page 10

140 13 3
                                    

💘 нalιn dana ѕнιga...💘

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ


*Arewabooks@shooly84*



💘 10 💘




_kuyi haƙuri na gaji sosai ban iya editing_

*_Da zaki san halin dana shiga akan soyayyarki  da kin tausayamin, ƙaunarki na wahalar da ruhina da rayuwata, amma akan kaina nafi son hakan zanyi alfahari ace zafin ƙaunarki ne ya halakar dani koba komai nabar tahiri mai girma, ina sonki da yawa Asi na_*

Saƙonshi daya shigo kenan bayan mun gama wayar, na karanta na sake karantawa wata zazzafar ƙaunarshi ta sake ratsani, naji ina tsananin bala'in, masifar, jarabar sonshi, naji akan son da nake mishi zan iyayin komai dominshi hakan kuwa ya haɗa harda sadaukar da rayuwata dominshi.

Ina ƙaunar Ibraheem fiye da son da nike ma kaina, nasha faɗa mishi hakan amma ya kance son da kike min Asi bai kai rabin-rabin wanda nake miki ba, nakan zauna ina dogon tunani akan yanda nake tsananin ji dashi cikin rayuwata da yanda najejin sonshi kamar ya zautani amma yace shi yafi sona fiye da yanda nake sonshi, nakance to inhakane wane irin sone Ibraheem kemin?

Nakan tsare Abdul nace Abdul ina son Ibraheem irin son da baki ba zai iya furtawa ba, amma akullum Ibraheem kance yafi sona fiye da son da nake mishi shin Abdul kana ganin son da yakemin yafi wanda nake mishi ƙarfi?

Abdul ya kanyi dariya yace "kibar haɗa irin son da kikewa Ibraheem da wanda yake miki, ko kusa ko alama baki kama rabin-rahin son da Ibraheem ke miki ba, dan dai bakisan *Halin daya shiga* adalilin ƙaunarki bane, mu da muke tare dashi mu mukadan halin daya shiga akanki da soyayyarki Asiyah".

Muhammad ma abinda yace min kenan, kibar kwatanta don ɗa kikewa Ibraheem da irin wanda shi yake miki Asiyah, akwai bam-banci mai tarin yawa dan dai ke kanki kika sani shiyasa zakiji kamar kinfi sonshi amma *Halin daya shiga* akanki da soyayyarki mai girma ne.

Munyi haka da Yusif, yace "kibar jayayya da Ibraheem abatun ƙauna, ban taɓa ganinki ba balle nasan  halin da kike ciki game da soyayyarshi amma abinda nake so dake ki fahimta Ibraheem ya fiki ƙaunarki Asiyah, *halin daya shiga* akanki da soyayyarki kawai ya isa ya tabbatarwa da duniya  soyayyar da yake miki ta  rinjayi wadda kike mishi sau ba adadi.

To waini wannan wane irin sone Ibraheem kemin?

Anya kuwa ba zai tabbata ba kamar yanda yace zuciyarshi zata iya bugawa saboda zafin sona ba, koko ya haɗu da ciwon hauka kamar yanda yasha faɗamin *Zafin sonki zai iya zautani Asi*.....

Tausayinshi mai zafi ya taɓa zuciyata tare da ƙarin shigar wutar ƙaunarshi cikin zuciyata, na janyo waya na tura mishi amasar saƙonshi dana rubuta.

*_Na damu da halin daka shiga akan ƙaunata amma nima ina son ka sani halin dana shiga akan ƙaunarka mai girma ne, na yarda da kai kamar yanda kace muna son juna mun damu juna kuma muna ƙulafucin juna_*

*_Na damu da kai da yawa Ibraheem, zanso ace duk halin da zaka shiga tare dani ne, ma'ana tarihin nan da zakai alfaharin kafawa mukafashi tare, naɗau ɗamarar shiga kowane irin hali dominka, zan oyayin komai dan na gwada maka zafin ƙaunar da nike maka, hauka ko mutuwa indai akanka ne bani gudunsu Ibraheem, na damu da kai da al'amarinka sonka mai girma ne atare dani_*

Saƙona bai daɗe da zuwa ba nashi ya shigo inda yace...

So! So!! So!!! So masifa ne Asi, abune mai sanya damuwa mai haddasa fitina da tashin hankali musamman inbakai dacen samun kyakkyawan wajan daya dace kayi son ba.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now