ASHIRIN DA SHIDA

2.7K 166 1
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

Ina matukar godiya da irin Addu'anku a gareni, godiya mara adadi, fatana Allah ya bar zumunci da kaunar juna

Deducated to *sweet sadee* ina sonki sosai irin mai tasowa daga zuciyar nan, ina mugun sonkiiiiii irin over din nan 😘😘😘







Page *49~50*

Daidaita nutsuwarsa ya yi tare da faɗin ina zuwa Aunty Mama, yana gama faɗin haka ya kama hannun Ni'eema ya nufi bedroom da ita a bakin gado ya mata masauki ya kalleta cikin haɗe rai ya ce "Wallahi in ba ki yi min shiru ba sai na falla maki mari kuma karki yarda Aunty Mama tasan kina ciki inko ba haka ba duk abin da ta yi maki babu ruwana." Yana gama faɗin haka ya yi waje. Bude ƙofar ya yi yana faɗin barka da dare Aunty Mamana." Murmushi ta saki ta ce "Yawwa ɗan Albarka ashe baka yi barci ba?” Cikin ransa ya ce ‘Yo ta ina zan yi barci bayan Daddy ya yi mini gata ya haɗa ni aure da irin macen da nake so.’ Amma a fili sai cewa ya yi "Wallahi kuwa Aunty yanzu dai nake ta shirin yin barcin."

“Ok dama zuwa na yi na ji wane ne irin shawara ka yanke na maganar auranka da yarinyar can..?" Zufan da ya tsatsafo masa ya share ya ce "Ni fa wallahi Mama kawai na amshi auran nan ki yi mana Addu'ar fatan Alhairi donin yarinyar tana da hankali.” Zaro ido ta yi ta ce "Ok ya yi kyau tunda ka zaɓi farin cikin wasu a kai na, zan yi maganin rashin kunyarku daga kai har ita, ina faɗa maka yarinyar nan fa babu wanda yasa ubanta, wato kai kana son a ce 'ya'yanka sun tashi basu da Kakannin wajen uwa ko? " "Kai Aunty Mama wai wa yace maku bata da uba tana fa da ubanta, kuma In Sha Allah za ku gan shi da idonku."Ya yi maganar cikin ɓacin rai. "Kai da alla matsa shashasha kawai to ina ruwana da ganin ubanta, ni fa son tane bana yi kuma ba zan sota ba, dama kan maganar auran hafsat ne ya kawo ni ka san ansaka ranar bikin to shi ne ta lissafa mini abin da take so."

“Ok Aunty Mama ai ma da kirana kika yi zai fi, amma duk da haka babu damuwa zuwa da safe sai mu yi maganar tunda dare ya yi, ɗazun na tura maki wasu kuɗi alert bai shigo ba ne? Abdul-Nasir ya yi saurin sauya maganar. Washe baki ta yi ta ce "Na ga kuwa shigowar alert amma na yi tunanin MTN ne shi yasa ban duba ba, Allah ya yi Albarka." Ta yi maganar tana miƙewa. Karaf idon ta ya sauka a kan hijjab ɗin NI'EEMA, kallon hijjab ɗin ta yi ta ce " Abdul-Nasir wannan mene ne kamar hijabi?"  Ta yi maganar tana ɗaga hijjab ɗin. Sai da Abdul-Nasir ya firgita. Ya ce "Eh Aunty Mama hijjab ne ɗazun su Nazir suka shigo da shi mantawa suka yi basu ɗauka ba." A diririce ya yi maganar. Harara ta watsa masa ta ce "Abdul-Nasir yaushe ka soma yi mini ƙarya ne haka? Uban mai zai sa su Sagir ɗin su shigo da hijjab har ya kawo warhaka baka ɗauke ba? Kai ko dai abin da nake tunani ne kake aikatawa? Ya zama dole na duba bedroom ɗinka babu mamaki yarinyar nan tana ɗaki nan shi yasa ɗazun da ƙyar ka buɗe mini komai."  Ta yi maganar cikin masifa tare da nufa hanyar bedroom ɗin.

Abdul kenan namijin duniya ko a kwalarsa, sai ma ɗaukar wayarsa ya yi ya soma latsawa. Ni'eema da tun shigowar Aunty Mama hankalin ta ke tashe, tana jin Aunty Mama ta ce zata shigo bedroom ɗin har fitsari sai da ta saki jikinta na wani irin rawa, numfashinta har yana neman ɗaukewa tsabar tsoro, da sauri ta shige bayan labule ta ɓoye, haka Aunty Mama ta shiga bedroom ɗin har toilet sai da ta duba, ganin babu kowa yasa ta fita ko tsayawa a falon bata yi ba ta kama hanyar fita "Aunty Mama sai da safe." Abdul-Nasir ya faɗa.

Aunty Mama na fita, ya saki ajiyar zuciya, zuwa ya yi ya rufe ƙofar sannan ya shiga bedroom ɗin, Ni'eema ya gani tsaye jikinta yana rawa zufa ya wanke mata fuska, dariya ya saki ganin yadda Ni'imar take. Mamaki ya kama Ni'eema na yadda yake dariya "Dama yana dariya haka?" ganin yaki daina dariyar yasa ta kama hanya zata fita, da sauri ya riƙo hannunta, ta yi saurin fisgewa don ta ji haushi sosai musamman dariyar da yake mata. Kuka ta fashe masa da shi ta ce "Ka sakar mini hannu ni ɗaki zan tafi." Rungumeta ya yi tsam a ƙirjinsa ya ce "Haba *Khadijata* mene ne na yi fushi za ki tafi, bayan kin san har yanzu ban samu nutsuwa dake ba."  A hankali yake mata maganar yanayi yana cigaba da shafa ilahirin jikin ta. Kawar da kai ta yi ta ce "Ba kaine kake mini dariya ba?"  Na daina ya faɗa tare da cire mata rigar barcinta, tana rungume a jikinsa suka isa gadonsa.

Tashi ta yi ta zauna tare da kare ƙirjinta ta ce "Please ka barni na koma ɓangaren Mami, wallahi tsoro nake ji kar Aunty Mama ta dawo?"  "A'a yau kam a nan za ki kwana domin mu raya wannan daren." Ya yi maganar yana ƙara matsa bres ɗinta. " Please Yayanmu tsoro nake ji fa." Cikin hawaye ta yi maganar.  "Tsoro kuma tsoron wa to?"  "Tsoron kar Aunty Mama ta kuma zuwa." Baki yana rawa ta ba shi amsa.  "No Khadija Aunty Mama ba zata kuma zuwa ba, kwantar da hankalinki kin ji?" Da kai ta amsa. cak ya tsaya da abin da yake ya ce "Khadija da gaske ne ba'a san wane ne mahaifinki ba?" Ya yi mata tambayar fuskarsa babu wasa. Ɗaga kai ta yi ta ce "Ina da mahaifi sai dai ban san shi ba, haka kuma ban san ko yana raye ba ."  Ta ƙarasa maganar cikin kuka. Tausayinta ya kama shi "mene ne sunan mahaifinki? Ya tambaya. "Mami ta ce mini sunan shi Yaseer Mu'azzam Baba." Ni'eema taba shi amsa. Ja da baya Abdul  ya yi yana kallon Ni'eemar jin ta ambaci sunan Alhaji Yasser Mu'azzam Baba." Alhaji Yasser Mu'azzam Baba? *YMB Investment* kike nufi?" Girgiza kai ta yi ta ce "Ni fa ban san shi ba."  Ta ba shi amsa.



Mu je zuwa...

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now