page 8

103 8 0
                                    

💘 нalιn dana ѕнιga...💘

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

*Arewabooks@Shooly84*

💘 8 💘




   Ina nan ina lisssfin zuwan Ibraheem kaduna tare da lissafin ranakun da suka rage na bikin ƴar uwata Farida, abin haushi Muhammad ke faɗa mun wai Ibraheem ya fasa zuwa, hankalina ya tashi na shiga damuwa nace to akan me ya fasa Muhammad?

Ba wai ya fasa bane gaba ɗaya, ya dai ɗaga tafiyar ne sabosa  Abdul ya faɗa mishi bikin Farida 21 May shine yace zai bari sai lokacin yazo danya samu ya halacci bikin, yace dai wuraran 15 May ko 18 zai iso, kinga alissafi yau saura wajan kwana ashirin da huɗu kenan.

Ni dai kam jikina ya mutu dan naji ba daɗi nariga na gama sa rai da zuwanshi yanzu kuma ace an fasa, Muhammad yace "haƙuri zakiyi ki kwantar da hankalinki kamar yau ne zakiga lokacin yayi har kunga juna..."

Aini damuwata ɗaya Muhammad kar lokacin yazo yace ya kuma fasawa, yace ina insha Allah haka ba zai faru ba kisa rai ma kinga Ibro ɗinki kin gama.

Muna nan tsaye tare da Muhammad Abdul-Jabbar yazo ya faka motarshi kusa data Muhammad, inda muka bishi da kallo.

Inda Muhammad yace kai wannan rai da naci yake, shiko fushi ba yayi, jiya yazo an wulaƙantashi yau ba zai hamashi zuwa ba, amuzantashi amma ba zaisa yaƙi dawowa gobe ba, kaini ban taɓa ganin jarababben mutum irin wannan ba.

Nayi dariya nace na yadda lallai da gaske kana taya Ibraheem kishi, tunda agabana kake zagar min saurayi, ya ɓata fuska yace "Asiyah tunda Ibraheem ya soma sonki bai ƙara kula wata mace da sunan so ba, amma ke kullum cikin tara samari kike saboda Allah kinyi mishi adalci"?

Toh ya zanyi Muhammad, cewa fa ake ana sona bani ke cewa ina so ba, amma dai ya kamata kisan irin takun da zaki rinƙayi masu ko? 

Na rinƙa wulaƙantasu ko?

Bance ba, amma ya kamata ki guji fushin Ibraheem dan yana kishinki da yawa, duk randa ya ganki da irin waɗancan akwai fitina, nace to shikenan zanyi ƙoƙari na kiyaye, bai bari Abdul-Jabbar ya ƙaraso inda muke ba yai min sallama ya shige motarshi yai gaba ya barni da dariyar yanda yai kicin-kicin da fuskarshi kamar shine Ibraheem ɗin, shi bai yadda ba yana taya ɗan'uwanshi kishi.

*****************

Ina zaune kan dardumar dana idar da sallar magriba ban tashi ba inaso akira isha nayi saina fito falo, daganan cikin ɗakin naji muryar Bashar da Abdul a falon Mami.

Bashar ke faɗima Abdul wai Isa yai mai waya ɗazu yace afaɗa mishi Ibraheen yayi Accident, ya nemi layinshi bai samu ba shiyasa ya kirashi ya faɗa mishi, itama Asiyar bai sameta alayinta ba...

Ni da nake sauraro daga ɗaki nafi wanda ake gayama saƙon fahimtar abinda akace, Ibraheem yayi Accident kalmar dana rinƙa nanatawa akan harshena kenan, yayin da gaba ɗaya jikina ya ɗauki rawa saboda tsoro da firgita dajin abinda ya faru ga Ibraheem.

Na tashi da kyar jikina ba ƙarfi na isa inda su Abdul suke na jinkina da ƙofa wadda taimin makari daga faɗuwa naci gaba da sauraren abinda Bashar ke cewa.

Wai jiya sukai hatsarin su huɗune acikin motar ɗaya ya mutu shi kuma Ibraheem ɗin yai muguwar buguwa wanda har yanzu baisan inda kanshi yake ba...

Jiri gaba ɗaya ya taso min na tashin hankali nai taga-taga zan faɗi Mami tai saurin taroni  ta zaunar dani kan kujera, nan na sami damar rintse idanuwana da ƙarfi kalmomin da naji abakin Bashar su suke yawo atsakiyar kaina suna haddasamin tashin hankali.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now