TALATIN DA DAYA

2.9K 169 2
                                    

*NI'EEMA*

Written by *Zulaiha Rano*

~Alhamdu Lillah ina godiya gareku my fans na Addu'oi da kukayi min, an yi biki lafiya an kuma gama lafiya tuni amarya ta na gidanta, Allah Ya bar zumunci da kaunar juna~  _ni ce dai 'Yar Mutan Rano_

Deducated to '''All my fans I heart you '''

*59~60*

Cikin gidan suka nufa, Abdul na tsaye har sai da yaga sun shige sannan ya ja motarsa, a cikin gidan kuwa tun daga bakin get Ni'eema ke gaisawa da jama'a har suka dan gana da babban falon da suka gani cike da mutane, tsugunawa Ni'eema da Suhaila suka yi sun gaida jama'ar falon, can ta hango su Mami da Aunty Khadija suna hira, wata 'yar kyakkyawan yarinya zaune a jikin Mami, da sauri ta ƙarasa wajen tana faɗin "Auntyna barka da hutawa, Mami shi ne kuka tafi kuka barni?" Harara Mami ta watsa mata ta ce "kina barcin ne zamu tsaya jiranki?"  "Sorry Mami ai gamu mun iso Yayanmu ya aje mu, Mami wannan yarinyar fa?"

Shafa kan yarinyar Mami ta yi ta ce " Ilham ce 'yar gidan sister, jiya ba aje da ita ba."  Murmushi Ni'eema ta yi tare da ɗaukar yarinyar don sosai yarinyar ta yi mata kyau, Suhaila tana gefe sai kallon ko'ina na gidan take don sosai ya yi mata kyau, da tsari "Suhaila 'yar Aunty ina kika baro Auntyn?" Mami ta yi wa Suhaila tambaya. Ɗan murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, don sosai take kunyar Mami har ma da Ni'eema, ita yanzu dama don ta nunawa Ni'eema nadamar ta a fili yasa ta take shige mata, abinci aka kawo masu mai rai da lafiya, sai da sukaci suka ƙoshi. Har dare suna gidan don sun yi farin ciki da ganin yan'uwan su, Ni'eema kam Addu'a take Allah yasa ita ma mahaifinta ya bayyana.

*Bayan sati biyu*

NI'EEMA ce kwance a kan gadonta idonta a lumshe, fuskar ta ɗauke da murmushi yanzu ta gama waya da Yayansu, cikin farin ciki, Mami ce ta shigo bedroom ɗin hannunta ɗauke da plet ɗin abinci kusa da Ni'eema ta isa tana cewa" Wai Ummina lafiyar ki kuwa?" Ɗago da kai ta yi tare da kallon Mamin tana faɗin "lafiya lau nake Mami kawai dai kwana biyun nan kasala ke damuna." "Allah Ya kyauta ga abinci nan ki ci duk yau banga abin da kika ciba." Mami ta yi maganar tana miƙa mata plet ɗin abincin." Ƙamshin abinci ya daki hancin Ni'eema take zuciyarta ta soma tashi kayan cikinta suka soma yamutsawa wani irin amai ya taso mata, da sauri ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet ko kafin ta kai tuni Aman har ya fara kwarara.

Hankalin Mami a tashe ta nufi inda Ni'eemar take, tana faɗin “Sannu Ummina me ya sameki?" A ruɗe Mami ke maganar ganin yadda Ni'imar take kwarara aman, riƙeta ta yi har ta gama sannan ta ɗibo ruwa ta ba Ni'eema ta kuskure baki, sosai Ni'eema ta galabaita domin sai mayar da numfashi take yi, da taimakon Mami ta isa kan gado ta kwanta Mami ta cigaba da gyara wajen.

NI'EEMA dai sai mayar da numfashi take, nan da nan wani zazzafan zazzaɓi ya rufeta, haƙoranta sai haɗuwa suke, tsaf Mami ta kammala gyara wajen "Ummina sannu kin ji ina ya yi maki ciwo?"  Da ƙyar ta iya girgiza kai, alamar ba ko'ina. "bari na kawo maki tea sai kisha tun da duk abin da ke cikin naki ya fita." Mami ta yi maganar tana miƙewa. Lumshe ido kawai Ni'eema ta yi don yadda take jin jikin ta, Mami ta gama haɗa tea ɗin kenan Suhaila ta yi sallama. Bayan Mami ta amsa mata sallamar ta miƙa mata cup ɗin tea ɗin ta ce ta kai wa Ni'eema. Amsa ta yi sannan ta nufi bedroom ɗin can kan gado ta hango Ni'eemar da sauri ta ƙarasa wajen, ɗan zaro ido ta yi baki na rawa tace "lafiya kuwa?"  da ƙyar Ni'eema ta iya bata amsa "Ayya sorry Allah Ya ƙara sauƙi ga tea in ji Mami." amsa Ni'eema ta yi ta soma sha, ko kwatan cup ɗin bata yi ba, wani aman ya kuma taso mata, ta soma kwarara shi, da gudu Suhaila ta je ta kira Mami, a wannan karon hankalin Mami ya fi tashi don lokaci ɗaya Ni'eema ta zabgeta faɗa.

"Maman Sagir kodai asbiti zamu je kalli fa yadda lokaci ɗaya yadda ta koma?" Suhaila ta yi maganar kamar zata yi kuka. "Ni ma tunanin haka nake yi domin bata taɓa irin wannan ciwon ba." Je ki yi wa direba magana bari na fito da ita." Suna isa asbitin cikin gaggawa aka amsheta a Emergency room aka sanyata, drip aka jona mata, don ganin yadda ta fita hayyacinta.

Mami sai kai-wa take yi tana dawowa sam  hankalinta yaƙi kwanciya, Dr Faruk ne ke bata baki, wanda ya fito daga ɗakin da Ni'eemar take "ki kwantar da hankalinki Hajiya In Sha Allah da sauki mun yi nasaran tsayar da aman sai ta farka sai mu yi mata test don sanin wani ciwon ke damunta. gyaɗa kai Mami ta yi don ba zata iya magana ba, tunda ba sanin me yake damun Ni'eemar ta yi ba, kallon Suhaila Mami ta yi wacce ta haɗa kai da gwiwa tana sharan kwalla "Daina kuka Suhaila yi mata Addu'a shi ne mafita."  Zan je gida na manta ban ɗauko waya ba, gashi ban sanar da Abban ku ba." Mami ta yi maganar tana kama hanya.

Tana cikin tafiya sai ta ji ta yi karo da mutum, a razane ta ɗago da kai don bawa wanda ta buge haƙuri, sai idonsu ya haɗu da na shi wani razana Mami ta yi tare da ja baya, wata uwar harara ta maka masa, ta yi saurin komawa inda ta fito. Shi ma wanda ta buge ɗin da mugun mamaki yake bin ta da Kallo, har abada ba zai manta wannan fuskar ba, duk da ya daɗe bai ganta ba, ganin inda ta nufa shi ma da sauri ya bi bayanta, yana faɗin " Zainab!Zainab!! Zainab!!!."  jin yana kiran sunanta yasa ta ƙara sauri, a wajen Suhaila ta yi birki "Mami baki tafi ba ne?" Suhaila ta tambaya.

Ganin wani babban mutum ta yi ya gurfana gaban Mami fuskar sa ɗauke da hawaye yana faɗin "Don Allah Zainab ki saurareni ki ji tausayina."  Cikin kuka yake maganar. Mami banza ta yi mashi kamar bata san yana yi ba." Gabadaya hankalin jama'ar asbitin kallon su suka dawo da shi kan su Mami, suna mamakin yadda mutum mai daraja a idon mutane kamar wannan amma shi ke tsugune gaban wata...


Ni ma dai 'Yar Mutan Rano sai da na yi mamakin wannan abu.

Mu je zuwa.

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now