COMPLETE

4.5K 215 12
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*







Page *75~76*
🔚🔚🔚

Ba ƙaramin gudu ya sharara ba har Allah Ya kawo shi gida, ƙarfe bakwai na dare ya isa gidan,  AlhamduLillah tun da ya isa gida lafiya, a parking space ya faka motar, bai shiga cikin gidan ba sai da ya gabatar da sallar magriba, kai tsaye yana fitowa daga sallah Falon Aunty Mama ya shiga a burinsa ya soma tozali da a bar  ƙaunarsa Ni'eema, sallama ya yi Aunty Mama dake zaune tana duba wani littafi ta ɗaga kai tare da watsa masa harara, ko sallamarsa bata amsa ba, saboda tsabar takaicinsa da take ji. Jiki a sanyaye ya ƙarasa inda Aunty Mama take tare da zubewa a ƙasa, murya na rawa ya soma gaidata, hararan dai ta kuma banka masa ta miƙe zata bar falon.

Da sauri ya sa hannu tare da riƙo ta, har ƙwalla sun soma taruwa a idonsa, muryarsa a sanyaye ya ce

"Don Allah Aunty Mama ki yi haƙuri ni mai laifi ne a wajen ki amma ina neman yafiya."

Cikin hawaye yake maganar.

Aunty Mama dai shiru ta yi domin har ga Allah Abdul-Nasir ya gama cusa mata takaici.

"Ina roƙonki da Allah ki yi haƙuri wallahi fushin ki a gareni babban tashin hankali ne."

Hmmm Aunty Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce

"Abdul-Nasir ka ba ni mamaki fiye da tunanin ka, a ce ka tafi ka bar 'yar mutane a gida, ko ka damu da jin lafiyar ta ballantana na ɗanka ka je ka yi zamanka yanzu mai zaka ce min kuma? "

" Ki yi haƙuri na yi laifi kuma In Sha Allah ba zan kuma ba."

"Ni ba ka yi mini komai  ba matarka ka yi wa laifi don haka ita zaka nema tafiyarta."

"Kema na ɓata maki Aunty Mama ki yi haƙuri ba zan kumawa."

Tashi Aunty Mama ta yi ta bar falon don fa Abdul-Nasir ɗin ya kai ta maƙura, bayyi ƙasa a gwiwa ba ya bita har bedroom ɗin yana cigaba da mata magiya, sosai ya bata tausayi don taga alamar nadama a tattare da shi, don haka sai ta saki murmushi tace

"Na yafe maka Abdul-Nasir amma ka kiyaye gaba, domin Allah ya baka mata ta gari gata da nutsuwa da kunya, shawarar da zan baka shi ne ka kula da ita don a wannan zamanin kafin ka samu mai irin halayyar ta da wahala."

"In Sha Allah zan kula Aunty Mama, ku dai taya mu da Addu'a."

"Addu'a kam kullum yinta muke, Allah ya maka Albarka ya baka zuri'a ta gari."

"Ameen Aunty Mamana."

Hira suka shiga yi cikin jin daɗi Abdul-Nasir yana son tambayar Ni'eema amma yana kunyar Aunty Mama, daurewa ya yi ya ce

"Aunty Mama wai ina Suhaila?"

Tsaf Aunty Mama ta gane da biyu yake tambayar. Don haka sai ta ce

"Tana gidan Ni'eema tare suka tare, don a lokacin kai ka yi yaji."

Zaro ido Abdul ya yi cikin mamaki ya ce

"Aunty Mama Ni'eema ta tare ne a gidan? "

" Eh yau kwana huɗu kenan."

Shiru Abdul ya yi domin tabbas yasan ya aikata kuskure, saurin kawar da shirun ya yi ya ta hanyar soma ba Aunty Mama labarin wajen aikinsa da ƙarin matsayin da ya samu, fatan Alhairi Aunty Mama ta yi masa, sannan ta ce,

"Ya kamata fa ka tafi gida dare na yi fa."

"Eh! Yanzu zan tafi In Sha Allah."

Ya ƙarasa maganar yana tashi tsaye, dama ya ƙosa ya yi arba da Ni'eema da Fasmir, sallama yayi wa Aunty Mama yana barin falon, yana fita yasa masu aikin gidan suka kwashi tsarabar da ya kawo masu ya kai wa Aunty Maman.

आप प्रकाशित भागों के अंत तक पहुँच चुके हैं।

⏰ पिछला अद्यतन: Aug 12, 2023 ⏰

नए भागों की सूचना पाने के लिए इस कहानी को अपनी लाइब्रेरी में जोड़ें!

NE'EEMA COMPLETEजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें