ASHIRIN

2.6K 211 7
                                    

NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

Page *37~38*

This page is dedicated to *Nafeesa Ankеrh*
Ina yin ki irin sosai din nan &  I love you wujiga wujiga 😘😘😘😍

"Haba Malam ka kuma dubawa, wallahi muddin ta Auri ɗana duk wani farinciki na gushewa zai yi, saboda na tsani yarinyar sosai bana ko ƙaunar ganinta a cikin gidan, ballantana kuma a ce ta zama surukata, duk ma wannan mai sauƙi ne don kwata-kwata ba'a san ubanta ba ta ya zan so hada zuri'a da ita, nifa wallahi Malam in zaka yi aikin ka yi harda uwarta, don itabma ta tsare mana komai na gidan." Jiki a saɓule take maganar kai da gani kasan bata cikin nutsuwa.

"Gaskiya Hajiya abin da na gani shi nake sanar maki, sai dai kuma akwai wata hanya da nake ganin in aka bi za'a dace." da sauri ta ce "ina jinka Malam faɗi na ji don na matsu da samun mafita."
  "A'a bafa magani zan baki ba don ni dai bani iya wa da harkan yarinyar, sai dai kina iya ba ɗanki umurnin koda ya aure ta tofa karya kuskura ya kasance ta, domin matuƙar ya kasance ta tofa taki ta ƙare saboda wani irin mugun sonta ne zai shiga zuciyar sa, gashi kuma a dubawar da na yi aure nan kwana kusa za'a yi." duk maganar da yake bai ɗago ba balli ya kallace ta.

"Kai ni kam Zainab da ɗiyarta sun zamomin ciwon ido, yanzu ina kallo ɗan da na haifa zai auri zuri'ar Zainab." hankali tashe take wannan sambatun.  "To dai ki ɗauki shawara ta zata maki daɗi."  miƙewa Hajiya Lantana ta yi ta ce "To Malam mun gode bari mu tafi, amma da mun so koda haukatar da ita ne ayi koma kashe ta gaba ɗaya."  zaro ido Malam din ya yi ya ce kin san halina bani da Imani amma tunda na ce maki aikin ba zai yiwu ba to ki yadda, amma nan gaba kuna iya dawowa." gyada kai kawai suka yi sannan Aunty Mama ta aje masa kudi, sannan suka yi masa sallama.

Cikin motar Hajiya Lantana suna tafiya kowa da tunanin sa, ita Aunty Mama tunanin ma rasa Wanda zata yi ta yi, minti kaɗan sai ta saki tsaki "Kin san mene ne Hajiya?" Hajiya Lantana ta yi maganar tana kallon Aunty Mama. Girgiza kai kawai tayi. "ok yanzu kawai mubar maganar Ni'eema mu koma ta Suhaila da Musaddik don sune a gaban mu."  kin kawo shawara amma bari na gama da wannan matsalar dake gaba na.

Suna zaune a falon su sai hira suke hankali kwance, sallama ya yi tare da shiga falon, amsawa suka yi tare da bin sa da kallo, da sauri mommy ta ce "Musaddik lafiya kuwa na ganka haka?"  zama ya yi a kujera tare da sauke ajiyar zuciya, shi ma Dady haka ya soma tambayar sa. Ɗan murmushi ya yi ya ce "Dady  please ka taimaka min wallahi in na rasa ta ina iya shiga wani hali."  ya kai ƙarshen maganar tare da zubewa ƙasa alamar roƙo.

Hankalin su ya tashi musamman yadda ya fita a hayyacin shi lokaci ɗaya " haba Musaddik duk duniya babu wanda zaka sanarwa da matsalar ka kamarmu, don haka faɗa min ko mene ne kuma ko yar wace ce In Sha Allah zan nemar maka auran ta a yau."  " Dady  ba kowa bace illah Khadija yar abokin ka Alhaji Musa."  bakin sa na rawa yake maganar. "Ma sha Allah haba kai kuwa dama akan yar Alhaji Musa kake cewa zaka rasa ranka, to kwantar da hankalin ka yanzu zan kira shi mu yi maganar."  Dady ya yi maganar cikin jin daɗi.

"Ban gane ba Alhaji wace ce Khadija a gidan don ban santa ba?"Mommy ta yi tambayar cikin mamaki. " kin santa sai dai baki san sunan ta haka ba, yar wajen Mami ce Maman su Sagir *NI'EEMA*." Musaddik ya bata amsa.

Wani irin zabura ta yi jikin ta na rawa hankalin ta ya yi mugun tashi don bata taɓa kawo haka a ranta ba "Ni'eema"  ta maimaita sunan. "Gaskiyar magana ba zai tab'a yiwuwa ba don wallahi ba zan haɗa zuri'a da shegiya ba ta ya, zaka ce wata Ni'eema to tun muna shedar juna ka sake tunani don ba zaka aure taba."  kallon rashin fahimta Dady ke mata ya ce "Ban fahimci maganar kiba, akan wane dalili zaki ce ba zai aure taba, to bari ki ji yanzu nan zan kira Alhaji Musa kuma kan maganar auran don haka babu ruwan ki da auran sa, kuma a ina kika ji ance shegiya ce?"

"Alhaji kenan ai duniya ta shaida bata da uba, don tunda aka haifeta babu wanda ya tab'a zuwa da sunan shi ne ubanta, don haka aure tsakanin ta da Musaddik babu shi matuƙar ina numfashi, 'yar talaka ma ban so ya Auro ballantana shegiya marar asali?”

Shi dai Alhaji Ahmad bai ce mata komai ba, sai ma zaro wayar sa da ya yi ya soma kiran layin Alhaji Musa bigu biyu ya dauka, bayan sun gaisa ne Alhaji Ahmad ya soma masa bayanin dalilin kiran, hankalin Dady ya tashi da jin maganar abokin nasa,, amma sai ya ce masa su haɗu a ofis ɗin sa gobe don tattaunawa. A haka suka tsaya.

NI'IMA ce zaune a falo, suna hira da Mami don daga shekaran jiya zuwa yau ta ɗan samu sauƙin damuwar da take ciki, wani programs ake Gabatarwa a tashar liberty T.V da wani mutum wanda ya ɗauki hankalin su ita da Mami "Lah Mami wallahi na taba ganin mutumin nan." Ni'eema ta yi maganar tana nuna t.v. A razane Mami ta ke kallon Ni'eemar bakin ta har rawa yake ta ce “A ina kika san shi?" Ni'eema ta yi mamakin lokaci ɗaya hankalin Mami ya tashi. "kai Mami sau ɗaya fa na taɓa ganin sa yana da kirki wallahi gashi mai kuɗi."  duk wannan bayanin da Ni'eema ke yi Mami bata fahimci komai ba ciki, don tuni ta afka tunani har abada ba zata taɓa manta fuskar nan ba...

Hmmmm to shi kuma wannan waye? Fan's sai kun biyo ni don jin yadda zata kaya..

😭😭😭😭😭😭😭Allah sarki ni Ahe ba ni da masoya.

Mu je zuwa.

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now