BABI NA SHA TAKWAS

2.5K 169 1
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

Page *35~36*

Deducated to *Marubuta & Zamani Writers Association* ana mugun tare irin totallyn nan😘😘😍😍





Hafsat ɗaki ta shiga zuciyar cike da farin cikin wannan hukuncin na Dady, sai dai kuma ta wani fannin tana tausayawa Ni'eema, don tasan Aunty Mama bata ƙaunar Ni'eemar ko kaɗan.

Shi kuwa Abdul-Nasir a na shi ɓangaren ya kasa fahimtar a wani hali yake, don shi fa gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya, tabbas ya san ba wai farinciki ya ke yi ba, haka kuma baya takaici da umarnin mahaifinsa, abu ɗaya ya sani shi ne zai rungumi ƙaddara ya cigaba da addu'a har Allah ya ba shi mafita, da wannan tunanin zuciyarsa ta yi sanyi.

Washegari da safe ranar ta kasance akwai makaranta, tun da wuri Ni'eema ta tashi ta mu shirya su Sagir sannan ita ma ta shirya, sun yi break a tsanaki sannan Ni'eema ta miƙe kamar yadda ta ta saba, ta yi wa Mami sallama tare da ɗaukar jakar makarantar ta. Suna  fita a harabar gidan ta yi karo da Yayansu, da sauri ta ɗauke kai ƙirjinta na harbawa da sauri, su kam su Nazir wajen shi suka nufa suna fadin "Ina kwana Yayanmu?"

Wani ƙayataccen murmushi ya saki tare da amsawa cikin muryar sa mai daɗin sauraro "lafiya lau 'yan samarin Mami, har kun shirya ke nan?"  "E" suka ba shi amsa. "OK to ku zo na saukeku a school ɗin."  wani farin ciki ya kamasu. Ni'eema kam ranta ne ya ɓaci ganin yadda ya tasa yaran gaba gashi tasan latti zai ja mata, ƙaramin tsaki ta ja tare da cigaba da tafiyarta, tana fita inda motar dake kai su makaranta take, sai taga wayam har sun wuce, hankalinta ya tashi cikin ranta ta ce "Mugu dama don ya ja mata latti ne, shi ya sa ya riƙe yaran." Dama ita tuni ta daɗe da sanin shi ɗin mugune, harara ta cilla masa wanda shi bai ma san ta yi ba. komawa ciki ta yi tacewa Mami ta bata kuɗin nafef, kuɗin Mami ta bata sannan ta kama hanyar school.

Haka Ni'eema ta kasance ko cikin school bata da walwala, gaba ɗaya hankalinta ba a kwance yake ba, hatta kawayenta sun rasa gane kanta a haka har aka tashi, bata tsaya jiran komai ba ta yi gida. Tana cire uniform ta zube a gado tunanin yadda zata rayu babu Musaddik take yi, ƙarar wayar ta ya dakatar da ita daga tunanin ta, tana jin wayar na ringing amma bata ɗauka ba har sai da ya kusa tsinkewa, sannan ta yi ƙarfin halin ɗaukar wayar. Muryan Musaddik ta bayyana fes cikin dodon kunnenta yana faɗin "farin cikina fatan kina lafiya, ina fatan baki manta da soyayya ta ba, da Alkawarin auran dake tsakanin mu?"

Wasu zafafan hawaye suka tsiyayo daga idon ta, bakin ta ma yaƙi buɗewa ballantana ta bashi amsa, sai kuka, hankali Musaddik ya yi masifar tashi jin Ni'eema taki magana sai sautin kukanta "Please Ni'eema bar kuka bari nazo, wallahi bana son kukan ki, ko kaɗan."  hankali tashe yake maganar ba'a fi minti sha biyar ba sai gashi ya iso gidan. Yana fakin motar sa, ya fita tare da ciro wayar sa ya soma kiran layin Ni'eemar. Ni'eema dake kwance ta yi saurin daukar wayar tare da yin sallama.

Powder kawai ta murza tare da daukan hijjab ta sanya, a harabar sasan su ta ganshi tsaye, kallo ɗaya ya yi mata ya tabbatar da lallai babu lafiya don ba haka ya saba ganin Ni'eemar sa ba. Cikin sanyin murya ta soma gaisar da shi bayan sun zauna a kan kujerun dake wajen.

Amsawa ya yi yana ƙara kallon ta jiki a sanyaye ya ce "Farin ciki na lafiya kuwa?"  hawayen da take ɓoyewa suka silalo daga idonta. Wani sabon tashin hankali ya shiga muryar sa har rawa take ya ce "Please Ni'eema bar kuka ki yi min bayani ba fa kuka ba ne mafita ba."  da ƙyar ta buɗe baƙi ta ce "Ya Musaddik ka yi haƙuri dole na sanar maka da abin da ke raina, nabsan ba zaka ji dadi ba ni ma bana cikin jin daɗin... Bata gama maganar ba Abdul-Nasir ya fito daga ɗakinsa yana amsa waya.

Da sauri ya zame wayar a kunnen sa tare da zaro ido yana kallon su, don zaman da suka yi da gani kasan zamane na masoya, Musaddik ne ya isa kusa da shi tare da miƙa masa hannu suka yi musabaha "Abdul ashe ka dawo ba ni da labari? " murmushi Abdul din ya yi bayan ya watsa wa Ni'eema wata harara ya ce" Wallahi ka ganni jiya na zo." "Ma Sha Allah."  shi ne abin da Musaddik ya faɗa, Shi kam Abdul-Nasir kama gaban sa ya yi, ba tare da ya kuma magana ba.

Ganin kallon da Yayansu ya cilla mata da sauri ta shige falon su, hawaye masu zafi na rabuwa da masoyin ta suka cigaba da sauka a fuskar ta, Musaddik na juyowa yaga babu Ni'eema a wajen take ya yi tunanin ta koma falo, jiki babu lakka ya nufi motar sa da ƙudurin yau ɗin nan zai sanar da Abban sa azo maganar auran sa da Ni'eema, ko hankalin sa zai kwanta.

*********************************

Aunty Mama zaune gaban wani malami da Hajiya Lantana ta rakata, bayan ta gama zayyano masa matsalar ta da kuma dalilin zuwan ta wajen sa, kallon ta ya yi na wani lokaci sannan ya soma surkullen sa da buga ƙasa, yi yake babu kakkautawa a kalla ya kai minti goma yana aikin abu ɗaya sannan ya ɗago ya zuba mata idonuwan sa ya ce "Gaskiya Hajiya aikin ki mai wuya ne, na yi iya yina banga nasara ba, don wannan yarinya da kike gani itatce matar da ɗanki zai aura kuma ita ce matar arzikin sa, uwa uba kuma tana matuƙar riƙo da Addinin, sam bata sakaci da Addu'a, matuƙar kika matsa to fa kina iya rasa ranki...
Wani zafafaffen zufa ya ke ketowa Aunty Mama don maganar yi mata yawa, ita da tazo neman mafita kuma sai ta ji maganar da tafi ƙarfin ta...



Muje zuwa.

NE'EEMA COMPLETEМесто, где живут истории. Откройте их для себя