TALATIN DA BIYAR

2.8K 165 0
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*





Page *67~68*

Allahumma amin, duk suka amsa, sannan suka ɓalle da hira cikin nishaɗi, duk da dai Ni'eema ba wani lafiya sosai gare taba.

Amma haka ta daure su kai ta yin hira har nisan lokaci, Nazir ne ya shigo falon da wayar Ni'eema a hannu yana faɗin " Aunty tun ɗazun ake ta kiran wayar."

Amsa ta yi tare da karawa wayar a kunne ta fara yin sallama cikin daddadan muryan ta, Abdul-Nasir daga ɗaya ɓangaren ya amsa tare da lumshe ido, don muryar ta saukar masa da kasala.

Tabbas a irin yadda ta yi magana da kusa da shi take, babu abinda zai hana shi yi mata kiss, sai da ya daidai ta nutsuwar sa sannan ya ce "Kina ina ne haka tunda gari ya waya bamu haɗu ba?" "Ƙara ƙasa da murya ta yi ta ce" gani a falon Dady kusa da Babana." Wani irin miƙewa ya yi tare da faɗin "Da gaske Khadija kina tare da mahaifinki?"

Da yake tunda ya yi sallar Asbah yake barci bai ma san da zuwan su ba. "Allah da gaske ka zo ka ga ni." Ni'eema taba shi amsa.

Jallabiya kawai ya sura sannan ya fita daga ɓangarensa, yana ganin motor YMB Investment a harabar gidan ya yarda da maganar Ni'eema, bai zame ko'ina ba sai falon Aunty Mama.

Sallama ya yi tare da shiga falon, kusa da ita ya zauna ya soma gaisar da ita, fuska sake ta amsa gaisuwar ta ce"sai yanzu ka tashi hala?"

"Wallahi kuwa Aunty ko break ban yi ba, yanzu ma Khadija ce ta sanya ni fitowa, domin ta sanar mini da zuwan mahaifinta, shi ne na bari na zo na sanar dake zuwan na shi, yanzu haka yana cikin gidan nan tare da 'yar shi Khadija." Ya yi maganar yana kallon Aunty Mama.

Wani harara ta watsa masa ta ce "Hala na zama sa'ar wasar ka, ai wannan matar taka bata da uba, ina jiye maka ranar da 'ya'yanka za su fahimci haka, saboda na daɗe da sanin kai yanzu ka daina ɗaukar duk maganar da nake yi maka, amma akwai ranar ƙin dillanci.

Miƙewa ya yi ya ce "Wallahi Aunty Mama ki fita ki gani suna falon Dady." Daga haka ya fita.

Kai tsaye Falon Dady ya shiga, cikin sallama, sannan ya fara gaida mutanen ɗakin, cikin girmamawa, fuska sake suka amsa ma shi.

"Alhaji wannan shi ne babban ɗan namu?" Alhaji Yaseer ya tambaya. "A'a da yayyinsa, amma shi ne ke zaune a nan. Dady ya ba shi amsa.
"To mu dai bari mu tashi mu je gida, tunda an gaggaisa Baby zaki bi mu ko?" Alhaji Yaseer Ya yi maganar ya kallon Ni'eemar.

"Sai dai ka tambayi mijinta ga shi nan zaune gabanka." Abbu wato Alhaji Yusuf shi ya yi maganar. Duk kallonsa suka yi suna mamakin maganarsa. Hajiya Kubra ta ce "Au ashe har suruki gare mu? Ma sha Allah gaskiya na ji daɗi."

Murmushi kawai Alhaji Yaseer ya yi, ba tare da ya ce komai ba, domin wani kunyar da ya lulluɓe shi ba kaɗan ba ne 'Ashe har suruki gare shi?' Ya yi wa kan shi tambayar a ƙasan zuciyar shi.

Mami miƙewa ta yi ta bar masu falon, tana fita Hajiya Kubra ta bi ta, don take ta ji tana ƙaunar Mami har cikin ranta, falon Mamin suka shiga inda suka yada zango a kan kujeru suka fara hira. Lokaci ƙalilan shaƙuwa ta shiga tsakanin Mami da Hajiya Kubra. "Baby me kike so a duniyar nan in yi maki?" Alhaji Yaseer ya tambaya Ni'eema. Girgiza kai ta yi ta ce" Baban ni kam ban son komai, amma ina son a bawa 'yan'uwana kyautar sabbin motoci... Daidai da shigowar Aunty Mama falon, sai da gabanta ya faɗi jin furucin Ni'eemar.

"Ok har su nawa ne yanzu sai na sanya a kawo?" "Su uku ne Baba Ni'eema ta ba shi amsa. Bai jira komai ba ya soma kiran waya, take ya faɗi buƙatar Ni'eemar. Gaisar da su Aunty Mama ta soma yi, cikin zuciyar tana faɗi take 'lallai kuwa wannan shi ne mahaifin yarinyar nan, to dama tana da uba matsayin Alhaji Yaseer me ya kawo ta agolanci nan gidan?' Ta yi wa kanta tambayar da babu amsa.

Miƙewa Ni'eema ta yi ta ce " Babana zan je in kwanta na gaji."
"To a tashi lafiya yar Babanta, in kuma baki tashi da wuri ba har muka tafi, to sai dai mijin ki ya kawo ki ko zuwa gobe ne, sannan baki faɗi sunan masu motar ba, don da rasit da komai za a kawo?"

*Suhaila, Maryam, Hafsat* sune masu motocin, Ni'eema ta fada tana cigaba da tafiya. Gabaɗaya da kallo suka bi ta, don tsantsan mamaki, su waɗanda suke mata gorin motor ya yin zuwa school, yau su takewa kyautar motor. Nan take jikin Aunty Mama ya yi sanyi, har ta ji ta soma sauke makaman yaƙin da ta ɗauka a kan Ni'eema.

Abdul-Nasir na ganin Ni'eema ta fita, shi ma ya yi saurin bin bayanta tare da riƙo hannunta, ya yi ɓangaren shi da ita, bata ce komai ba, don dama tana da buƙatar taimakon, da ƙyar take daga ƙafarta. A kan kujeran falo ya zaunar da ita. Ya ce" Khadija Allah ya maki Albarka, haƙiƙa ina farin cikin samun ki matsayin matata, kina da hali mai kyau, ba ki rama sharri da sharri, sai dai ki rama sharri da Alhairi, ba zan gaji da faɗa maki irin son da nake maki ba."
"Sai abu na gaba shi ne ina taya ki murnan bayyanar mahaifin mu wato Alhaji Yasser."

Murmushi ta saki irin na ƙarfin hali ta ce " Nagode Yayanmu, amma Please ka barni barci nake ji."
"Ok mu je bedroom sai ki kwanta, ya yi maganar yana ɗaukar ta kamar wata baby, bai zame da ita ko'ina da ita baa sai kan gadon, baby bari na rage maki kayan jikinki, sai ki fi jin daɗin barcin." Ya yi maganar yana zage mata zip ɗin rigar.

Duk kayan jikin ta sai da ya cire mata, hannu ya kai yana tab'a dukiyar fulaninta, "Baby ina son waɗannan abun, suna matuƙar burge ni." lumshe ido Ni'eema ta yi bata ce komai ba, tana jin daɗin yadda yake mata, sai dai kuma bata iya mai da masa martani.

Domin yadda jikin nata yake, kiss ɗin ta Abdul yake kota ina, ɗago kai ya yi ya ce " khadija yau har da na celebrity ɗin ganin Babanmu sai na yi, sau uku zan yi, a lokaci d'aya." Ware ido ta yi tare da tashi zaune, ta kai fuskar ta daf da tashi, ta manna masa wani hot kiss a kumatu, wanda har numfashi sa sai da ya ɗauke na minti na, tace "haba Yayanmu ajiyar ka fa take ba ni wahala, ina laifin ka yi sau ɗaya, sai ka bar ni in yi barci, anjima da dare sai ka ƙara don yau a nan zan Kwana."

Dogon ajiyar zuciya ya ja, don yadda Ni'imar ta yi masa maganar ta tafi da imaninsa, kasa magana ya yi sai cigaba da jagolgolata yake son ransa, sai da ya ji ya gamsu kana ya barta, tare da faɗawa toilet, ko kafin ya fito tuni barci ya kwasheta...






Mu je zuwa.

NE'EEMA COMPLETEWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu