100 FINAL (THE END)

18.6K 403 41
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Dedicated to
Hauwa A usman
Jiddarh

Page 120

End


Hankalin ummi kusan
yafi na kowa tashi ganin yadda aka shige da zeenat dinta cikin dakin tiyata ko motsi kirki batayi .
gabadaya takasa zaune takasa tsaye.
Sai aikin zariya take tana Kai kawo a farfajiyar hospital din.
yayinda hawayen idanunta ke sake gudana bisa kuncinta  .
ahankali ta karasa inda deeni ke tsaye jingine da kansa abango yana kukan Zuci dana zahiri.
ta kai hannuta ta dafa kafadarsa tana runtse idanunta domin son sanin abinda zata furta masa, wanda zai dawo masa da natsuwarsa tare da kwantar masa da hankali.
muryarta cike da rudanin kuka ta soma mgn kayi hakuri deeni..
kayi hakuri kayi mata addu'a....
ahalin yanzu babu abinda zeenat tafi bakuta daga garemu facce addu'armu ..
addua itace kawai mafuta  garemu bakidaya, Allah yasa ayi aikin nan cikin sa'a  ta rabu da cikin jikinta lfy... .

ya Juyo ahankali yana fuskantar ummi da idanunshi da suka gama birkicewa zuwa wani launin na daban.
Ummi tayi masa xuru da idanunta tana kallonsa da jimamin halin damuwar da tilon Danta ke ciki.
wannan shine Karo na sau ba adadi datake ganin "yaronta " mafi soyuwa gareta cikin taskon rayuwa me tattare da rudani.
Shr kawai yayi yanacigaba da kallon umminsa gabadaya duniyar yaji tana jujjuyawa dashi  yayinda bakinsa keson yin mgn  Amman ya Kasa furta daidai da  kallama daya . domin ko yace zai Yi mgnr bazata fito ba .
Dan haka ya cire hanky ya shiga goge hawayen idanunsa da gumin dake tsatsafo masa.
kana  Suka cigaba da kallon kallon da adduar samun nasara acikin zukatansu .
Suna nan tsaye tsawon minti 30 sai ga wata doctor to fito daga   lab zatashiga dakin tiyarta da sauri  deeni ya bita abaya yana tmbyrta halin daake ciki Amman babu wata gamsashiyar bayyani daya samu daga gareta.
sai ma dakatar dashi datayi dacewar yallabai kayi hakuri kajira mu a waje.
yace madam please kiyi min hakuri nima ina son  naga halin da Matata take ciki Amman ina taki sauraronsa .
dole tasa ya juya ya koma gurin ummi suka cigaba da  tsayuwa ta sake fitowa ta wuce su tashige wani office tashin hankali kam bazan iya misaltamuku irin wanda deeni da ummi suke ciki ba sai dai addua.

hankalunsa ya kai karshen tashi.
shr ba'a fito da zeenat ba, hk ma likitoci .har likacin sallah ta gabato ummi tace WA
deeni yaje yayi sallah yayi mata addua kawai hk ya  tafi yin sallah jikinsa a matukar raunane.
yayinda yan'uwa kowa sai addua akeyi..

Adakin tiyata kuwa gabadaya likitoci tsaye suke akan zeenat kowanensu da kayan aiki sanye ajikinsu da handglof a duka hannayensu byn Sunyi scaning sun tabbatar da ko ya'ya nawane a cikin cikinta .
sannnan suka fara Yi mata allura take hankalinta yakarasa gushewa Duniya da abinda ke cikinta suka jujjuyawa daita, kana suka soma aikinsu cikin kwarewa da iyawa tare da adduar samun nasara koina Shiru bakajin motsin kowa cikin cikin dakin sai motsin sizos kawai da motsin mutun biyu din dake  kan aiki.
suma bawai mgn sukeyi ba  sai dai suyi nuni ga abinda za'a miko musu Lokacin da aka tsagata aka soma ciro yaro daya namiji kosashshen km lafiyayye yana motsi aka yanke cibinsa aka mikawa wani mutun dake tsaye gefe guda aka sake fito da wani shima namiji ne aka yanke cibi aka mikawa still mutumin dazu ganin za'a km ciro wani yasa sauran mutane suka soma kiran allahu Akbar ....babu kaukautawa aka mika masa sai dai ita wannna macece sai ta karshe baby  still Macece itama take dakin ya dauki kabbara allahu Akbar...Allahhu Akbar kana aka fita da yaran dan gyarasu ummi da deeni sunyi matukar murna har sun sanarwa dagin .
suma sunyi murna da farinciki da saukar zeenat lfy an shirya yaran tsab ana murna ganinsu a hospital din.
shi kuwa deeni kwata kwata bata yaran yake ba zeenat dinsa yake son gani .
hk ma ummi doctors Suka ce karsu damu su kwantar da hankalinsu ana kimtsata tukun km har yanzu allura bata Saketa ba sai nan da  wasu  yan awanni .

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now