page 25

93 6 0
                                    

🤳🏻

🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*


🕳 *25* 🕳

{ *_Kiyi kokarin koyawa yaranki kananun abuwa a lokacin da suke kananun shekaru,domin awannan lokacin suna da saurin daukan abu, manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa haddan yaro karami kamar rubune kan dutse,haddan babban mutun kuma kamar rubune a ruwa,ki koya musu sallama in zasu shiga gida kowana gida ko daki kada ki bari yaro in dai yana iya magana yana shiga kanki daki ba sallama_*}

بسم الله الرحمن الر حيم




Cak! Na tsaya da tafiyar da nake yi, ya yinda numfashina da tunani da kwakwalwata suka daina aiki na hucin gadi, my dear ko ba kiji ne? Hakan da yace ya dawo da natsuwata na yi wani murmushin da bansan ya taho ba nace, kana dai nufin Nigeria inada nake zaune?

Ƴar dariya ya saki akwai wani gari mai suna haka ne bayan tamu ƙasar? Nayi maza na dai-daita kaina nace, kawai mamaki nake ba sanarwa sai dai naji kwatsam, yace "daman kwatsam ɗin nake son maki ai", anyway dear dama just to tell you na shigo ƙasa ne za muyi magana latter yanzu akwai tarin gajiya atare dani, mukayi sallama ba dan na so ba, na shige gida rai na fes...

***

Bayan kwana biyu ina kwance aɗakina ina shan sanyin A C da jin kaɗe-kaɗen waƙoƙin india a cikin wayata, naji kira yana shigowa, na ɗauko wayar ganin mai kiran yasa na miƙe zaune da sauri tare da amsawa, Ahmad Ali ne ke magana, nayi ɗan murmushi kafin nace komai, ya ci gaba faɗin ɗan leko waje muga kona gane kwatancen gidan naku mana.

Dam...zuciyata ta buga nayi wata irin hantsilowa daga kan gadon cikin ruɗewa nace Ahmad kana nufin gata a ƙofar gidanmu na Kaduna? Sautin dariyarshi naji, yace in kina tababa fito ki tabbatar kawai, gani nan zuwa nace mai na kashe wayar, jikina sai ɓari yake na tsaya gaban madubi ina ƙarema kaina kallo, ganin bani tare da wata makusa yasa na ƙara feshe doguwar rigar atamfa dake jikina da turare na yafa wani madaidacin gyale akaina dama kan nawa ɗaure yake cikin ɓaƙin ƙaton abin ɗaure kai, na sanya flat shoe nai waje, sai da na tsaya bakin get na daidaita natsuwata kana na buɗe na fice.

Wata marron ɗin mota ce sabuwa dal tanata kyalli cikin hasken ranar da yayi yamma tana niyyar faɗuwa, ban tsaya duban sunanta ba saboda ba shine matsalata ba, na dinfari motar ƙafafuwana suna harɗewa dan haka na koma tafiya ahankali wanda zakayi zaton ƴanga ce..

Zuciyata kuma da zaka ƙurama ƙirjina ido zakaga yadda yake ɗagawa da sauka tsabar bugun da take ba ƙaƙƙautawa, na isa wajan motar jin alamun buɗe locks yasa na gane yana nufin na buɗe na shiga, dan haka cikin tsananin mutuwar jiki na buɗe na shige na maida na rufe, sanyin Ac mota da wani irin ƙamshi suka ratsani, ban damu ba burina kawai nayi tozali da fuskarshi..

Masha Allah na furta cikin zuciyata domin ganin kyakkyawar halittar dake zaune gabana shima ya ƙuramin nashi idanuwan fuskarshi cike da murmushi, lallai na yadda zahiri yafi hoto, ya faɗi hakan yaci gaba da cewa Asiyah dama haka kike da sihirtaccen kyau afili?

Nima murmushin nayi aƙasan raina nace ashe abu ɗaya muka fahimta, dan shima azahiri yafi hotonshi haske da kuma kyawun halitta.

Duk sai ya yimin kwarjina na kasa sakewa dashi, dan haka ya koma shi ne mai yin hirar ni kuma ina amsa shi jefi-jefi tare da murmushi, ya gaji yace, wai ko Asiyar bata lafiya ne?

A chatt ba'a kadaki wajen magana amma na zo kinyi lakwas, murmushin kawai na sake yi bance komai ba, yace ok na gane irinku, afili miskilai ne ku amma arubuce akwaiku da surutu, nace a'a ko a filin ma ina magana kawai bansan abinda zance maka bane yanzu, akwai nauyi da rashin sabo na haɗuwar farko...

Shakka babu Asiyah, amma fa ni bani baƙunta, zaki sake ne ma ki rinƙa surutu bari muyi haɗuwa biyu zuwa uku kiga, gaba ɗaya mukai dariya, ba zato naji ya kama hannuna, na kallai da sauri sai naga ya zura min wani kyakkawan zoben azurfa atsayana na biyun ƙarshe, na ƙurama zoben ido dan ba ƙaramin kyau gareshi ba, sai kuma ya yi mun cif kamar angwada yatsan, shima yana riƙe da hannun yace ashe dai na hasaso yatsan dai-dai, a Dubai na ganshi na aiyanoki araina naga zai dace dake...

Na ce gaskiya na ko gode dan ya yi min kyau sosai ya kuma birgeni matuƙa, ya sakarmin hannun yana shafa sajen fuskarshi tare da hamma, sannan ya ce to baƙo zaiyi halin my dear, zanje na hutu dan yau na shigo garin, gobe kuma zan wuce Azare gaida dangi ko inbiyo maki zaki rakani? Ya faɗa yana murmushi da ƙuramin ido, nima idon na zuba mashi cikin mamaki nace wa ce ni, wataran dai maje taren, amma yanzu ka dai gaishesu, na gode ƙwarai da ziyara sai gani na biyu, yace to shikenan, sai anjima munyi waya ko chatt, dan goben nan na shiga Azare da wahala kiji ni...

A haka mukai sallama cikin farin ciki kamar kada ya tafi, na koma gida zuciyata cike da murna fuskata murmushi yaƙi ɗaukewa, musamman inna kalli yatsana naga zoben nan nata walainiya, zuwan Ahmad gareni wani sabon al'amarine daya taɓa faruwa karo na farko, in akayi la'akari da shekara da shekarun dana kwashe ina soyayya da *Gaibu*...

Shi kuwa wannan cikin watanni biyu da haɗuwarmu ya bayyana gareni, fatana ayanzu Allah ya dubeni ya saka mai soyayyata atashi zuciyar, Allah ya tsaga aure atsakanina dashi, danni dai ta kowane fanni ya yimin, da shekaru da kyawon halitta da tsarin yanayinshi sunyi mani....



*_Monday har zuwa Friday sai a hankali domin ranakun zuwa makaranta ne, ƴan'uwa ba zaku rinƙa samun post yadda ya kamata ba sai yanda hali yayi, amma dai weekend insha Allah kullum ne, da fatan zaku min uzri kowa yasan harkar karatu da cin lokaci da kuma caza kwakwalwa_*😀



🕳🕯Machika novel🕯🕳

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now