauna can ɓarayinsu kafin ya gama, nikam maganar sama-sama najita dan ban tsaya ba balle naji da kyau.

Kallo guda naima saurayi na watsar dan harga Allah baimin ba, siriri ne mai ɗan tsayi, duk ba wannan ya sani takaici ba sai ganinshi baƙiƙƙirin irin baƙin nan mai shaining, nan da nan sai naji kyamarshi ta kamani.

Amma wani abun makaki cikin kwanaki kaɗan naga mutanen gidan sun soma sabawa dashi, dan ba ƙarya yaron akwai ladabi ma na gaba dashi, watanni biyu suka shuɗe naga sunyi wani mugun sabo da Rabi'atu, a hankali ya soma shigowa falo suna taɓa hira tsakaninshi dasu Mami, ni ce dai har yau ko sannu bata taɓa haɗani dashi ba, danna fahimci ɗan girman kaine, yana da jin kanshi sosai, abinda ke ƙara sanya mani takaicinshi kenan, araina na ce dalla ji wannan baƙin yaron, ko ubanwa yake ɗaga ma kai oho!.

Bai da labarin yadda na tsani baƙin namiji baya bani sha'awa baya birgeni, baki ma kuma irin nashi wanda ina jin sai a can ƙasar *Senegal* za'a samu ire-irenshi, anya ma kuwa bai haɗa jini dasu ba?

Gashi da shegen girman kai da ɗaukar kanshi wata tsiya can, ni bani fatan ma ko hanya ta haɗamu balle magana, dan haka na soma kiyaye duk wata hanya da zata iya haɗmu, dama kuma ni ba ma'abociya zaman falo bace inhar Abbah baya gari nafi keɓe kaina aɗaki inta chatting a facebook aikina kenan.

Sai da muka kwashi tsawon wata uku Ahmad bai zo kaduna ba, na kuma daina kiranshi awaya sai shi lokaci-lokaci yakan kirani, muna yawan chatting dai.

Ina zaune a ɗakina da safe naga kiran Ahmad ya shigo, na ɗaga muka gaisa ya gaya mani ya shigo gari, dan haka na tashi na sheƙa wanka na shirya na shirya ma Mami ƙarya kamar koda yaushe na fice inda Ahmad yayi masauki, wannan karon kam bayan romance ba abinda ya faru tsakaninmu saboda ina period, dan haka ban jima ba nace mai zan koma.

Kamar kullum shiya saukeni alayinmu, na motsa da niyyar fita yayi saurin riƙo man hannu yana murzawa, shiru yayi na ɗan wani lokaci kafin yace kin tuna wata magana da kika gaya mani Asiyah?

Kin taɓa ceman zan soki toh maganar dai ta tabbata, Asiyah ni Ahmad Ali ina sonki ina ƙaunarki ina muraɗin aurenki inkin amince mani, nayi shiru lokaci mai tsawo wasu al'amura suna ziyartar jikina, zuwa can na sauke ajiyar zuciya ina murmushin baƙin ciki kafin nace, masha Allah na gode ma Allah daya nuna mani wannan rana nan kusa, Ahmad ina sonka nafi kowa ƙaunar aurenka, ina maka wani irin so wanda bansan yanda zan fassara shi ba, amma kuma ina mai takaicin rashin kasancewar mu tare..

In baka mance ba nayi maka alƙawarin duk ranar daka furta kalmar so a gareni ni kuma zan rabuda kai, Ahmad ayau ni Asiyah na rabuda kai badan bani sonka ba sai dan wasu dalilai masu ƙarfi, amma ka sani ina sonka zuciyata gaba ɗaya ahalin yanzu tana cike da ƙaunarka sai dai bazan iya aurenka ba..

Na gode da ƙaunarka gareni, sannan kuma duk lokacin daka zo kaduna ina maraba da kai ka zo mu gaisa a ƙofar gidan ubana dan ba zan sake binka ko ina ba, daga haka na buɗe motar na fice na barshi sake da baki yana mamakina.

A wannan dare na shaƙi kukan rabuwa da Ahmad, nasan za'ayi matuƙar mamakin abinda yasa na rabuda dashi duk kuwa da tarin son shi da nake, na farko dai yadda nake ƙaunar Ahmad kona aure shi ba komai zai ƙareni ba sai tarin baƙin ciki da rayuwar ƙunci, danna san ba zan taɓa iya jayayya dashi ba, ba zan taɓa iya ƙwatar ma kaina ƴanci ba awajenshi, duk abinda ya yi mani zanyi haƙuri saboda bana son ɓacin ranshi.

Nasan halin maza kuma, zai dinga amfani da son da nike mashi yana cuta mani, na biyu kuma rayuwar ƙunci zanyi danna san ƴan mata ba zasu taɓa bar mani shi ba, sannan shima baya da control ɗin kanshi da kowacce yai muraɗi zai kwanta da ita ne, da kuma sauran dalilai masu dama ciki hadda lalata min rayuwa da yayi ya amsar mani budurcina da naita tsiminshi shekaru ashirin da takwas.

Tun daga wannan rana na soma shafe babin Ahmad arayuwata, lokaci zuwa lokaci yana kiran wayata ina ƙin ɗauka, har ya soma gajiya ya rage kira daga baya yama daina dif.

Dan haka na baiwa kaina haƙuri na duƙufa istigifari ina neman gafaran Ubangijina akan laifukan zina dana biye mukaita aikatawa, ahankali na samu natsuwa da salamar rayuwa.


Ban sake kula ko wane namiji ba sai wani Usman dana haɗu dashi ina tsaye bakin titi motata ta mutu na dawo daga kasuwar gari, kawai jingina da motar nayi ina kallon ababen hawa suna ta wucewa, alokacin ne naga wata kyakkyawar mota ash ta faka kaɗan daga inda nake, wani madai-daicin mutum ya fito, wankan tarwaɗa ne mai ɗan jiki bana ƙiba ba sannan tsawonshi kadaran kadahan, baida muni afuska amma kuma ba kyakkawa bane, shiya taimaka min motata ta tashi sannan ya matsa ya amshi lambata wannan shi ne mafarin haɗuwata da Usman.




🕳🕯 *machika novel*🕯🕳

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now