page 22

75 4 0
                                    

.🤳🏻

🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
нalιn dana ѕнιga...
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*


💘 *22* 💘


بسم الله الرحمن الر حيم




Maganar da muka yi da Abubakar ta sani cikin wani tunani, bawai dan yaimin hannunka mai sanda da maganar ta Abdul ba, ni dai kawai saina fara raya wani abu game dashi Abdul acikin raina, daga baya na bar abun cikin raina bamcema kowa komai ba.

Yaunda yammanne ni ɗaya ce aƙofar gidan, na dawo daga gidan Anti Lubah zan shiga gida kiran Ibraheem ya shigo wayar na tsaya ina masawa, dana gama ban tashi ba nai zaune nan ina yabawa irin kulawar da Ibraheem ke bani.

Abubakar ya katse tunani ta hanyar zama kusa dani da ya yi, na tada kai na kalleshi, yace na kula dake cikin kwanakin nan tunani ya shigeki, da alama dai auren kikeso da gaske, nayi dariya nace aina faɗa maka tuni aure baya gabana ayanzu tunda...gwaninki baya kusa dake ko? Muka kyalkyale da dariya.

Ya karɓi wayata yana latse-latse muna hirs naga ya tsaya ynaa duba wani abu cikin wayar fuskarshi da alamar mamaki, banyi magana ba shiya kalloni yace, meya haɗaki da lambar *Saleem*? Waye haka ? Nima na tambayeshi.

Me lamba 33...na ƙanƙance ido ina kallonshi da son fahimtar me yake nufi, dan dai lambar da yake magana akai ta *Ibraheem* ce, na karɓi wayar na duba lambar na kalleshi na ce waye kake nufi Saleem?

Wani guy ne anan bayanmu, amma kasan wannan lambar da kake magana ta Ibraheem ɗina ce, ya ƙara dubawa yace, to inajin lambobinne suka yi kama, muka bar maganar ahaka inda ƙarshe ma mukai sallama kowa ya kama gabanshi.

Amma dai awajena sai wannan batu ya zama abin tsoratarwa agareni, dan tuni zuciyata ta soma karanta mani wasu abubuwa, yanzu kuma ga wannan ta ɓullo daga Abubakar dole akwai alamar wani abu aciki.

Da safe har gida na sameshi nace dan Allah Abubakar batun lambar wayar nan nake so ka sake dubamin in kana da ta Saleem ɗin awajenka, yace to ya ɗauko wayarshi yana karanto min ina dubawa atawa..

Abin tsoratarwa da mamaki lambar ita ce ta Ibraheem kuma ta Saleem, to meyasa haka?

Na kalli Abubakar wanda shima yasa min ido, yace kin tabbata lambarce? Na juya kai da ɗan guntun murmushi nace ko daga bacci ka tadani zan iya kawo maka lambar Ibraheem akai, dan haka wannan lamba ta Saleem ita ce dai ta Ibraheem, yace to meya kawo hakan? Nai murmushi kawai nace a ina Saleem yake Abubakar?

A nan bayanmu yake, na sanshi ne na tambaya, ya kuma cewa ba lallai ki sanshi ba gaskiya, dan bai faye zama anan ba sai lokaci-lokaci sai dai ayanzu haka ina tsammanin yana cikin Unguwar...

Kaina ya fara ɗaukar zafi, amma ban bari na ruɗe ba ko wata alamar damuwa ta bayyana akan fuskata ba, nace da zakamin ƙoƙarin da zanji maganarshi ta ɓangarenka ina son gasgata abinda ke shirin faruwa ne.

Ya ɗau wayarshi ya fara neman layin nashi abinda ya nuna number busy, alamar ana amfani da ita...kamin ya sake neman layin kira ya shigo tawa wayar wanda ya nuna private number kawai, (wato anɓuye lambar) ina gani nasan shi ne dan tunda akace yana Niger ɗin nan ban taɓa kirana da lamba ba sai dai aɓoye.

Na ɗaga wayar tare da sallama bayan Abubakar ya gargaɗeni da karna yadda na nuna mashi wani abu, muka gaisa kamar yadda muka saba cikin nuna so da kulawa, na tambayeshi ya jikin Mama yace jiki ya yi sauƙi dan harna fara tunanin zuwa gareki Siyah, na matsu da son ganinki kusa dani, ina takura ainun da rashinki wajena, (tunda nake waya dashi yau ne kawai nakejin kalamanshi kamar zasu sani amai, dan har wata zufa ke tsarfafowa a ilahirin jikina) amma afili ƴar dariya nayi da faɗin uhm Ibraheem kenan, harna gaji da jin gakanan zuwa.

Kina nufin meye Siyah? Nace da dagaske ka damu dani da tuni kayi sanadin da zan gankia ko nace muga juna, aƙarshe kai mana ƙoƙarin kasancewa da juna.

Kiyi haƙuri Asiyah ki kwantar da hankalinki insha Allahu wannan karon babu abinda zai hanani zuwa gareki, nace sai ikon Allah ko? Wannan haka yake amma nai miki laƙawari da yarda Allah wannan karon zakiyi tozali da abin ƙaunarki, Allah Asiyah dan bakisan yanda nake jarabar sonki bane, na bala'in damuwa dake, ina matsifar son kasancewa dake, nace ko?

Uhm Siyah kina wasa da irin son da nake maki, dariya nayi babu maganar wasa ni dai agareni yadda da kalamanka shi ne kazo inda nake, zna baki mamaki Asiyah dan zan zo maji ne Unexpected, nace hmmm Allah ya kawoka lafiya, ya ɗanci gaba da jana da fiya wadda nakejin tamkar saukar kubiya cikin zuciyata, daga bisani mukai sallama dashi.

Muka kalli juna da Abubakar wanda tare muka saurari maganar Ibraheem ko nace Saleem, ka gane muryarshi Abubakar? Ƙwarai na gane shi ne, amma bari na kirashi da lambata danki ƙara ƙasƙantawa, yana danna layin ta shiga kira biyu ya ɗauka dama speaker yasa, sallamarshi ta faɗarmun da gaba, yadda yake min babu banbanci haka maganar tashi take kamar dani yake wayar, yace ya Abubakar kwana biyu, wallahi Saleem nayi zaton kana Kazaure ne, eh to naje nayi kwana biyu, Abubakar yace okey to zan ɓullu da yamma, amma yanzu kana ina ne?

Ina *Sai Allah Ya yi* ana cin masa ko? Sukai dariya dayin sallama wa juna, Abubakar ya kallan kin yadda ko, ƙwarai shi ne Ibraheem kuma Saleem...

Kai na dafe cikin damuwa anya ba'ana son zautani bane, anyi wancan ya wuce wannan ma ya zo ya tabbata min irin wancan, anya zan iya jurewa wannan karon ba tare da nayi wani abu akai ba?

Amma ke Asiya aganinki me zaisa Saleem ya yi maki irin wannan abun? Na kalli Abubakar na ce sashi akayi, na tabbatar turoshi akayi wajena, yanzu haka in zaka bincika baiko sanni ba, amma sun san juna da Abdul, nasan da hannun Abdul acikin wannan lamarin, amma k abarni dasu zan san matakin ɗauka akai.

***

Ina shiga gida da Abdul na faracin karo dashi ya tareni da maganar waiko kwana biyun nan kuna magana da Ibraheem?

Jinai ya ƙara tinzira zuciyata tai sama, damuwa da ɓacin rai suka ɗaukaka, cikin zaɗin zuciya da murya nace Uwar Ibraheem na...ban ƙarashe ba ya katseni ta hanyar rufemin baki da hannunshi, yace Ibraheem bai can-canci irin haka daga gareki ba, duk irin ɓacin ran da zaki shiga bai kamata ki huce haushinki akanshi ba balle harya kaiki da zagin iyayenshi.

Ni kawai ma saina sa mashi ido, wato shi ba ranar da zai daina cutata, ɓacin rai tare da damuwa suka cikani bamma ƙarabi takanshi ba na wuce na barshi wajan.

A ɗakina naci kukana na godewa Allah, abinda zuciyata ta yadda ta kuma ƙaskata shi ne babu Ibraheem, har la'asar ban iya fitowa daga ɗaki ba, ina can ina saƙe-saƙe da abinda zaije ya komo cikin rayuwata.

Na jawo waya na danna layin Ibraheem (Saleem) ya ɗauka da sallama wadda sai da ta sani faɗuwar gaba, ace wai wannan murya ta wanda na ƙwallafa rai akantane, amma ace ba ainihinshi bane, wake magana?

Ya tambaya, (Da yake na ɓoye lambata kamar yadda yake mani) nai shiru kamar ba zanyi magana ba sai da ya sake tambaya sannan nace Asiyah ce.

Asiyata? Ya tambaya da babbar murya irinta mamaki ko tsoro, nayi ƴar dariya irinta damuwa ɓace ni ɗin ce dai nima na rama na kiraka da no name, ya soma magana cikin inda-inda ga muryarshi tana rawa...

Kin gane ko Asiyah wallahi ko ina sonki, ki yadda dani da gaske ina son ki, na sake yin ƴar dariya nace malam Saleem kenan, amma dan Allah nawa aka biyaka ka aiwatar da wannan aikin akaina?

Ya salam! Ya faɗa da babbar murya tare da jan wani ɗan ihu aƙarshe kashe wayar ya yi gaba ɗaya.

Nai tagumi ina nazari abinda kawai nake son sani shi ne dalilin daya sa Abdul yake shirya min wannan bau karo na biyu kenan, sai na riga na gama cin buri da tsananta sona da ƙaunata ga mutum aƙarshe na fahimci cews komai na cikin al'amarin shiri ne, to meyasa haka ne?

Hawaye suka biyo kumatuna banyi tunanin gogesu ba dan haka na barsu sukaita kwarara, kukan baƙin ciki nake musamman inna lissafa tsawon shekarun da aka ɗauka wajan yimin wasa da hankali, sai naji gbaa ɗaya duniyar ta ƙara yimin zafi, naji gaba ɗaya na tsani kaina da dukkan al'amuran da suka shafi rayuwata.

Hakan yasa na ƙara tsananta kukana wani sa'in harji nake kamar na kashe kaina na huta da irin wannan baƙin cikin dana tsinci kaina aciki..



🕳🕯Machikanovel🕯🕳

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now