BABI NA GOMA SHA DAYA

2.8K 172 1
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

Dedicated to *Hussain ATK & Hassan ATK* '''sannun ku da kokari Allah ya bar zumunci, ana jone irin har abada din nan''' 🤝🤝

Page *21~22*

Da yake Mami ke da girki duk sauran fita suka yi suka barta a sashin Dadyn, zama ta gyara tare da fuskantar shi, kallon ta ya yi ya ce "Zainab da ganin bakinki da magana?" Murmushi Mami ta yi ta ce "Sosai ina da magana Alhaji."  Ta yi maganar cikin tausasa murya.

"Ina jinki Amaryata nasan tunda kike son mini magana, to mai muhimmanci ne don haka ina sauraro." Ya dire maganar yana muskutawa.

"Har ga Allah Alhaji ban so hukuncin da ka yanke ɗazun ba, a gaskiya ban ji daɗi ba sam, da kabar Ummi ta cigaba da zuwa makaranta a nafef kamar yadda ta tasaba." A hankali Mami take maganar cikin nutsuwa.

Gyaɗa kai Dady ya yi ya ce "Zainab kin ban mamaki, ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba, idan na fahimci maganarki wato kina son nuna mini cewar  ba ni ne na haifi Ni'eema ko?" Cike da ɓacin rai Dady ke magana.

"Ka yi haƙuri Alhaji amma ban yi maganar nan wata manufa ba, in ranka ya ɓaci don Allah ka yi haƙuri hakan ba zai sake faruwa ba." Murmushi Dady ya yi domin yana son halayyan Mami don mace ce mai fahimta da hangen nesa, Allah sarki Zainab mai tunanin gaba wato burinta a zauna lafiya , a fili kuwa sai cewa ya yi "Karki damu Zainab na fahimce ki amma ayi yadda nace ɗin." "An gama Allah Ya zaɓa mana mafi alhairinSa."
"Amin." Dady ya amsa.

Tunda Dady ya yi wa su Maryam magana, sai Ni'eema ta samu sauƙi daga wajensu duk da ba wai hira suke yi ba amma ta samu ɗan sauƙi, domin in bata gama shiryawa da wuri ba, har zama ake a jira ta, sai dai fa dalilin maganar da Dadyn ya yi masu wata sabuwar tsanar suka ɗaura mata, harara kawai ke haɗasu sai habaice-habaice, maganar zuwa makaranta kuwa yanzu a motar gidan take tafiya, Mami ta so hanata shiga amma ganin yadda Dady ya nuna rashin jin daɗinsa yasa ta haƙura.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Fitowar su daga aji ke nan ita da ƙawarta Siyama, sun tsaya yin rubutu, shi yasa basu fito da wuri ba, duk filin makaranta babu mutane sai yan ajinsu, kallon Siyama ta yi tana cewa "Yau kam naga boni motar gidan mu har sun wuce, gashi babu kuɗi a hannuna, Mami ta ba ni kuɗin na manta dasu a kan kujera, yanzu kam ban san ya zan yi ba." Ni'eema ta yi maganar kamar zata yi kuka, Siyama ta saki murmushi tana faɗin
   "Haba ke kuwa Ni'eema mu je sai direbana ya saukeki mana." "A'a ki bar shi kawai tunda ba hanyar mu ɗaya ba, zan hau nafef idan ya sauke ni sai na amshi kuɗi wajen Mami na ba shi." Juyin duniya amma fir Ni'eema taƙi, haka Siyama ta gaji ta bar ta.

Tafiya take yi hankali kwance cikin nutsuwa, har ta fita baƙin titi wajen da zata samu abin hawa, ta zo tsallaka titi sam bata lura da zuwan motarba duk yadda ta so kaucewa motar hakan bai faru ba, sai da motar ta isa wajen da take tare da bugar ƙafarta, hakan ya sanya ta hantsila gefe, “Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raju'un!" Shi ne abin da mai motar yake faɗa. Da sauri ya yi fakin motar tare da fitowa, wajen da take tsugune riƙe da ƙafa ya nufa "Sannu 'yata tashi mu je in kai ki asbiti a duba maki ƙafar." Ɗago da kai Ni'eema ta yi cikin sanyin murya ta ce “A'a Baba ba sai ka kai ni Asbiti ba saboda ban ji ciwo sosai ba.”

“BABA” Ya maimaita sunan, tunda yake a duniya bai taɓa jin an ambace shi da sunan Baba ba sai yau, wani irin faɗuwar gaba ya ji dalilin muryarta sai ya ji kamar yasan muryar.

Ni'eema kam miƙewa ta yi da niyyar tafi duk da dai ɗingasa ƙafar take yi, domin ta bugu,  “Tsaya mana 'yar Baba kin ga fa yadda ƙafar take mu je asbiti a duba maki ita." Cikin tausayawa yake yi mata magana.
  To kawai Ni'eema ta amsa da shi, saboda ba ta ƙaunar yin musu da wanda ya girme mata, ballantana kuma wannan da take ganin ya haifeta, don haka motar sa ta shiga kamar yadda ya buƙata, shi kuma ya ja suka tafi, wani haɗaɗɗen asbiti suka shiga wanda daga gani kasan sai wane da wane suke zuwa asbitin, suna fakin, ya fita ya zaga inda take ya buɗe mata ƙofar motar yana cewa, “Fito mu shiga ciki sai a yi maki treatment ɗin wajen."

“To Baba.” Ni'eema ta sake amsawa a karo na biyu.
Ba ƙaramin daɗi yake ji ba idan ya ji Ni'eema tana ce masa Baba, a haka suka shiga babu wani ɓata lokaci aka gama mata treatment ɗin sannan suka fito, motar ya kuma buɗe mata ta shiga, shi ma ya zaga ya shiga kallon Ni'eema ya yi ya ce "bari na saukeki gida tunda ciwon da sauƙi." Gyaɗa kai ta yi. Cikin zuciyar tana mamaki yadda babban mutum kamar wannan mai tarin kuɗi, domin ko motar sa ka kalla ya isa ka gane matsayin sa ballantana aje ga suturar dake sanye a jikinsa, fatar jikinsa kam kallo daya zakayi mata kasan hutu ya samu wajen zama, ta yi mamakin yadda ya bugeta da mota har  yake nuna yana jin tausayinta, ‘dama akwai masu kuɗin dake da tausayi haka?’ Bata kai da ba kanta amsa ba, ta ji yana tambayarta wane layi za su bi? Ta fara yi masa kwatance har suka shiga layinsu.

A daidai ƙofar gidan ya yi fakin, domin tafiyar n daga nesa ta nuna masa gidan, tana ganin ya tsaya da motar cikin sauri ta kai hannu da niyyar buɗe ƙofar, maganar da ya yi ce ta sanyata tsayawa
  “Haba 'yar Baba baki faɗa mini sunanki ba kike shirin fita?” "Ayya yi haƙuri Baba sunana Khadija." Ta ba shi amsa da kulawa.
  “Suna mai daɗi Allah Ya yi maki Albarka, ki cigaba da karatu kin ji ki dage ban da wasa ga magungunan ki Allah Ya ƙara sauƙi."

“Nagode Ni'eema ta fada tana fita daga motar, tana masa godiya, da ƙyar ta kai kanta sashin su don sosai ƙafar ke mata zafi, Mami dake zaune a Falo hankalinta a tashe ganin har uku da rabi ta yi Ni'eema bata shigo gida ba, tuni ta soma tunanin zuwa makarantarsu don ta ji ko lafiya, wayar Daddy ta kira sai dai bai ɗauka ba, abin da ya hana ta fita ke nan ta zauna tare da zuba tagumi. Kamar a mafarki ta ji sallamar Ni'eemar da sauri ta miƙe tana faɗin Ummiee lafiya kike sai yan..? Bata gama rufe bakinta ba ta yi turus ganin yadda Ni'eema ke jan ƙafa
"Inna Lillahi Ummina me ya same ki?" Mami ta kuma maganar a ruɗe tana isa wajen da Ni'eemar take.

“Mami mota ce ta bige ni bayan an tashe mu daga makaranta.” Ni'eema taba Mami amsa.


NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now