page 16

93 5 2
                                    

🤳🏻

⏳🕹⏳🕹⏳🕹
нalιn dana ѕнιga...
⏳🕹⏳🕹⏳🕹

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*


💘 *16* 💘

بسم الله الرحمن الر حيم




Kwana biyu ya rage Ibraheem ya zo, da yamma ya kira wayata bayan mun gaisa ya ce anya ko Siyah ba zan miki laifi ba, na ce laifi wane iri Ibraheem?

Game da zuwa na kaduna, gabana ya faɗi kar dai ace ya fasa, banyi magana ba yaci gaba da cewa, yardarki zan nema inkin karɓi uzrina to, in baki yarda ba shikenan sai nayi yanda kike so kina jina?

Asanyaye na amsa ina jinka, Siyah ina son ganin wassn polo wanda za'a fara cikin satin da zamu shiga anan kaduna shine na ce inba zan sa miki damuwa ba kimin adalci na ɗaga zuwana har zuwa lokacin sai na taho gaba ɗaya koya kika ce?

Nai doguwar ajiyar zuciya kamin na nisa na ce zuwa yaushe kenan?

Nan da kwana bakwai ko ya yi tsayi?

Na juya kai ina faɗin Allah yasa muna da rai, yai saurin amsawa da Amin na gode Asiyah kinyi min adalci sosai dan gaskiya ina jarabar son wasan polo ko ƙanƙani bana son kallonshi ya wuceni.

Nayi ƴar dariya na ce ra'ayinmu ya zo ɗaya kenan, kema kina son polo ko?

Sosai na faɗa cikin dariya, wasan yana matuƙar birgeni ya shiga raina ainun, kina nufin kina zuws kallon?

Yai maganar ne kamar aruɗe kuma atsorace , na ce a'a ban taɓa zuws inda akeyi ba kuma bana sha'awar zuwa, sha'awata na kalla a tv in anayi hankalina akwance.

Uhm! Naji saukar numfashin shi kamin yace har hankalina ya kwanta, na tambayeshi game me?

Yace kin gane ko Asiyah abin ne...koda yake ma share kawai, na ƙyalkyale da dariya na ce na ɗagoka fa Ibraheem, shima yai dariyar aiba wani abu bane dan kayi kishin abinda kake so ko? Uhm haka ne aishi kishi halak ne, to ina kishinki da yawa ina sonki da yawa nai murmushi ns ce na gamsi da cewarka tuni, abinda kawai nake so da kai kayi ƙoƙarin ganin cikar burinmu, karki damu da wannan Siyah, insha Allah nan da ƙanƙanin lokaci ni dake zamu zamo ƙarƙashin inuwa ɗaya.

Kwana biyu ya rage Ibraheem ya zo kaduna kwatsam Abbanmu ya kwanta ciwo ƙasar England alokacin kwananshi tara da tafiyar, hankali tashe ni da Mami tare da Hashim muka bi jirgi muka iske shi acan.

Mun tarar jikinshi ya yi tsanani hankalinmu ainun ya tashi, wai ciwo ne n alokaci ɗaya ya fito bayi santsin tails da ruwa suka jashi ya faɗi tun daga faɗuwar har zuwa lokacin da muka isa asibitin baisan inda kanshi yake ba.

Likitoci sai ƙoƙari suke akanshi amma kamar ba'a komai ko ɗan yatsa baya motsi ajikinshi, mukan munga tashin hankali bamu da abinyi sai kuka da addu'a domin halin da Abbanmu yake ciki sai Allah kawai.

***

Kwananmu shidda cikin zunlumi da jimamin halin da Abbah yake ciki, mun duƙufa gayawa Allah ya taimakemu ya ɗaga mana kafaɗun Abbanmu.

Aranar da yamma muna tare aɗakin da Abbanmu yake harda Abbas daya biyo bayanmu munsa Abbah agaba muna kallo dukkanmu muna riƙe ɗa carbi kowa da irin addu'ar da yake acikin zuciyarshi.

Kamar almara naga hannun Abbah yana motsawa, da fari nai zaton idona kemin gizo sai ban damu ba, lokaci kaɗan na ƙara gani motsin kamin nai tunanin wani abu naji Mami tace kuna ganin abinda nake gani koko idona kemin gizo?

HALIN DANA SHIGA...Onde histórias criam vida. Descubra agora