BABI NA BAKWAI

3.2K 185 1
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

Page *13~14*

Dedicated to ~MY SWEET SISTER~ *BILKISU BILYAMIN* '''Nagode kwarai da kaunar da kike nuna min, Allah ya bar zumunci, Ubangiji ya Albarkaci rayuwar ki'''  _har abada ana Tare_ 😘😘😘

*HAFSAT BELLO*🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ '''YASEEN BAKI MANA TYPING DA YAWA, KULLUM SAI KAINA YAYI CIWO DA TUNANIN MIJIN MUM DINMU'''

           *CI GABAN LABARI*

Hawaye masu zafi Ni'eema ke fitarwa na tausayin irin rayuwar da Mami ta yi, tun kan ta zo duniya mahaifinta ya ce baya sonta, duniya Maminta kaɗai ce mai sonta tun da ta iya jure wahalhalu ciki har da igiyar auranta don son  zuwanta duniya, hannu Mami tasa tare da share mata hawaye ta ce " Ya isa haka Ummina lokacin kuka ya wuce, yanzu  burina shi ne ganin Mahaifina in dai yana raye, don kullum addu'a nake matuƙar yana raye Allah ya bayyana shi."

Amin Mamina In Sha Allah zan tayaki addu'a  Allah ya bayyana shi, yawwa yar Albarka tashi maza jeki kwanta, dare ya yi nisa kuma please my daughter karki sa damuwar abin aranki, yanzu dai kin san matsayinki kina da uba, sai dai muddin bai bayyana kansa ba baki kusantar sa." To Mami Ni'eema ta amsa tana tafiya bedroom dinta.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Da misalin karfe takwas na dare, Zaune suke kan kujerun dining room kowa ka kalla spoon ne a hannun sa suna cin abinci, kallo daya zaka masu kasan duk uwa daya uba daya ta haifesu ta dalilin mugun kaman da suka yi, Alhaji Ahmad modibbo family kenan zaune da iyalansa suna cin abincin dare, shahararran mai kuɗine wanda idan aka yi ittikafi in bai zo na ɗaya ba a masu kuɗin Kaduna to kuwa zai zo na biyu, matarsa daya Hajiya Amina da 'ya'yanta huɗu don haihuwar bisa tsari suke yi, Musaddik shi ne babba sai mai bi masa Maryam, sai Saddik auta Hanifa, 'ya'yane yan gata wanda suka tashi cikin hutu da jin daɗi, sai dai duk da irin gatan da suke ciki sun sami kyakkyawan tarbiya.

Matsalar Hajiya Amina bata son, talaka ko kananun masu kudi, tafi mu'amala da masu kudin gaske ƙamar su, Addu'a take kullum kada Allah yasa Musaddik ya nemo 'yar talakawa, don ba zata taɓa yarda ta haɗa jini da talakaba(Allah sarki Talaka bawan Allah )

Musaddik ne zaune cikin ɗakin sa tare da zuba uban tagumi duk ta inda ya juya fuskar ta yake gani, yaune ganin farko daya mata amma gaba daya ta susutar masa da tunani, tsaki yaja ya ce cikin zuciyar sa "mai ke damunane haka abin da bantaba jiba yau shike shirin faruwa dani? To  kodai son Yarinyar nake yi? Nooo ya yi saurin bawa kansa amsa.”

Ganin yana shirin takurawa kansa da tunani, sai ya yi saurin tashi ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi, duk don rabuwa da tunanin Yarinyar can. Yana fitowa shafa yayi sannan ya hau kan lafiyayyan gadon sa wanda yaji shimfida na Alfarma (To Allah ya tashemu lafiya oga Musaddik, sai dai ina fatan ba yar talakawa kske tunani ba lol).

Abin mamaki da tunanin ta ya tashi bayan dumbin mafarkin da ya yi da ita cikin barcinsa, har mamakin yadda yarinyar ta samu wajen zama a zuciyar sa, ko tunata yayi wani farin ciki ke kamashi, Alla Alla yake yamma ta yi ya je don sake ganin beauty face din ta, ya san koda ya je da rana tana school shi yasa ya bari sai da yamman.

Ko a wajen break iyayen shi sun kula da yanayin farin cikin da yake ciki har Momy tana zolayar sa" wai ko dan Momy ka yi tsintuwane? " murmushi ya yi ya ce" Momy mai kika gani hala?" "No gani kawai na yi kana cikin farin ciki, kona sami sarkuwane?" Momy ta tambaya. Sosa kai ya fara tare da murmushi ya ce "Haba Momy babu komai fa."  Yana gama bata amsa, ya miƙewa don bai son Momy ta fahimci komai.

°^°^°^°^°^°^°^°^°^°^°^°^°^°^°^°^°^

Hankali tashe Mami kewa Ni'eema Sannu "Ummin Mami meya same ki haka?"  da ƙyar Ni'eema ke bude idonta wanda sukayi mata nauyi murya a dashe ta ce"Mami kaina ke min ciwo da zazzabi." Ni'eema taba Mami amsa "Subhanallah Sannu Ummina bari na kawo maki magani, kisha sai ki kwanta."  "to Momy."  Ni'eema ta amsa, ruwa Mami ta kawo mata da magani ta je kicin ta dauko mata abinci, zama Mami ta yi kusa da Ni'eema ta ce "yawwa Mamana fara cin abinci sai kisha magani."  Haka Ni'eema ta tashi tafara cin abincin duk da bakinta babu daɗi, kadan taci tace "Mami na koshi." mika mata maganin da ta balla ta yi ta ce "to sha maganin."  tana gama shan maganin min goma ta yi zaune sannan ta kwanta.

Mafarin ciwon Ni'eema, sanadin kukan da tasha a daren jiya ne na labarin da Mami ta bata. Bata farka ba sai bayan la'asar a lokacin kam Alhamdulillah ta samu sauki, wanka ta soma yi sannan ta rama sallolinta, ta shirya cikin doguwan rigarta baka mai kyau, wanda ya amshi jikinta sosai tayi kyau, Falo ta nufa inda Mami ke zaune tana duba wani littafin Addu'oi, murmushi ta saki ganin Ni'eema ta fito da alama taji sauki.

"Alhamdulillah Ummina ta ji sauki." Mami ta yi maganar tana aje littafin, wajen Mami ta isa ta ce " Mamina ina sonki sosai."  "Nima ina son Ummina."  Mami ta fadawa Ni'eeman. Ta bude baki zata yi magana suka ji sallama, dago kan da zata yi sai ko idon su ya haɗe da na juna...










Muje Zuwa..

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now