BABI NA TAKWAS

3K 196 3
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

This page is dedicated To My sweet Daughter *BADEEYAT* '''(beauty Queen) thanks for supporting me, Allah Ya ƙara maki lafiya da kaifin brain ina jin daɗin novel ɗin 'YAN GIDAN HAYA kamar yadda kika fara lafiya Allah Ya baki ikon gamawa lafiya. I love you wujiga wujiga. 😘😘😘

Page *15~16*

Kallon juna suka yi fuskar sa ɗauke da murmushi, da sauri Ni'eema ta sadda kanta ƙasa, domin irin kallon da yake mata, muryar sa ta ji yana faɗin "Mami barka da war haka fatan kuna lafiya" "barka zuwa Musaddik kaine da yamman nan, sannu da zuwa." Zama ya yi a kan kujeran dake fuskantar Ni'eema sannan ya amsa da "Yawwa Mami."

Tashi Ni'ima ta yi ta nufi kicin, ta haɗowa Musaddik abin sha, cikin nutsuwa take tafiya tun da ta fito ya zuba mata ido yana kallonta, tambihi yakewa da irin kyakkyawar halittan da ya yi wa Ni'ima, muryarta ta dawo da shi daga dogon tunanin da ya shiga "Uncle Musaddik ga drinks nan" Ni'eema ta yi maganar cikin sanyin murya. Har tsakar kan shi sai da ya ji maganar, musamman yadda ta kirayi sunansa, sai ya ji duk duniya ta fi kowa iya faɗar sunan. Murmushi ya sakar mata ya ce "Na gode." sannan ya ɗauki kofi ya soma tsiyaya wa tare da kai wa bakin sa.

Ni'eema dai barin wajen ta yi ta koma bedroom ɗinta, saboda irin kallon da Musaddik ya ke yi mata, ba ƙaramin kashe mata jikinta yake yi ba. Da kallo ya bi bayanta har sai da ta shige bedroom. Ajiyar zuciya ya sauke tare da dawo da hankali kan Mami ya fara magana "Mami wai yau lafiyar ta ƙalau kuwa?" Cikin rashin fahimta Mami ta ce "Wa kenan?"Auntyn su Sagir nake nufi." A sanyaye ya yi maganar "Au wai Ni'eema kake nufi? ai yau da zazzaɓi ta wuni yanzu da yamman nan, gaf da zaka shigo ta samu sauƙi." Mami ta ba shi amsa. "Ayya Allah ya ƙara sauƙi." Cikin tausayawa ya yi maganar.

Amin Mami ta amsa, Musaddik ya miƙe tare da cewa "Mami bari na tafi dama leƙowa na yi na gaisar da ku." "aiko mun gode sosai da gaisuwa, Allah ya bada ladan ziyara, ka gaida Mommyn taku." Mami ta yi maganar fuska sake. "In Sha Allah za su ji." Ya yi maganar yana fita

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Alhaji Musa Abba shi ne mijin Mami, ɗan kasuwane yana da tarin dukiya, tare da matan Aure uku Hajiya Saude ita ce uwar gida wacce suke kira MAMA, ta haifi yara biyar maza uku mata biyu, Abdulhakim, Abudlrashid, Fatima, Maryam autarta Salmah. Duk 'ya'yan manya ne, domin su uku sun yi aure, yanzu daga Maryam sai Salmah suka rage basu yi Aure ba.

Sai ta tsakiya wato Hajiya Jamila wacce suke kira AUNTY MAMA, ita kuma yaran ta uku Abdul-Nasir, Hafsat sai Auta Suhaila. Aunty Mama kam har yanzu bata auras ba duk makaranta suke yi.

Sai Zainab wacce ta kasance Amarya. Wato Mamin Ni'eema ita ke da yara biyu Sagir da Nazir. Mama da Aunty Mama komai tare suke yi, kusa dai Aunty ita ke tsarawa Mama komai, sun haɗewa Mami kai sam basa sanyata cikin sabgar su. Allah ya yi Mami da haƙuri don haka bata taɓa damuwa da halin da suke nuna mata ba, domin ita dai da zuciya ɗaya take zaune da su.

Ni'eema da Suhaila duk a shekara ɗaya aka haifesu sai dai, Suhaila ta girme ta da watanni, sai Maryam ita kuwa ta girmesu Maryam da Suhaila ba su ƙaunar ganin Ni'eema a gidan, kullum cikin zagi da goranta mata su ke, ita kam Ni'eema ta kasance yarinya ce mai haƙuri da nutsuwa kullum Mami faɗa takebyi mata a kan duk abin da su Suhaila suka mata karta tankasu su ci darajar mahaifinsu kuma babu ruwan ta da su, sosai Ni'eema ta ɗauki nusihar Mamin ta.

wannan kenan.

********************************

Tun lokacin da ya shigo gidan ta gansa, ta tsaya jiran ganin ya nufi sasan su sai taga ya yi sashin su Ni'eema, sosai hankalin ta ya tashi har ta soma addu'a Allah Ya sa ba wajen Ni'eema ya je ba, domin har ga Allah ita kam sonsa take yi, firgigi ta dawo daga tunanin ta jin muryar sa yana faɗin "lafiya kuwa Suhaila?" Hmmm um sai da ta saki ajiyar zuciya sannan ta fara magana "Babu komai fa Yaya Musaddik." Ta ba shi amsa. "ok to ai da sauƙi naga sai magana nake yi maki na ji shiru." "babu komai." ta ba shi amsa. Gyaɗa kai kawai ya yi sannan ya buɗe motorsa ya bata wuta.

Da kallo ta ba shi na mamaki don lamarin Musaddik yana bata mamaki, rai bace ta koma sashin su inda Mahaifiyarta take nan ta je ta zauna, kallon ta Uwar ta yi tana faɗin  "Ke lafiyar ki kuwa Suhaila kika shigo mini nan cikin baƙin rai?" Ƙara turo baki Suhaila ta yi cikin shagwaba ta fara magana "Aunty wallahi Musaddik ne ya ɓata mini rai, tun ɗazun ina zaman jiransa ya fito shi ne yana fitowa bai ko saurareni ba ya ja motar sa ya yi gaba." Cikin sauri Aunty ta katse mata maganar da faɗin "Bangane ba? Yana fitowa ya yi gaba ba wa kenan kike nufi?" "Musaddik fa na ce maki." Suhaila ta yi maganar cikin ƙosawa. Musaddik da yaushe ya shigo gidan, kuma da yaushe ya fita? Domin bai shigo nan sashin ba?"

"Daga sashin Mamansu Sagir fa yake, wallahi Aunty ina tsoron kar yaya Musaddik ya ce yana son waccan banzar yarinyar mara asali, don ni kam na daɗe ina son Musaddik a raina." Suhaila ta yi maganar har da hawaye. Dariyar rainin hankali Aunty ta yi ta ce "Haba Suhaila ta ya Musaddik zai so wata Ni'eema? Kema kin san hakan ba zai yiwu ba, shi kansa ba zai fara ba saboda Momynsa bata ƙaunar haɗa jini da talaka ballantana kuma ita Ni'imar daba asali ke gareta ba, ki kwantar da hankalinki kamar kin auri Musaddik kin gama."

Wani farin ciki ya mamaye zuciyar Suhaila jin abin da Auntyn ta faɗa “Yawwa Auntyna haka nake son jin...”


Mu je zuwa...

NE'EEMA COMPLETEOnde histórias criam vida. Descubra agora