page 1

827 31 7
                                    

🤳🏻

🖤💘 нalιn dana ѕнιga...💘🖤

*~Labarin gaske ne~*

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984



*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...

*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*
*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*
*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*
*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*
*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*

*DAGA MARUBUCIYAR:*

*MUNAH*

*MUSO JUNANMU*

*ZARAH HAYAT*

*Gani Allah ya nufeni da sake dawo maku da wani sabon salo, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfanar ga al'ummar duniya, yadda na farashi Allah ya bani ikon gamawa lafiya Ameen*


💘 1 💘


بسم ا للةالر حمن الر
حم




*Halin dana shiga* arayuwata, haline mawuyaci mai rikitarwa sa'an nan mai ban al'ajabi.

In'an juya ta wani ɓangaren kuma zai zamo abin ban haushi mai ban takaici, wasu da yawa kuwa na tabbata zasu zamo ne masu yin dariya agareni...

wanda ba zan so mai karatu ya zamo maiyi mani dariya ba akan *halin dana shiga* ba...

Abinda zan so da kai, ka zamo mai  tausayawa a gareni da kuma bani shawarar abin daya dace nayi game da wannan *halin dana shiga*.

Abinda nake son fara sanar da kai shine ni ɗin nan anjefani cikin damuwa wadda ba zata taɓa barina ba har illah masha Allahu, domin haƙiƙa anyi min illah babba cikin rayuwata....

Mai karatu bari kaji irin mawuyacin *halin dana shiga* cikin rayuwata.

*_Halin dana shiga_*

Ni na zamo ƴa ta hudu daga cikin jerin ƴaƴa shidda da iyayenmu suka haifa, mahaifinmu Alhaji Bello Jalingo ɗaɓ kasuwa ne wanda Allah ya azurtashi da arziki na ban mamaki...

Sai dai gaba ɗaya harkokinshi yana yinsu ne a ƙasashen ƙetare, dan haka ne bai fiye zama tare damu ba, cikin wata biyu ba yayin cikakken sati biyu a gida Najeriya.

Amma fa akwai kulawa  irinta Uba da ƴaƴanshi, duk wasu harkokinmu dake kanshi yana biya mana su, yana kula da duk wasu al'amuranmu na rayiwa...

Kulawa da tarbiyarmu yana hannun mahaifiyarmu Hajiya Karimatu, wadda mu mukan kirata da Mami, ita kuma ta zamo mace mai tsananin haƙuri da kawar da kai da rashin nuna damuwarta akan al'amura da dama.

Babban burin rayuwarta shine kwanciyar hankalinmu, ta tsani abinda zai taɓa mana hankali, sau tari akan gane damuwarta ne idan ɗanta yana cikin mayuwacin hali...

Wannan yasa mutane da yawa kan ce wai ita mai ƙulafucin ƴaƴa ce...


Ita da mahaifinmu tushensu ɗaya, fulanin Jalingo ne ta cikin jihar Taraba, haka kuma sun zamo ƴan uwa dan sun haɗa kakanni ta ɓangaren iyayensu maza.

Tun kafin mahaifinmu yayi aure yake harkokin kasuwancin shi a Kaduna, bayan auran Mami ma ya taho da ita Kaduna sukaci gaba da zama yana gudanar da harkokinshi har Allah ya azurtashi da dukiya da ya'ya.


Babban wanmu Hashim shike tsaye akan harkokin Babanmu dake nan gida Najeriya, sai Abbas wanda shi kuma  "Personal Manager ne a A. B. J motors shima mallakin mahaifinmu ne.

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now