💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA .A .BAGUDO
Page 63
Byn ta idar da sallah ne ta Mike 'ahankali jikinta a tsanyaye takarasa jikin window dakinta .
" ta makale hade da dan zuge labule window kadan ,ta yadda zata ji dadin hango abinda ke wakana a compound din estate din.Tana nan tsaye tana kallon yadda motocin ke shige da fice a cikin estate din , ta zurawa waje Ido sosai kmr mai shirin hango wani abu na daban aciki estate din, yayinda take shakar wata iska ta musamman mai dadi da ratsa jiki.
wanda rabonta da jin irin haka ta dade , tun kafin shigowarta cikin gidan.,har wani lumshe shanyayun idanunta take sakamakon farinciki data tsinci kainta ciki.
,Ta dauki tsawon lokacin makalle agurin tana shan iska "karar bude kofar dakin data ji anyi ne.
Yasa ta dan juyo da sauri hade da sakin labulen window.ahankali nablah ta sauke idanunta fess. akan Zeenat dake tsaye kikam.. tana mazurai . take gaban nablah Yashiga faduwa da sauri a yatsine Zeenat ke watsawa nablah wani irin mugun kallon wanda ke hautsina kayan cikinta , ganin irin kallon rashin arzikin da Zeenat ke binta dashi ne . yasa nablah shan jinin jikinta.
tabe baki Zeenat tayi sannan tace Yar iskar baiwa... kawai abinda yakawo kennan , kin wani zo kin nemi waje a daki kin zauna kina tamkar boka dan tsabar munafurci , to kike so yayi miki sauran aiki da yayi saura uhm ?
Nablah tayi saurin girgiza kanta tare da cewa dan Allah aunty kiyi hakuri wlh na dauka ko mungama aikin ne.
Zeenat , ta sake watsamata wata uwar hararar hade da kallon banza.. wanda hakan ya suka sake frigita zuciyar nabla dake tsaye Amman ta dake batare da tabari Zeenat din ta gane yanayin data ciki ba .
Mtsssssss Zeenat taja tsaki tare da cewa dan Allah malam ni fito ki kije ki karasawa mutane aiki sannan km ki daura min abinci ,Yar isakar baiwa... nablah tayi shr tare da dago shanyayun idanunta tana kallon Zeenat dasu ,yayinda take jin zuciyarta tamkar zata kama da wuta tsabar takaicin sunan da Zeenat din kirata dashi .
Zeenat tace
Kin wani tsareni da idanunwa narai narai kina kallona ko baza kiyi bane ?
a tsanake batare da wata alamun tsoro ko fargaba ba nablah tace zanyi ..
Ok minti biyu kacal nabaki "naganki a kitchen "idan kika kuskura kika bata min lokaci zakiga yadda zan ci ubanki a gidan nan " tana gama fadar haka
ta juya fuuuuuu tasoma tafiya tana kunfar baki."Nablah tayi zuru kawai tare da bin bayan Zeenat da wani irin kallon mamaki da alajabi abinda tayi mata.
dan ko kusa batayi tsammani zata fuskanci irin wannan babbar wulakancin ba mai cike da al,mara .
Yau itace aka aiki tajawo aka zagin mahaifinta..abanza uban ta fa aka zaga ,ta furta akan akasan ranta, wato silar ainkinta ne jawo a dinga wulakanta mata uba Haka km ma har da kiranta da sunan baiwa...baiwa fa takirani dashi ta sake maimaita sunan a filli gabadaya abin yazo mata wani iri km abazata" tamkar ba gaske ba.
Anya kuwa rayuwar zata yuwu a Haka tun ba,aje koina ba an fara da zagar mata mahaifnta.
" Anya kuwa zan iya daukar wannan kalar kaskancin da iskanci kuwa ,abinda ta tmbyi kanta da kanta Keenan?,'ahankali ta furzar da iska ta bakinta tana furta wlh da sake Dan zan iya daukar komai na kunci rayuwa Amman Banda zagar min iyaye .
,
, Mtssss taja tsaki itama tana harara kofar da Zeenat tabi .cikin sanyi jiki ta nufi kitchen .
Ko minti biyu batayi da daura ruwan abincin dare ba Zeenat takaraso ta tsaya a bakin kitchen din tana kiran.. ke....ke.. nablah dake tsaye tana jin Tayi banza daita duk da tasan daita take sannan km taki juyowa ...
Sai ma cigaba da aikinta Tayi.
YOU ARE READING
AUREN SIRRI COMPLETE
Mystery / ThrillerMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan