page 11

101 6 0
                                    

🤳🏻

⏳🕹⏳🕹⏳🕹
нalιn dana ѕнιga..
⏳🕹⏳🕹⏳🕹

~Labarin gaske ne~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984

*_Not edited_*

*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...

*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*
*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*
*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*
*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*
*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*

*Ina baku haƙurin dogon jinkirin dana ɗauka, hakan ya faru ne kan wasu uzrirrika da fatan zaku min afuwa*👏🏻

💘 *11* 💘


بسم الله الرحمن الر حيم




Nai jinya na wartsake a jiki, amma a zuciyata ba abinda ya sauya, kullu yaumin ƙaunata sona tamkar ƙara tinzira suke akan *Ibraheem* , wanda zuwa lokacin nan ya tabbata cewa tabbas Ibraheem Gaibu ne babu shi, amma na rasa tayanda za'ayi na tsige son nan nashi araina balle har na hana wanda yake ƙara tinzirowa shiga.

Amma a wani abu dana sawa raina wasa ace babu Ibraheem gani nake wataran za'a dawo acemin akwaishi harma ace mun Asiyah fito zoga Ibraheem aƙofar gida yana nemanki, sautari in akai sallama cikin gidanmu nakan ji gabana ya faɗi na kumasa kunne naji me za'ace, abinda zan so kullum naji ance Asiya ga Ibraheem, amma shiru har zuwa yau da nike bada wannan labari ba wani bayani.

Dogon lokaci ina fama da zafi da ƙuncin na zuciya wanda nai imani ciwon da nake ji acikinta ba zai taɓa ɓarina ba har....

Cikin wannan lokacin na ƙauracewa ganin Muhammad na ɗaukewa karba wayarshi ko Abdul da muke gida ɗaya dashi na haramta magana da shi nama haramta mashi ganina kai gaba ɗaya gidan na ƙauracewa doguwar hurɗa dasu.
Na kanyi zaune nai dogon nazari akan faruwar wannan al'amari, abinda nake son fahimta shin menene dalilin da yasa su Abdul su kaimin wannan shiri? Amma ko ƙanƙani na kasa samo hanya ɗaya illah ako yaushe nai dogon nazarin na kan gano tabbas akwai ƙwaƙƙwaran dalili wanda ni na kasa gano meye shi.

Cikin sati na hudu da fahimtar Muhammad shine Ibraheem na yanke shawarar tuntuɓar Isa da Yusif dan naji daga garesu.

Yusif na fara kira bayan mun gaisa na ce ban taɓa ganinka ba Yusuf, amma kana da kima da matsayi mai girma awajena, dan na kan jika ajikina amatsayin makusancina, kuma a yanzu kaima na juyaka na maidaka tamkar Abdul da Muhammad, dalilin har da kai akayi amfanin wajan yimin yawo da hankali da yaudararmin zuciya ta afkawa son *Gaibu*.

A nan dan girman zatin Ubangiji Yusif kun kyauta min kana ganin kunyi adalci ga halin da kuka jefani?

Kiyi haƙuri Asiya, abinda ya fara cemin kenan, ya ci gaba da cewa bamu taɓa haɗuwa da juna ba baki sanni afuska ba kamar yanda ban taɓa ganin taki fuskar ba amma wallahi Allah ɗaya ne Asiya ina tsananin rajin daɗin abinda akai miki.
Tun farkon sakoni cikin al'amarin naso ganar dake gaskiya akan abinda ke faruwa amma Abdul ya takamin birki ya lallaɓani akan sanar dake kamar naci amanar shine, wannan shine dalilin da yasa yaƙi yarda muga juna kenan.

Naja dogon numfashi tare da gangarowar hawaye na ce, amma Yusif wai da gaske babu Ibraheem?

Yai ɗan shiru...daga bisani ya nisa yace to inma akwaishin gaskiya ni ban sani ba, hawaye ya ƙara zubomin cikin muryar kuka na ce, amma fa kai kake nuna min Ibraheem amininka ne makusanci, ya ce eh yanda na ce maki haka akace na ce maki, amma azahirin bansan wani Ibraheem ba.

Raina ya ƙara ɓaci wai da gaske dai babu Ibraheem, komai ya faru game dashi dani shiri ne.

Dana kira Isah shima kamar Yusif ɗinne komai sashi akayi shiri ne cewa akai suce, Isha ma harda ƙarin cewa shi tunda yake ƙafarshi bata taɓa taka Lagos ba, dana tambayi batun hotonan dana bayar akaima Ibraheem ya ce Abdul da Muhammad suka zo har gida suka amsa, yanzu haka suna wajen Muhammad.

A ranar na tabbata babu Ibraheem da duk wani da suka shigo maganar irinsu Anty Amina, Nafisa, Abdulmalik na bincika gaba ɗaya basu da wata masaniya akan Ibraheem, komai akanshi shirya masu akayi akace suce.

Nai kuka mara musultuwa, kuka irin wanda baijin lallashi, danko Mami da taga irin kukan sanyamin ido kawai tayi, sai da na bari dan kaina take ce min yanzu ke kan abinda bai kai ya kawo ba kike son halaka kanki ko Asiyah?

Na kalleta da idanuwan da suka ƙanƙance na ce yanzu Mami *Halin dana shiga ne*bai kai ya kawo ba?

Ta ce to ya zakiyi tunda da kanki kin tabbatar da gasken babu shi ba saiki haƙura ba, na goge hawaye nace to Mami ya kike aon nayi ne?

Kinfi kowa sanin yanda Ibraheem yake araina sannan ace rana ɗaya na cireshi to tawacce hanya zanbi nacire shin Um Mami?

Ta dafa kaina ta ce kiyi haƙuri ki kuma dangana kiyita adu'a ahankali sai kiga komai ya wuce kamar ba'ayi ba, ina kallonta na ce wai Mami akanme Abdul ya yi mani haka?

Ta juya kai ina zan sani Asiyah tunda ba zuciyarshi nake gani ba, ni dai abinda zance maki kiyi haƙuri, nai ƙasa da kai bance komai ba wani tunani ya darsu araina, ina mutumin nan mai baƙaƙen kaya?

Wanda muka haɗu a Business center shine ya faɗo min araina, tunda dashi aka ruɗeni akace Ibraheem ne, toshi miye makomarshi waye shi?

Nasan dai tabbas ba Muhammad bane, tunda wancan shi fari ne , koma waye ni dai shi zuciyata ke so tunda akanshi aka ɗorata shine muraɗin raina.

********************

Ina kwance aɗakin Mami bayan sallar la'asar ita kuma batanan taje biki cikin gari, nai rigingine ina kallon silin tunani dai nake akan abinda ya faru kamar daga sama naji kukan wayata jin ringing ɗin abazata ya sani firgita na tashi zaune ina dube-dube inda na hangota can kan madubi na tashi da kyar na ɗaukota na duba screen ɗin naga sunan *Merah Dil*...wato (Zuciyata) sunan dana sawa Ibraheem kenan.

Duk da nasan Muhammad ne sai da naji wani iri ajikina, tsanarshi ta ƙara darsuwa araina, na tuna kwanakin baya ba abinda kesa naji farin ciki irin naga kira daga merah dil...amma a yau sai abubuwa suka taru suka cakuɗe min naji ƙunci da ɗaci araina, wayar tashi ta ƙara saukar min da damuwa amma kuma alokacin sai da zuciyata ta buga ta ƙara zafi akan son Ibraheem Gaibu.

Tun ranar da abun ya faru sai yau na amsa wayar Muhammad wanda kullum rana ta Allah sai ya kira, jin muryar tashi sai daya ruɗani dan da muryar da yake min magana as Ibraheem da ita yai amfani alokacin.

Na runtse ido da ƙarfi har sai da kwalla ta zubo mani, na kwantar da murya na ce ina jinka Ibraheem, yai ɗan shiru kamin ya nisa ya ce Muhammad ne Asiyah, na buɗa ido ona gyaɗa kai na ce na sani me kake nema awajena?

Ya sassauta murya ainun ya maidata kamar lokacin yana Ibraheem in yana son lallashina akan wani abu, yace ina son ganinki Asi.

Muryar da yai magana da itane tasa zuciyata bugawa da ƙarfi ba tare da jinkirin magana ba ko jan zance na ce kajira fitowata....

💘🖤 Machikanovels🖤💘

HALIN DANA SHIGA...Where stories live. Discover now