6

11.9K 461 4
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 11-12

Washegari bai tashi da wuri ba sai wajejen shabiyu na safe yatashi. yashiga, bathroom byn ya fito ne yayi tsaye gaban mirrow yana kallon every part of him ,tsawon lokacin yana tsaye yana kallon kansa ta mirrow kafin daga baya ya janyo wata karamar   stood dake gefe  ya zauna .
hannushi ya dora a saman fadaden kirjinsa yana shafa kwantaccen gashin kirjinsa  hade da lumshe idanunsa "shi kansa yasan duk matar data mallakesa  matsayin mijinta bakaramin Lucky Tayi ba .

cikin sanyi jiki tamkar macce yasoma    shafe jikinsa da body lotion "  DEENi na kashewa kanshi kudi fiyye da tunanin may karatu ,
mikewa yayi cikin tafiyarsa ta kasaita ya nufi cikin bedroom din shi dan saka kayan " har  ya nufi kofar dazata kaishi parlour" sai ya tuna ana jiransa dan haka yaja  tsaki  mtssss sannan ya nufe kofar bedroom dinshi  byn yashige tare da cewa koma waye zai tafi idan yagaji da zama dan yanzu baida lokacin kowa  .

Shiryawa yayi cikin wasu hadadun kananan kaya wando blue jeans da  riga longslive" wani irin kyau Allah yayi masa na daukar hankali"  ya isa kan durowa ya kwashi wayoyinsa ya zuba cikin aljihun wandonsa "ya sanya takalmansa mai sawun ciki  ya zura hannushi daya  cikin dayan aljihun .

Shemah ce zaune  a parlour DEENi  take  zaman jiransa "wacce     tun karfe  tara na safiyar ranar   ta dako samamko son ganin DEENI din.

  da farko bedroom din ummi ta nufa , sanin datayi dole zai shigo gurin ummi ,ganin har ummi tagama abinda take  tadawo main  parlour dinta yasa itama tabiyo bayanta , .
Ganin tagaji da zama   kusan 1 hour tana  zaune  zaman jiransa  Amman bata ga alamun. fitowarsa ba  yasa tacewa ummi dan Allah takira mata shi .

Ummi takirasa  tasanar dashi bai ce  da ummi  komai ba dan kusan  da haushi yatashi . Ita Kuma ganin yayi shr yasa tace mata taje part dinsa .

Koda ya yafito falonsa yaga mutun zaune shi duk tunaninsa FK ne ko cikin abokan aikinsa kallo daya Yayi mata ya dauke idanunsa daga kanta "yi yayi tamkar bai ganta  ya nufi hanyar fita. ta taso da sauri tana kiran sunanshi " cigaba yayi da tafiyarsa danshi a ganinsa bai ga abinda zai sa ya tsaya ba ,.
ganin saurin bazai mata ba , dan  haka ta kara da dan  gudu da sassarfa har ta cimmasa  ,a  daidai cona da zata kai mutun main parlour din gidan tasha gabansa da sauri  tana sauke ajiyar zuciya hade da cewa dan Allah yaya katsaya magana nake son yi dakai .
dubanta yayi tamkar bazaiyi magana  sai Kuma yace  meyye matsalarki dani ? Dan ji Yayi kmr ya dauketa da maruka " Kalmar daya fada ne yasa taji zuciyarta ta tsinke "  Tayi wani irin tsalle kmr zata tafasa kirjinta ,.
Tayi shiru tana tattaro kalmar dazatayi amfani  wajen fahimtar dashi abinda ke ranta .
  cikin sanyi murya yace ina zaton kin manta ko ni wanene shiyasa kika tareni , sai da  ta saita kanta sosai, ta'aro jarumta takara akan wanda take da"  sannan tasamu kwarin gwiwa. cikin marairaicewa murya irin ta masu neman taimako tace dan Allah yaya" kadan bani aron  lokacin uziri ne dani.
yamata wani irin duban dayasa yanhanji cikinta kadawa sannan yace uhmm ina jinki kuma ki tabbatar da uzirinnaki mai ma'ana ne .
"da idanunta ta amsa masa dan gabadaya  ilahirin jikinta  kirma yake tsabar rudewa datayi har wani gumi take fitarwa na wahala.
tun ba yau  ba DEENi  yasan shemah nason furta wani abu gareshi Amman rashin ganin fuskarsa yasa taki tunkarsa shi bema san dalilinsa na tsayawa ba  .
Shi kansa yasan  dole wannan ranar zata zo komai daren dadewa  ".

ahankali take sauke ajiyar zuciya saboda fargaban da tashin hankali , abinda  zai biyo baya " numfashi taja hade dayin   kasa da kanta dan sam bazata iya kallon kwayar idanunshi a wannan lokacin .
Ahankali    tasoma magana muryata  kasa kasa  cikin in...inna ,tace  daman ..daman..ina son sanar dakai   " ina..ina so.....da hannushi ya dakatar  daita" tun bata kai ga karasa maganarta ba  tare da buga mata wata irin razananniyar  tsawa  wanda yasa ba shemah ba ,har zeenat dake kokarin  fitowa daga dakin ummi zuwa parlour "ta   koma cikin daki da sauri " ta manne da jikin kofar  hade da cewa wayyo... Allahna me Kuma yasame sa  haka cikin tashin hankali ta sake mannewa da jikin kofar .   , hatta ummi dake zaune a falo  say da taji amon muryasa  ,wani irin kallo yake jifarta dashi   yace kina.... me uhmm repeat what u say   ,  lip's dinshi  cikin bakinsa yana cizawa sannna yace  what ar u try to  say ,ya sake jiho mata wata  tambaya, still shr kake jin shemah  ba bakin magana Amman gabadaya ilahirin jikinta ya dauki kirma .
Cikin isa da takama yace u better keep what'ever you won't say before I sikater you now  jikin  shemah yacigaba   rawa kafafuwanta suka Gaza daukarta dana sani kuwa tayishi yafi cikin buhu ,  ya tsareta da mayatattun idanunsa " murya a kwasashe yace     na sake jin kin Kuma furtamin  wannan bazar kalmar wlh azim  zakiga yadda zanyi da namanki stupid girl kawai.
ya ja tsaki  ya wuce abinsa ta tsaya nan tana bin bayansa da kallo  ranta a bace  batasan lokacin da Hawaye yasoma zubo mata   tana tunanin yaushe ne zata daina kuka akan son DEENi mutumin da take matukar so tamkar ranta  mutumin da mata ke rububin son shi  mutumin dayake jama mata aji ga shegen kyau da kwarjini " nan ta zube kasa  ta risgar kuka  ahankali hade da sa hunnta duka ta toshe bakinta dasu .

Zeenat dake tsaye jikin byn kofar  dakin ,banda kirma  bbu abinda jikinta keyi , tsabar frigice jin abinda shemah ke kokarin yi' domin taji  duk abinda ya faru tsakanin yaya DEENi da shemah tsabar  tsoro ne ya hanata fitowa ,wani irin kishi ne taji yana taso mata tun daga kan tsintsiyar kafarta  yana bin ilahirin jikinta hade da kashe mata duk wani  gabobin dake jikinta ,  taji a ranta  da tana iya fitowa,. tabbas  da ita kadai tasan  yadda zatayi da shemah, tsinuwa kuwa iri iri  bbu wanda zeenat bata aikawa shemah ba .

, ahankali zeenat ta sulale   kasa ta dora hannuwanta duka bisa kanta.cikin kuka take cewa  Shikenan ummi tacuce ni  zata kai ni  tabaro "gashi taki yarda da aurena ,da yaya DEENi ga wasu can suna neman   farautarsa .
,ba tasan tana shirin jefa diyarta cikin halaka bane akan tilon danta.
  dan ita yanzu ji take zata iya yin komai akan DEENI  .
Ahankali  Tace ita yanzu yazatayi da ranta , idan Kuma  yace hakura daita fa ?  Taji gabanta fadi
Da sauri tasoma girgiza kanta tace hakan ma  bazai taba faruwa  ba inshallahu sai ta aure yaya DEENi  mijinta ne ita kadai , .
dan ita yanzu wani irin son DEENi din ne yashigeta na  farat daya ,kmr kar taji ya furta yana sonta ...itama  taji tana maseefar kaunarsa ,  Ita taji ta Gani zata iya rayuwa dashi  akowani irin  hali.
kawai,a hankali ta sake  ta saki  wani irin  marayar kuka mai ban tausayi  tana furta ummi karkimin haka dan Allah  ..kar min haka ummi ke uwace gareni har da rabi .
dan Allah karki rabani yaya DEENi  wlh zan iya zama dashi a haka , duk munin halinsa ina son shi  " tunda harshi  ne ya furta yana sona ...
gabadaya  ta rikece da wani sabon  kuka tana sambatu .
kuka tayi sosai har da shesheka ahankali ta sauko da hannuta bisa kirjinta" ta dafe kirjinta dataji yana mata  wani irin ciwo zuciyarta na  dokowa da sauri da sauri  zeenat ta runtse idanunta dan ita kadai tasan yadda take ji.....

  ta ciki  dakin zeenat ke rizgar  nata kukan ,yayinda shemah da ke  waje durkushe ta nata   .

Taku yake cikin izza da jin kai da jin shi wani ne yake takunsa har yakaraso ya zauna kujerar da umminsa ke zaune ya dora kansa kan cinyarta "ita Kuma ta'ajiye jaridar dake hannuta tun  soma jin amon muryasa ta daina karatu  datake "ya sakar mata murmushi  gafen baki tamkar bbu abinda ke damunsa ,yace gud morning my first lov ....
ta daura hannuta bisa sumar kansa tare da fadin morning my son yakatashi lfy , ya dan tabe baki sannan yace nut bad  ....
tace ya'akayi ne son  me kakeson cine akwai dinshi iri iri akan darning wanda   orready zeenat tashirya komai  .
turo baki yayi cike shagwaba har zaiyi magana " kome ya tuna sai Kuma ya fasa cewa komai " ummi ta tsurawa fusharshi idanu tace kayi shr ya lumshe idanunsa  muje kayi breakfast din ina lura da kai tunda kasoma zancen yarinyar nan bakason zama  ma a gidan  ballanantana Kaci abinci  ahankali ya ware idanunshi akan umminsa sannan yace first lov  na koshi fita ma zanyi yanzu ....

MMN SUDAIS CE

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now