1

50.4K 1.3K 36
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
       💖💖💖
💗💗💗💗💗

  Bismillahirahmanurrahim

Aysha A bagudo

Page 1-2

Lekki  Unguwace  mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta   ,a silent place, saboda bata cika   hayaniya mutane ba  , dauke da tarin sanyin ni'ima mai dadi  sakamakon kusancinsu da ruwan teku" unguwace da tattara kan manya ma'aikata da kusoshin gwanati, hade da manyan masu kudi ,ga tarin  yan yahoo boy'z  domin mafi yawancisu   sunfi sha'awar  zama acikinta. rayuwar mutane  unguwar abin sha'awa  bbu ruwan wani da wani  domin suna rayuwasu ne tamkar a kasar waje   .

PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE

Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta , hadin kai tattare da zaman lfy,  Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ,ga tsantsar fahimtar juna dake tsakanin wannan family. kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu .

Let alh Muhammed bello khaliyal ,haifafen garin Lagos ne ,Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dake jahar kebbi. sananne  mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance. sannan kuma take zaman lfy, marigayi Muhammed bello  soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan .
ya rike mukamai da dama a wancan lokacin. ya rasu yabar tarin dukiya da da ya'ya da jikoki  bila adade.
    gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki  domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu  .

kafin rasuwarsa    dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da en'uwan , dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafin daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din  mai mazan kanta.
ya tattara  kan yan'uwasa suna zaune a ciki ,yana da mata hudu  hjy  shema'u  wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da ya'ya  goma   Sha biyu, mata takwas maza hudu  sai hjy  hauwa mai dauke da ya'ya goma maza biyar mata biyar ,sai hajiya rabi mai ya'ya takwas maza biyar mata uku   sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy  shuwa  itama tana   da yaya takwas mata bakwai namiji daya .
bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama . an ginashine  saboda  taron sada zumunci , wanda zasu dinga yi a duk karshen wata  .

haka suka taso har zuwa girmansu cike da son junansu .
anan cikin  dangi mazan suka zabi matan suma  matan suka zaba akayi  bikinsu anan cikin estate din suka zauna  tare da iyalinsu  har zuwa  sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire.
yayinda ya'yansa da ya'yan en uwa suka cigaba da kula da estate din .
  a lokacin  aliyu  da  habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda  karatu .

Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu  ya dukufa  gurin juya dukiyarsa ,ba abinda  yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya,  yayiwa sauran yan'uwansa zarra  aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. hade da tarin compenis  a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da  gidaje a abuja da sauran garuruwa .
tsananin neman kudinsa ne yasa  bai ajiye iyali da wuri ba ,burinsa bai wuce  ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba .

Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila  a india tun daga lokacin da aliyu ya daura  idanunshi akanta "ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi . fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne , ahmed  ne babba sai ita sai farida ,  kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata. sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince  da auren .
koda yazo daita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba .
kasancewarta mace mai tsananin  son jama'a da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da  mahamud ya'ya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar ya'yan data haifa  acikinta .
suma  kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke   kiranta da ummi ,duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa  hakan ne yasa ta sake janyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu.

AUREN SIRRI COMPLETE On viuen les histories. Descobreix ara