TALATIN DA BIYU

2.7K 166 2
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*






Page *61~62*

SUHAILA wacce ta koma kamar wata wacce hankalin ta ya ɗan gushe, saboda mugun mamakin da ya kamata ‘Babban mutum kamar *YMB Investment* wanda kaf Nigeria aka san da zamansa shi ne tsugune gaban Mami yana hawaye, to mene ne haɗin shi da Mami ɗin?’ Ta yi wa kanta tambayar da babu amsa.
  Ƙara ɗago da kai ta yi tare da kallon shi  ‘tabbas babu ƙarya shi ɗinne.’ Wani irin faɗuwar gaba ta ji lokacin da ta tsinkayi fuskar Ni'eema akan tasa "Inna Lillahi ko dai shi ne mahaifin Ni'eema?" Suhaila ta sake yin tambayar a ƙasan zuciyarta a karo na uku.

A fusace Mami ta watsa masa wani mummunar kallo ta ce "Don Allah Malam ka bar ni in sarara, a ina kasan ni ne? Idan ma ka sanni to ni ban sanka ba, ka wani zo ka sanya ni a gaba, na roƙeka don Allah ka kyele ni ƙar mijina ya zo ya ganka tare da ni ya yi tunanin da wani abu a tsakanin mu."

"Zan barki Zainab amma sai kin saurare ni da abin da nake tafe da shi, wallahi tallahi na yi nadama na san na aikata maki ba daidai ba, amma ina son ki yafe mini." Cikin hawaye yake maganar sam bai damu da jama'ar dake kallon su ba.

Banza Mami ta yi ma shi, tare da ɗauke kanta domin sarai tasan Yaseer ba zai taɓa barinta ba, kallon Suhaila ta yi ta ce wa Suhaila ta bata wayar ta zata kira Dady. Babu ɓata lokaci ta kira Dadyn ta sanar masa yadda ake ciki, a ruɗe ya baro ofis ɗin sa ya nufi asbitin.

Ko lokacin da ya iso asbitin Alhaji Yaseer bai matsa daga tsugune da yake ba, cikin mamaki Dady ya ƙarasa wajen yana tambayar ya jikin Ni'eemar. "Da sauƙi amma har yanzu bata farka ba tunda aka mata allurai." Mami ta ba shi amsa. "Allah Ya ƙara sauƙi."  Dady ya faɗa yana kallon Alhaji Yasser ɗin da mamaki. Cikin sauri ya miƙa masa hannu suka yi musabaha. Cike da mamaki ya ce " Alhaji dama kaine a nan?"  Jinjina kai Alhaji Yaseer ya yi ya ce "Dole ka ganni a nan Alhaji karka yi mamaki, roƙon Zainab nake ta yi  a bisa laifin dana yi mata amma taƙi sauraro na."

Kallon Mami ya yi wacce ta haɗa rai kamar zata fashe da kuka, tsabar mugun haushin Alhaji Yaseer ɗin take ji, duk da ta daɗe da yafe masa, amma ganin da ta yi masa yau komai ya dawo mata, tana wannan tunanin ne Dr ya ƙaraso yana sanar masu da farkawar Ni'eema, da sauri Suhaila ta shiga ɗakin, burinta kawai taga Ni'eema.

Mami ta take mata baya, nan suka bar Dady da Alhaji Yaseer ɗin suna tattaunawa, jinjina kai Dady ya yi ya ce "Gaskiya dai Alhaji sai dai in mun koma gida kaga yanzu hankalin mu ba a kwance ya ke ba.” Ya hannu tare da ciro kati ya ba shi, yana faɗin idan sun tashi zuwa sai ya neme shi ta number ɗin dake jikin katin, sosai Alhaji Yaseer ya yi murna domin ya tabbatar za su zauna da Zainab ya roƙeta gafara, Addu'ar sa ita ce Allah yasa ta haifi ɗan dake cikinta, da wannan tunanin suka yi sallama.

Wajen Ni'eema Mami ta nufa tana faɗin "Sannu Ummina ya jikin?" ɗan murmushi ta yi ta ce "Da ɗauki Mamina."  "Allah Ya ƙara sauƙi, me zaki ci?"  Girgiza kai ta yi ta ce "babu komai Mami na ƙoshi." Ni'eema taba Mami amsa. "Haba Ummina ki daure ko kaɗan ne ki ci zaki fi samun sauƙi." Cikin lallashi Mami ke maganar. "A'a Mami ko na ci amai zan yi ki bari kawai, har zuwa anjima."  lallashin ta suke ta yi ita da Suhailan, amma fir ta ce bata son cin komai.

Dr. Ne ya dubi Mami ya ce "Hajiya muna buƙatar fitsarinta, don mu gwada."  "To." Kawai Mami ta amsa. Da taimakon Mami ta isa toilet ɗin ta yo fitsarin, Mami ta miƙa ma Dr ɗin, sai da ya ɗibi jininta sannan ya fita.

********************************

Wani dogon ajiyar zuciya ya saki, tare da furta AlhamduLillah a fili, domin ba ƙaramin matsuwa ya yi ba a wannan tafiyar da ya yi ta sati biyu, tsabar kewar Ni'eema ya ke, fita ya yi daga motar tare da nufa ɓangarensa, a nufin sa baya son ya shiga cikin gidan har sai ya samu nutsuwa, yana buɗe ƙofa ya soma kiran layin Ni'eemar, amma abin mamaki har ta tsinke ba'a ɗaga ba, kira uku ya yi mata bata ɗaga ba, da sauri ya nufa ɓangaren Mami don ya duba ko lafiya.

A fili yaga su Nazir suna buga ball, da gudu suka kwasa sai jikin shi, suna faɗin "Sannu da zuwa Yayanmu."  Kawunan su ya shafa yana faɗin  "Mami tana ciki kuwa?" Har suna haɗa baki wajen cewa Mami tana asbiti.  "Asbiti ita dawa?" Ya tambaya cikin tashin hankali. "Aunty Ni'eema ce bata da lafiya... Ai bai ma bari sun gama faɗa ba ya juya da sauri, motarsa ya nufa cikin sauri don yasan asbitin da 'yan gidan suke zuwa.

A 360 ya isa asbitin, yana parking ya nufi shiga a ƙofar suka yi kicibus da Suhaila, da sauri ta tsuguna tana gaida shi, a gaggauce ya amsa yana tambayarta a wanne ɗaki Ni'eema take ciki. Tana faɗa masa ya wuce cikin sauri, sam bai kula da Mami a ɗakin ba don Dady dama ya fita, daret wajen gadon ya nufa tare da rungumarta, ganin haka ita ma Mami waje ta yi, ya ce "Ayya Baby ashe baki da lafiya shi ne baki sanar mini ba?" "Sannu da zuwa Yayanmu ashe dama kana tafe?" Ni'eema ta tambaya cikin ƙarfin hali. "Eh ashe da rabon zan ga halin da kike ciki shi yasa na zo, sorry mene ne yake damunki?" Ya yi tambayar hannunta na cikin na shi.  "Ni ma dai ban sani ba amai dai nake ta yi tun ɗazun, dama kuma duk sauran kwanakin ban jin daɗin jikina."  Sannu Allah ya kawo sauƙi baby."

Dr. Ne ya shigo ɗakin ganin Abdul-Nasir ɗin zaune, yasa shi miƙa masa hannu fuskar Dakta ɗauke da fara'a ya miƙawa Abdul-Nasir takarda tare da faɗin Congrat abokina matar ka tana ɗauke da juna biyu." Wani kyakkyawan murmushi Abdul ya saki tare da ƙara rumgumarta yana miƙa tsantsan godiyar sa ga Allah, da kyautar da Ubangiji Ya yi masa.

Ni'eema kam mamakin yadda kwata-kwata sau biyu Abdul-Nasir ya kwanta da ita amma har ciki ya shiga? Lallai ikon Allah yaifi gaban wasa.

Dr ya tsinka masu tunanin "Abokina ya na da kyau ake kula da ita musamman yarda da alama zata sha wahalar cikin nan, zuwa anjima in ruwan ya ƙare zan sallame ku." Cike da murna ya amsa da "Allah Ya kai mu."








Mu je zuwa.

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now