page 29

114 10 5
                                    

🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*



🕳 *29* 🕳



بسم الله الرحمن الر حيم




Mun ɗauki watanni masu ɗan dama tare da Usman, bana jin sonshi kwata-kwata araina amma kuma bana ƙinshi, Usman shahararren ɗan kasuwa ne wanda kasuwancin nashi ya tara mai dunkiya mai tarin yawa.

Babu irin kalar kayayyakin da baya sarowa daga ƙasashen ƙetare zuwa nan gida Nigeria, yana da mata ɗaya da 'ƴa'ƴa biyu mata masu ƙananun shekaru dan baifi shekara shidda da yin auren ba, Usman yana matuƙar sona amma koda wasa bai taɓa man maganar aure ba.

Ni ce na wataran nayi mashi shaguɓe shi ne yake ceman ya soma ginin gidan daya ke son mu zauna gaba ɗaya da matarshi, tun daga lokacin ban sake mai ita ba dan dama ina fargabar ya aurenin yaga ba budurwa bace..

Mun gama fira wajen goma da rabi na dare yaja motar shi ya tafi ni kuma na ɗan tsaya a bakin get domin ganin Abdul ya tare hanyar yana kallona, nima ɗin watsa mashi mugun kallo nake ina jin kamar na rufeshi da duka, ya matso kusa dani inda ya soma cewa...

"Asiyah baki ganin zuwa yanzu ya kamata ki haƙura haka nan mu koma kamar da"?, naja wani mugun tsaki ina faɗin bani waje na wuce bacci nake ji, na taho da niyyar bangajeshi na shiga, ya yi gaggawar roƙoni ya haɗa da ƙirjinshi ya rungumeni da ƙarfi yana faɗin kiyi haƙuri Asiyah wallahi ina ƙaunarki da dukkan rayuwata, wani irin baƙin ciki da takaicin taɓamun jiki da yayi ya kamani, na shiga ƙoƙarin kwatar kaina amma ina na kasa.

Sai ƙara rungumata yake yana ƙoƙarin kissing ɗina, cikin tashin hankali na kafa haƙorana a gefen wuyanshi na gantsara mashi wani cizo, cikin gigicewa jin zafin cizon ya sakeni yayi baya yana taɓa wajen, ni kuma na duka na ciro takalmin ƙafata duka biyu na shiga kai mashi duka dasu tako ina...

Ina surfa mashi zagi da tsine ma rayuwarshi, ganin haka yasashi miƙo hannu da niyyar kama hannuwa na aida gudu na saki takalman na faɗa gida a guje jikina yanata kyarma, kai tsaye ɗakina na shige harda sanya makulli na kulle ɗakin na na haye can ƙarshen gado na ƙudundune jikina bai daina ɓari ba kafin daga baya kuka ya ɓalle min.

Lallai zanci mutunci Abdul zan mashi iyaka dani ba sai wani yaji ba ma, nida kaina zan ɗaukar ma kaina mataki.

Washe gari da muka haɗu a hanya can tsakar gida ya soma bani haƙuri yana faɗin baisan abinda ya shiga kanshi ba yayi man haka, na wurga mashi harara da cewa koma miye ka tabbatar kayi na farko kuma na ƙarshe, inba haka ba wallahi sai na ƙulla maka sharrin da zai kaika gidan yari, na faɗi maka ka fita harkata babu ruwanka dani, ko kallon tsiya ka sake yi mani zan ɗau mataki akanka, daga haka na wuce na bashi waje.

Can da yamma babu kowa agidan Mami da Rabi'atu sun fita, sai ni ɗaya a kitchen ina shirya mana abincin dare, ina zaune daga gefe ina chatting a facebook kafin abincin ya ƙarasa naji motsin shigowa kitchen ɗin.

Ina ɗaga kai muka haɗa ido da baƙon gidanmu, kallo guda nai mai na ɗauke kai, yana sanye cikin wandon jens blue da wata ash t-shart ƙafarshi silifas ne irin nasu na maza brown kala, sai sirantarshi ta sake fitowa asarari, bance mashi ba shima haka, kai tsaye fridge ya buɗa ya ɗau rowan gora ɗaya ya buɗe ya shanye ya aje goron gefe, sannan ya sake ɗaukar wani ya rufe ya juya dashi ahannu da niyyar fita.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now