BABI NA BIYAR

2.9K 204 2
                                    

*NI'IMA*

Written by *Zulaiha Rano*

           

Ina fita wani sabon kuka na barke da shi, akwatina na ɗauka wanda maigadin ya aje mini a ƙofar shiga falon Hajiya , tafiya nake ina share hawaye har na kai bakin get ɗin, hankalin maigadin ya tashi ganin irin kukan da nake yi "Hajiya lafiya kuwa?"  maigadin ya tambaya. "Babu komai Baba dama kaina ke ciwo." Na ba shi amsa.  "oh to Allah Ya baki lafiya." maigadin ya yi maganar yana buɗe mini ƙofa. Amin na amsa tare da fita.

Dubawa na yi gabas da yamma, kudu da arewa tunani nake ta hanyar da zan bi, haƙiƙa ina tunanin ta yadda zan nufi gidan mu a wannan yanayin tabbas na san tun daga yanzu har ƙarshen rayuwata cikin wahala kawai zan kasance, don matar Baba Habibu da shi kansa Baba Habibun ba ƙaunata suke yi ba, gashi kuma sune kaɗai gatana a duniya sai dai ba su sona kuma sun gaya min baki da baki sun kuma nuna min a aikace don sune mutanen farko da suka saka ni a wannan halin da nake ciki.

Cikin dakiyar  zuciya na kuma taran Nafef kai tsaye unguwar da na yi rayuwar ƙunci da baƙin ciki muka nufa mai Nafef na sauke ni na biya sa kuɗin sannan na fara jan akwatin wani irin faɗuwar gaba na ji ganin Baba Habibu zaune a ƙofar gida, ji na yi kamar kar na ƙarasa amma ina aikin gama ya gama don shi ma ya gan ni, fuskar sa haɗe sai zubga mini harara yake, da taimakon Hasbinallahu wani'imal wakil na isa wajen da yake tare da durƙusawa.

Murya na rawa na ce "ina yini Baba."  kallon sama da ƙasa ya yi min ya ce "da ban wuni ba za ki ganni? To tauraruwa mai wutsiya wacce ganin ta ba alheri ba, daga ganin zuwan ki ba da abin arziki kika zo ba, mai ya kawoki?"  ya yi tambayar cikin tsawa. Takaddan  hannun na na mika masa jiki na rawa na ce "Baba cewa ya yi na je gidanmu shi ne ya ban wannan takardar." na ƙarasa maganar cikin hawaye.

La'ila ha illal lahu "Zainab wato sai da kika kase auran ki ko?"  "Wal wallahi ban kashe ba shine ya saken." na yi maganar ina cigaba da kukana. Harara ya sa ke min, wanda ya sa hantar ciki na kullewa da sauri ta ja akwatin tayi cikin gidan, don sanin halin Baba Habibu yana iya dukan na anan wajen.

Matar Baba Habibu tana aikin ta sai jin sallama na tayi, cikin washe baki ta amsa a tunanin ta kwalema Zainab ta kawo mata, bata gama tunanin ba sai jin sababin mijin ta dake shigowa ta yi, a'a Kki dai wallahi Habibu kana da matsala mene ne kuma na yin masifa don tazo gidan nan, laifine don ta kawo mana ziyara? " " dalla rufan baki wayace maki ziyara ta kawo? Ya cigaba to bari ki ji auranta ta kashe shi ne ta dawo mana nan. "

Cikin sauri ta ce" Da gaske Habibu Zainab ta kashe Auranta? " takardar ya mika mata ya ce" ga zahiri kin gani saki har uku. " " saki uku fa ks ce Habibu? Gaskiya Zainab kin cucemu kin kuma cuci kanki ashe ke din baki son ci gabanmu tun da har kika rufe mana hanyar samun arzikinmu, to wallahi tun da haka kika zaba kin samu kaf aikin gidan nan ke ce da yin sa ko kina so ko baki so. "

" Tunanin zata zauna a gidan nan kikeyi kenan? Hmm ai bata da wajen zama a nan sai dai ta yi gaba." Baba Habibu yayi maganar cikin fushi. "Haba Habibu idan kakoreta kuma ina zata kawai barta a matsayin dana bata, gadai ɗakin kwana amma maganar mu bata abincin mu babu ita kuma dole ta yi mana bauta."

"To ai shi kenan tun da kin ce haka, ta zauna ga dakin nan. Uban me ya haɗaku har ya sakeki koko kin yi masa halin uwarki ne na rashin mutunci don uwarki ba mutunci ne da ita ba? " kaina a kasa nace" ban yi masa komai ba cewa ya yi baya son cikin dake jikina, har ya kaini Asbiti a kan a zubar shi ne naki yadda shi ne ya ce na zaba ciki ko Aure, ni kuma na ce masa ciki shi ne ya ban saki. "

Ka ji shashasha wato kin zabi ciki a kan auran ki, ke ga mai son haihuwa ko kin kyauta zako kiga kin zabi ciki, inba ke baki da hankali ba ai sai ki zabi auran ki in ya so daga baya wani cikin za ki samu, da yake ke ɗin daƙiƙiya ce ai gashi ya sakeki sai ki zauna, amma ba abincin gidana babu ruwana da sabgarki ko ki mutu ko kiyi rai........



Nice Taku.

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now