BABI NA BIYU

4.2K 242 1
                                    

NI'EEMA
  ZULAYHEATRANO89

Page 2.

Suna tafe suna hiransu, kawai sai ganin mutum ta yi a gabanta yana sakar mata kyakkyawar murmushi, wanda ya ƙara kawata masa fuskar sa,  wani mummunan faɗuwar gaba ta ji don tunda take bata taɓa ganin shi ba, yauce karon farko da ta taɓa ganinsa a rayuwarta, kuma a koran ganinta da shi har yana sakar Mata murmushi, shine mutumin farko bayan Maminta da ta ga ya sake mata fuskar lokaci ɗaya, cikin tunanin da take yi ne ta ji su  Nazir da sauri sun ƙwace hannunsu tare da zuwa wajen sa suna faɗin “oyo yo Uncle Musaddik” Ɗaukan su ya yi ɗaya bayan ɗaya sannan ya ajesu ya ce cikin wata lallausan murya “heee ! Yan'biyun Mami yanzu na fito daga ɓangaren Mami take cewa kuna school."
“Yes Uncle dawowarmu kenan.” Sagir ya bashi amsa don ya fi Nazir iya magana.
“OK sannunku da dawowa wannan wace ce?” Ya yi tambayar yana nuna Ni'ima.
“Lah! Uncle baka santa ba?  Auntyn muce fa Aunty Ni'eema.” Sagir ya ba shi amsa. “Ni'eema?” Musaddik ya maimaita sunan a zuciyarsa.
Ɗaga kafaɗa ya yi ya ce “To Sagir Nazir ku shiga ciki magriba ta yi.” Ya yi maganar tare da raɓawa ya wuce abinsa.
Nannauyan ajiyar zuciya ta saki, tare da kallon Sagir  ta ce “Wane ne wannan ɗin?”
“Shi ne fa Uncle Musaddik wanda muke zuwa gidansu da Dadynmu.” Gyada kai kawai ta yi alamar gamsuwa da maganar yaron, sannan suka ida shiga ɓangarensu, sallama suka yi Mami dake ta kai kawo tana shirya masu dinner a dining ta amsa, cikin sauri su Nazir suka isa ga Mami suna faɗin “Oyo-yo Maminmu.” Ita ma buɗe hannu ta yi tare da cewa “yawwa 'yan samarina barkan ku da dawowo, ya karatun?
  “Alhamdu Lillah! Ni'eema ta bata amsa.
“Madallah! Oya a zo a cire uniform sai a ci abinci.”
“To Mami.” Suka faɗa suna kwasa da gudu don shiga daƙinsu. Ni'eema ta ɗan ɗaga murya tana faɗin “kai ku bi a hankali fa karku faɗi yanzu zan shigo daki.” har sun shiga ɗakin sai kuma suka fito, tafiya suka fara yi a hankali a haka suka shiga bedroom ɗin.
Ni'ima ta Juyo da kallon ta ga Mami ta ce “Mami ɗazun na manta ban gaya maki ba, Malamin Hausanmu ya ce mu sayi littafin Magana Jari ce, mu je da shi gobe, gashi kuma dare ya yi.” Ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa.”
“Ok! Karki damu akwai wanda nake da shi zan baki, je ki cire Uniform Mamana.” Mami ta yi maganar cikin murmushi.
“Toh.” Ni'ima ta amsa sannan ta nufi bed ɗin tana shiga bata ɓata lokaci ba, ta shirya cikin doguwar riga ta ɗaura ɗankwalin kayan data sanya, toilet ta shiga to yo alwala bata tada sallah ba sai da ta leƙa ɗakinsu Sagir taga har sun tayar da sallah, sannan ta koma itama ta tayar da nata sallar.
Tana idarwa bayan ta yi Addu'a ta tashi, ko tsayawa tulawan Alkur'ani data saba yau ba ta yi ba, don zumuɗin Mami ta ce zata ba ta labarin Abbanta
“oya ku fito mu je dining ku zo da book ɗin home work ɗinku.” Ni'eema ke maganar lokacin da ta leƙa bed ɗinsu
“To Aunty gamu nan zuwa.” Suka bata amsa.
Duk suna zaune a dining ɗin sai ɗiban abinci suke yi, amma ban da Ni'eema da take ci kamar tana tausayin abincin “Assalamu Alaikum.” Shi ne abin da ya faɗa tare da shigowa, a tare suka amsa suna faɗin “Dady sannu da zuwa.” Fuska sake yake amsawa “'Ya'yan Dady kuna nan kun bar Dady da kewarku.” Alhaji Musa Abba kenan mijin Mami Dadyn su Nazir.
Murmushi suka yi gabadaya, “Dady ko da baka zo ba muna gama Assagment zamu shigo.” Nazir ya yi maganar yana kai loma.
Shafa kan yaron ya yi yana murmushi “Dady sannu da shigowa.”  Ni'eema ta yi maganar a nutse.
“ 'Yar Albarka ya karatun? " “Alhamdulillah!” Ni'eema ta bashi amsa. Murmushi ya saki yana kallon Mami ya ce “wato Zainab yau sarautar ta motsa ko magana ba a yi da ni?”
“Ah haba dai Alhaji na bari ne ku gama kai da 'ya'yan naka ai.” Mami ta yi maganar hankalinta kwance. “To ya yi kyau, ni fa idan ina ganin yaran nan tofa ban da sauran matsala, dama shigowa na yi in ga lafiyar ku, Alhamdulillah tun da kuna lafiya bari na isa ciki.” Ya ida maganar yana fita daga falon, don ba Mami ke da girki ba.
  Cigaba suka yi da cin abincinsu, suna kammalawa Ni'eema ta gyara wajen da suka ci abincin sannan suka koma Falo, home work ɗin su Nazir suka soma, bayan sun kammala Ni'eema ta ce masu su je su yi isha'i in za su kwanta su yi Addu'a. Babu musu suka tafi don sosai suke da buƙatar hutu, bayan sun wuce Ni'eema ta kalli Mami sai kuma ta kwabe fuska, sa rai Mami ta gane nufin ta amma sai ta basar ta ce “Ummina yau babu bacci da wuri ne gobe akwai school?” Da sauri ta ce “Mami.” Sai kuma ta yi shiru. 
“Na san abin da ya zaunar dake, to sai ki bude kunnuwa don jin ko wace ce Ummyn Maminta.” Cigaba da magana Mami tayi.
  “Haƙiƙa Khadija 'ya ce tsarkakakkiya kamar ko wanne ɗan sunnah, mutane da yawa suna maki kallon mara tushe mara asali amma sam ba haka bane da Mahaifinki har da kakanninki.”
“To kuma Mami ina suke?” Ni'eema ta yi saurin tambaya. 
“Kwantar da hankalinki yau za ki ji komai sai dai ina rokonki da Allah ko bayan raina karki neme su matuƙar dai ba sune suka neme ki ba, fatan za ki yi min wannan Alƙawarin?”
Ba tare da tunanin komai ba Ni'eema ta ce ta amince. 
“Ni'ima 'yar Halas ce sai dai mahaifinta ya sallama min ita tun kan tazo Duniya.”

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now