ASHIRIN DA BIYU

2.8K 165 7
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

Dadicated to *AYSHA ALIYU GARKUWA* '''ina sonkiiiiii irin over din nan,Allah ya raya mana Jabeer cikin Addinin islama, ana mugun jone irin har abada ɗin nan.'''

🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀  *Hafsat Bello ikon Allah typing mijin Mum dinmu ya tsaya kenan?*










Page *41~42*

Kallon Ni'eemar ya yi  cikin rashin fahimta ya ce "Ban gane ba wacce suhailar?"  ƙaramin murmushi ta yi ta ce "Suhaila dai ta nan gidan ƙanwarsa Yayanmu Abdul wallahi tana sonka na daɗe da sanin Suhaila tana sonka, don haka kai ma ka sota matukar kayi min haka zan yi farin ciki."  girgiza kai ya yi ya ce"ina Ni'eema ba zan iya auran Suhaila ba, yarinyar bata da kunya ko kadan."Musaddik ya ƙarasa maganar tare da jan ƙaramin tsaki. "haba uncle kai fa ka ce duk abin da na ce zaka yi, to please ka Auri Suhaila shi ne kaɗai abin da zaka yi raina ya faranta."  Na ji amma please ki ban lokaci zan yi tunani don gaskiya kina son sanya ni cikin matsala." Musaddik ya yi maganar yana kama hanyar tafiya.

Murmushi ta saki na jin daɗi, don ta yarda Musaddik masoyin tane tun da har yake son farin cikinta, juyawa ta yi ta nufi hanyar falon su, wayar ta ce ta yi ƙara alamar shigowar saƙo, dubawa ta yi taga wannan number ɗin ce dai da kullum sai ya turo da text kamar jaraba, da tana tunanin Musaddik ne, to amma yanzu ta fara tunanin kamar ba shi bane tun da shi kam yanzu suka rabu, ko buɗe text ɗin bata yi ba ta shige falon. Da sallama Mami ce zaune ita ɗaya da waya a hannunta da alama magana ta gama yi "Yawwa Ummin Mami kin dawo ko?" Mami ta tambaya.  "Eh Mami na dawo Musaddik ya fahimceni sosai mun yi rabuwar daɗi."  Ni'eema taba Mami amsa. "To Ma Sha Allah na yi farin ciki da hakan, yanzu dai tashi ki shiga kicin ki buɗe firij akwai wata jarka da nasata ciki jiya ki ɗauko mini ita, daga gefe kuma akwai wasu ƙananan robobi duk ki kawo Min su."  tashi Ni'eema ta yi don cika umurnin Mamin.

Duk ta kwaso tare da zubewa Mami a gaba ta ce "Mami gashi nan."  "Ummin Mami saurareni da kyau, duk waɗannan magungunan don ke na sayo domin haka daga yau zaki soma shan su har ranar da za'a yi ɗaurin auran."  turo baki Ni'eema ta yi ta ce "Allah Mami nifa dama baki sayo komai ba kawai ki bar kuɗinki."  Zaro ido Mami ta yi ta ce "Au mantawa na yi ai ban yi shawara dake ba ya yin siyowar, oya maza zo ki ɗauka ki fara sha tun kan raina ya ɓaci." Mami ta yi maganar fuska babu wasa. Kan dole Ni'eema ta soma shan maganin ba don ta so ba.

Kwanci tashi asarar mai rai haka yake don kuwa kwanakin auran Ni'eema da Abdul-Nasir sai ƙara matsowa yake domin sauran kwana biyar kacal, sai shirye-shiryen bikin suke ta yi, ɓangaren amarya da ango har yanzu babu wata magana da ta taɓa haɗasu, shi yana jin haushin irin yadda take nuna wa Musaddik so, ita kuma tana masa kallon mugu wanda ya shiga tsakanin ta da masoyin ta, ko a hanya suka haɗu ba wanda kewa juna magana.

Yau dai ya ƙudurci niyyar sai ya yi mata magana don ya lura yarinyar tana da girman kai, sai dai kuma zuciyar sa ganin duk abin da Ni'eema ke yi take yana matuƙar burgeta har ya kan kasa nutsuwa duk sanda bai yi tunanina taba.

Zaune yake saman kujerar dake ɓangarensa wayarsa yake latsawa, sai ga Sagir ya zo wajen yana faɗin "Yayanmu yau baka siyo mana ice-cream ba?" "Murmushi ya yi tare da gyara zama ya ce "Lah! Na manta ne fa, amma anjima zan fita na siyo maku, yanzu dai je ka kira mini Auntynku."  Da sauri Sagir ɗin ya nufi falon. Ni'eema ce da Mami, Ni'eema tana gyara ɗaurin ɗankwalin kanta, fitowar ta daga wanka kenan ta fito falo, Sagir ne ya shigo ya ce " Aunty Yayanmu ya ce ki je."  Zaro ido Ni'eema ta yi cikin tsoro, da kai kawai ta amsa, a tunanin ta Mami bata ji ba don haka sai ta yi kwanciyar ta akan kujera cikin ranta tana faɗin "Babu in da zan je salon ya kuma mini muguntan da ya saba."

Minti kusan goma kenan da aikowa, amma Mami ta ga Ni'eema bata da alamar tashi don haka sai ta ce"Ummin Mami bake na ji Sagir ya ce Yayanku yana kiranki ba? " Turo baki ta yi ta ce" Ni fa wallahi Mami ban son na je ya yi mini muguntan da yasa mini ne, ban da haka ina ruwan shi da ni." Gyadya kai kawai Mami ta yi ta ce "Eh lallai Ummin Mami mijin da zaki aura kike faɗi ma haka, to bari ki ji maza tashi ki ɗauko hijjab ɗinki tunkan raina ya ɓaci, wallahi matuƙar kika ce haka zaki dinga yi zamu sami matsala dake don ba haka kika ga ina yi ba tashi maza." Miƙewa Ni'eema ta yi tana ture turen baki ta je ta ɗauko hijjab ɗinta sannan ta fita.

Ɓangarensa ta nufa cikin tafiyar ta mai cike da nutsuwa da ɗaukar hankalin wanda ya gani, cikin siririyar muryan ta ta yi sallama. Da ƙyar ya amsa kamar wanda aka yi wa dole. "Ina wuni?" ta faɗa. Bai amsa mata ba sai ma wani harara da ya cilla mata ya ce "Kin ga ni fa ba dogon magana na kira ki yi mini ba don haka ki yi mini shiru, dama kiran ki na yi domin jin wane tanadi ki kawa auran da za a haɗa mu?"  Ya yi tambayar yana kallonta. Duƙar da kanta ƙasa ta yi wasu zafafan hawaye suka tsiyayo daga idonta, gabaɗaya maganar sa ɓata mata rai yake bama kamar yadda yake mata komai na isa isa.  A karo na biyu ya kuma mata tambayar, nan ma shiru taƙi amsa masa. Haka ya gaji da tambayarta ya yi shiru domin ya lura ba zata masa magana ba.

Wata uwar tsawa ya daka mata ya ce "Oya tashi ki ɓace mini da gani shashasha kawai."  Jikanta ne ya ɗauki rawa da sauri ta tashi ta bar wajen kamar yadda ya buƙata, a daidai ƙofar falo ta tsaya ta share fuskar ta gudun kar Mami ta yi mata faɗa.

************************************

Haka dai Ni'eema ta kasance cikin wannan yanayi har Allah ya sa rana ɗaurin Aure ya zo, AlhamduLillah an ɗaura aure lafiya cikin sadaki mafi daraja, Ni'eema da Abdul-Nasir sai dai cikin su babu wanda ke cikin farinciki,  har gara ma Abdul-Nasir don shi har wajen ɗaurin Auren ya halarta, amma Ni'eema ban da kuka babu abinda take yi, babu kamar lokacin da aka sanar mata an ɗaura.

Aunty Mama kam ita har kasa ɓoye baƙin cikin ta ta yi domin a ranar fushi take yi da kowa, hattana yan'uwanta da suka zo ba ta wani nuna jin daɗin zuwan na su ba, shi ya sa ana tashi daga ɗaura aure ta dannawa Abdul-Nasir kira ta waya. Bai ɓata lokaci ba ya isa bedroom ɗin nata inda ya samu daga ita sai Hajiya Lantana, a kasa ya zauna yana kuma gaida su"Lallai Abdul-Nasir da alama kana farin ciki da wannan Auren don naga har wani rawan kai kake yi, to bari ka ji na gaya maka yarinyar nan ko bayan ta tare karka yarda wani abu ya shiga tsakaninku na auratayya don ban shirya haɗa jini da shegiya ba." Dum haka Abdul ya ji maganar Aunty Mama har ga Allah bai taɓa tunanin jin haka daga gareta ba, ƙasa ya yi da kai ya ce "Amma Aunty Mama daga yau fa yarinyar nan ta na ƙarƙashin inuwar kulawata ne kuma ya zama dole na sauke duk wani haƙƙinta dake kaina, kamar yadda Shari'a ta tanadar."  Dogon salatin da Aunty Mama ta ja yasa shi yin shiru daga maganar shi "Lallai da kyau Abdul-Nasir wato ba zaka bi umarnina ba kenan ko shi kenan in dai wannan yarinyar ce da kanka zaka zo ka ba ni labari."
"Ikon Allah ashe shi ma Abdul haka yake ina masa kallon mutum kirki ashe abin ba haka ba ne." Hajiya Lantana ke maganar. Ke dai bari kawai Hajiya ai ni kam har na yi shiru da maganar ya yi duk yadda zai yi tunda dai Zainab kullum ita ke samun nasara a kaina. "







Mu je zuwa.

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now