page 18

76 4 0
                                    

🤳🏻

⏳🕹⏳🕹⏳🕹
нalιn dana ѕнιga...
⏳🕹⏳🕹⏳🕹

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*

💘 *18* 💘

بسم الله الرحمن الر حيم




*Ƙasarmu Ta Gado Nigeria*

Mun iske gida lafiya kowa kuma lafiya, ƴan barka da zuwa mun iskesu tamƙam agida dan haka ne tun isarmu ban samu nakeɓe ni ɗaya ba, kai ko damar hutuwa bamu samu ba, mutane ne daga wannan ya fita wasu zasu shigo.

Mutanen Jalingo ko dama agidan muka tarardasu, har bayan sallar isha'i bamu natsa ba, ni dai alokacin ne na zame nai gidan Anti Lubah, da Imam na fara cin karo atsakar gida yana wasa abakin famfo, ya zama ɗan saurayi abinshi.

Farin cikin ganinshi ya lulluɓeni, na tafi da gudu nararumeshi na rungume aƙirjina ina faɗin nayi kewarka yaro na, jin magana yasa Anti Lubah fitowa daga kitchen ganina yasata cogewa abakin ƙofa cike da mamaki, da gaske kece Asiyah?

Nayi dariya ni ɗince dai karkiyi mamaki, ta ƙaraso ta rungumeni muka hau murnar ganin juna, nayi farin cikin ganinki Asiyah, wannan daba farin sani nai maki ba ba zan ganeki ba, kinyi haske da fresh sai wani *glowing* fatarki keyi, amma fa kinban haushi da baki sanar dani zuwanki ba, nayi dariya nasan dama dole nai laifi amma ayimin haƙuri.

Nan muka dasa hirar yaushe gamo bamu muka rabu ba sai goman dare, tun agidan Anti Lubah nake neman layin Ibraheem na rasa harna dawo gida ina nema amma sam layin yaƙi samuwa, har zuwa yanzu misalin biyu da kwata na dare ƙoƙarin samun layin nkae amma hakan yaci tura.

Gari ya wayemin cikin damuwa rashin jin Ibraheem, ko karyawa bamuyi ba na cimma Abdul asassansu cikin damuwa nace wai Abdul me Ibraheem ke cikine tun jiya nake neman layinshi na rasa..

ya juya kai yana faɗin nima fa rabon da muyi magana ankusa kwana tara kenan, yanzu ƙara jarabawa mu gani, ina ni da shi muka ƙara kira baya shiga dai, na koma cikin gida cike da damuwa.

Da rana Muhammad ya zo gaida Abbah, kwatsam ya ganni abin ya bashi mamaki ya koma farin cikin ganina, yini mukai hira sai wajen magriba mukai sallama na bashi tsarabar da nayo mishi.

Da nai sallah gidan Anti Lubah na wuce, acanma mun ɗau lokaci muna hira da tattaunawa game da rashin samun Ibraheem, sai da nai sallar isha kafin na wuce gida na tadda Abdul na jirana, ya tambaya kin sami layin nashi ne?

Har yanzu dai, yace to shikenan bari na fita yanzu zan binciko miki halin da yake ciki.

Har kusan sha biyu ina jiran dawowar Abdul, bai shigo ba na gaji na shige ɗaki nai zuru cikin damuwa, wajen ɗaya saura kiran Abdul ya shigo, na ɗaga wayar nace ya ake ciki Abdul?

Yace dana fita dai ban sami wanda zanji wani abu game da Ibraheem ɗin ba awajenshi, na dawo gida to amma yanzun nan Ibraheem ɗin ya kirani, ashe wai yana Niger mahaifinshine ya rasu shekaran jiya, to yana tambayata game da layinki na can wai yanata nema ya kasa samunki, to ammafa gaskiya bance mashi kinzo ba, danna tabbata inyaji kina gari zai iya cewa zai baro can yazo amma ke ya kika gani?

Allah sarki tuni tausayinshi ya gama cikamin zuciya, rashin uba ai babban rashine kuma abu mafi tayar da hankali arayuwar ɗan adam, rashin uba wani muhimmin ɓangarene a rayuwa, na tuna ni nawa uban rashin lafiya yayi, amma hankalinmu ya tashi bai kuma kwanta ba sai da muka ga ya sami lafiyar, to balle shi kuma ɗungurungun ya rasashi rashi irin wanda ba za'a ƙara ganin juna ba.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now