BABI NA SHA UKU

2.8K 174 0
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

This Page is dedicated to *Ummyn Yusrah* Ina yinki irin da yawan nan I love you wujiga wujiga 😘😘😘

Page *25~26*

'Yar taji tsigar jikin ta ya tashi, sai taji kamar a mafarki. Bude ido tayi don ta tabbatar da gaskiyar abin da taji sai sukayi idon hudu da Musaddik, ai da sauri ta k'wasa zuwa falon Mami don ji tayi wata irin kunya ta rufe ta. "Alhamdulillah"  Musaddik ya fada a fili don ji, don da ganin yadda Ni'imar tayi yasan bazatayi wahalar karban soyayyar sa ba. Sallama ya doka cikin falon Mami, Mami dake zaune tana mamakin shigowar Ni'eema da gudu ta amsa, tsugunawa ya yi tare da gaisar da ita, amsawa cikin sakin fuska, don tuni ta gane nufin Musaddik akan Ni'eema.

Shiru yayi yana lallatsa wayar sa, zuwa can yace "Mami ina su Nazir ne, ban gansu a tsakar gida ba?"  "Su Nazir suna gidan Albdulhakim dazun da yazo suka bishi." Mami ta bashi amsa. Dan sosa kai ya yi tare da dukar da kai don yana kunyar fadama Mami abin da ke ransa, haka dai ya gaji da zama ya yayi mata sallama har a lokacin Ni'eema bata fito ba, yaso sake ganin beauty face din ta sai dai yana kunyar Mami. "To Musaddik ka gaida Momy Allah ya yi Albarka kana kwasan lada sosai."  Mami ta fada tana mikewa, don duba abincin da ta daura a kici. "Amin Mami."  Musaddik ya fada cikin zuciyar sa kuwa cewa yayi "wallahi duk sintirin da nakeyi saboda yar ki ce."

Da dare bayan sun gama cin abinci, suna hira wannan al'adar suce kafin su kwanta sai sunyi hira kuma Inda home work a lokacin su Sagir zasu yi, Mami ta dubi Ni'eema cikin nutsuwa tace "Ummin Mami zan tambaye ki amma karki boye min komai ki fada min Gaskiya, duk duniya baki da wata kawar da ta fini haka nima banda Abokiyar shawara kamar ke, ki daura ki sanar min Gaskiya." A hankali Ni'eema tace"Insha Allah matukar na sani zan fada maki Mamina, nayi Alkawari." ta kasara maganar cikin tunanin me Mami ke son tambayar ta.

"Yawwa Ummin Mami, meke tsakanin ki da Musaddik?"  Mami ta tambaya tana kallon Ni'eemar. Sun kuyar da kai kasa tayi tana wasa da abin hannunta "Ummin Mami dake nake magana fa?"  "Mami dazun ne ina wanke uniform din mu shine yace yana sona, amma Mami nifa bance masa komai ba."  tayi maganar kamar za tayi kuka. Murmushi Mami ta saki tace "Ummina tuni na gane Nufin Musaddik, a kanki ba zan hana ki soyayya ba amma ina son ki kama kanki kisa nutsuwa a cikin ranki, ki duba ko ke wacece nice kadai gatan ki, karki dauko min abin da zaisa ni jin kunya, duk da ina da tabbacin Musaddik nutsatstse ne."

Murmushi tayi tace "Mami na indai nine karki damu bazan taba baki kunya ba, ke dai kiyi min Addu'a."  "insha Allah Addu'a kullum cikin yinta muke, Allah ya sa Albarka cikin tarayyan ku. Ubangiji yasa Alhairi zaku kulla."  Mami ta yi maganar tana mikewa domin kuwa dare yayi sosai. "Ummi dauki su Nazir ki kai su daki nikam zanje na Kwanta wallahi duk na gaji." to Mami sai da safe. Nima bacci zanyi, bari na soma kaisu tukun." Ni'eema tayi maganar tana daukan Sagir.

**********************************

Tunda ga wannan rana Ni'eema da Musaddik suka fara gudanar da soyayyar su, wani irin mugun so Musaddik kewa Ni'eema wanda har yake jin in aka raba su zai shiga mawuya cin hali, kaf gidan Babu Wanda yasan halakar dake tsakanin su, har waya ya sawo mata IPhone 7+ wanda da kyar Mami ta bari Ni'eema ta amsa a cewar ta bata son a binda zai bata rai. Kasa da kai yayi yace "Mami kiyi hakuri ta amsa, wallahi babu wani kanana magana ai Ni'eema kanwata ce."  cikin sanyi yayi maganar.

To shi kenan Allah yasa Albarka, Ubangiji ya tabbatar da Alhairi sa, sai dai ina son ka rike amanar Ni'eema don Yarinya ce marainiya." "Insha Allah zan kula Mami kedai kiyi mana Addu'a."

Soyayya sukeyi mai burgewa, tsakanin Musaddik da Ni'eema har baka gane wanda yafi wani son juna. Ni'eema ce zaune a farfajiyan gidan su, game takeyi cikin wayar ta gefe kuma su Sagir ke buga ball, sam bata ji shigowar saba don tayi nisa ga abin da takeyi "He my beauty Gaskiya kina hutawa."  Muryan Musaddik ce ta ratsa kunnuwan ta..........

Dago da kai tayi tana kallon shi cikin murmushi mai k'ayatarwa tace"Barka da zuwa Uncle Fatan ka yini lafiya, ya Mummy da su Maryam?" tayi tambayar tana watsa masa wani shu'umin Kallo. Zama yayi kusa da ita yace "Beauty zaki kasheni da soyayyar ki, Anya kuwa in na rasa ki ba zan iya zaucewa ba?"  zaro ido tayi waje a rude tace "Please Uncle ka daina maganar rabuwa da ta zaucewa, in Allah ya yadda muna tare da juna."  gyada kai yayi yace "Allah ya barmu tare da ke my Beauty..

Suhaila ce ta fito daga bangaren su, cikin wasu tsadaddun kaya, sosai tayi kyau, fita zatayi gidan bikin kawarta, motar Musaddik ta gani a ajiye da alama yana gidan kenan, bangaren Mama ta shiga a tunanin ta can ya shiga, Koda ta shiga babu alamar yana ciki, don haka sai ta fita cikin ranta tana raya yana bangaren Mamin su Nazir.

Tun daga nesa ta hangosu Zaune,Kara bude ido tayi don zaman nasu yayi mata kama da ta cikakkun Masoya wanda suke masifar son junan su, ranta yayi mugun baci da ganin yadda suke zaunen suna Magana kasa kasa, A fusace ta nufi wajen........













Muje Zuwa...

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now