💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 9-10
Zeenat kwance a bedroom din ummi hannuta rike da wani English novel face to face tayi zurfi cikin karatun novel din saboda yadda take enjoy din novel din ya .
Yaya DEENI ne yashigo gaishe da ummi kafin yafita aiki ,byn sun gaisa ne ummi tace har ka shirya fita kennan ? Yace mata eh sannan yaja ya tsaya yayi shr ya zubawa ummi idanunshi .
ummi ta dubeshi tace da magana ne ? Tunda tarigada tasan muddin yayi shr irin haka to da magana a bakinsa.koda yake tasan dai zance nasa bai wuce maganar zeenat bane " Kuma daman tana son zeenat din tajima kunneta idan ta amince ruwanta "
dan haka ummi kalleshi da kyau tana nazarinsa ta numfasa sannan tace masa kayi shr alhalin nasan da magana abakinka .
, muryasa a shagwabe yace first lov kan dai maganar zeenat ne ,dan Allah first lov, ba yabon kai ba "ina da qualities din da za'a bani auren kowace irin mata nake so" Kuma ko Yar gidan waye ,.
Yar taki ma daba wani kyau ne daita ba" dan ma zan taimaka mata "ya fadi haka fuskarsa a hade ,.ummi tace duk da haka day bazan bada diyata ba kaje waje ka gwada sa'a r ka" wai ma in tambayeka DEENi yamaida hankalinsa sosai ga umminsa" tace kai da kake ta damun kanka da zance nan kullum. kasamu ita yarinya da maganar ,kun daidaita kanku ne ?
DEENI yace uhmm kece dai zaki sanar mata, ummi ta nuna kanta da dan yatsanta, nice ma zan tayaka yakin nemar maka soyayyarta" lallai ma bason auren nata kakeyi ba" kashare zance kawai tunda baka shiriya neman aure ba. yace to ni first lov in na fada sai naga tamkar Raina ne zatayi, ummi tace kunji girman kan ba a hassale ummi tace dan Allah kayi hakuri kabar zance nan. haba duk kabi katadda hankalinka da nawa. yarda ne dai bazanyi .
dan haka kayi hakuri kabar zancen nan kwata kwata dan ba yarda zanyi ba .DEENI daya gaji dayiwa ummi magiya ya hakura ya ficewarsa ,yana jin takaici kansa, tunda daga lokacin da zeenat taji DEENi ya ambaci sunanta ta mike zubur zaune daga kwanciyar datayi, hankalinta a tashe jikinta har rawa yake tsabar rudewa" ita zeenat din yaya DEENi yake nufi ko wata daban.
ahankali ta furta in ko ita yake nufi dakuwa ta more a rayuwarta, dan gaskiya yaya DEENi ba irin namijin da mace zatace bataso bane , ahankali ta sake furta A'a dan Allah ummi kada kimin bakinciki mana.tana jin fitarsa ta fito da sauri daga dakin tana kallon ummi dake zaune tana jan carbi, zatonta ko ummi zata mata maganar ne. Amman sai taga sabanin haka .
dan kuwa ummi ko kallon inda zeena take tsaye batayi ba.
dan tarigada tasan taji komai" to Kuma bayanin me zata tsaya yi mata. Ta dai yi shr ne taga yadda zata dauki lamarin .
Can kuma, ummi ta dago tana duban zeenat din tana nazarinta" yayinda zeenat din itama ummi take kallo" har zuwa lokacin ummi batace komai ba .
sai ma kau da kanta gefe datayi , ganin ummi bada niyyar ce mata komai ,yasa zeenat kira sunan ummi" ta juyo tana duban zeenat din da kyau".
ahankali cikin sanyi murya tace ummi wai wata zeenat din yaya DEENi keso ?
Ummi ta dan tabe baki sannan tace dan Allah rabu dashi wai ke yake nufi "da sauri zeenat tasa hannuwanta duka ta dafe kirjinta dasu tana zaro idanu waje "tace da gaske ni yake so ?
ummi tace zan miki karya ne" zeenat ta marairaice murya tace shine Kuma ummi zakice masa baki yarda ba.ummi tace to may kike nufi ,kina son kice min kina son DEENi kennan ? Zeenat Tayi shr dan bata da amsar bawa ummi dan gabadaya ilahirin jikinta bbu inda bai dauki rawa ba.
ummi ta sake yin magana daman kina son DEENi ne naga duk kin tada hankalinki haka ?zeenat tace nifa bance ina son shi ba Amman ke meyasa zakice A'a Kuma ma mayye dalilin dayasa kika ki amincewa ,ummi tace ok tutseni zakiyi" kan naki yarda ko yaya , zeenat tace ba haka bane" ummi tace tsaya ma kiji abinda yasa naki yarda, DEENi "da" nane' ni haife shi da cikina sannan ke ma kinsa halinsa sarai da shege miskilanci da saurin jin haushi mutun ,abu kankani ke hassalashi ga tarin girman kan tsiya, zeenat ta tsugunna nan gaban ummi hade kamo hannuwan ummi duka cikin nata muryarta sanyaye tace haba ummi dan day kawai saboda wannan halin nasa ne "zai sa kike amincewa , in dai dan haka ne' ni na amince da aurensa kinji .
ummi tace duk kinbi kin koma kalar tausayi wai ma meyye birgeki da DEENi ne naga duk jikinki ya dauki rawa haka ?.
Zeenat tace ai gaskiya yaya ba irin mutunmin da za'a tsaya cewa ba,aso bane ni dai na amince ,ummi tace ko kin amince, ni nace A'a ban yarda ba ,.
YOU ARE READING
AUREN SIRRI COMPLETE
Mystery / ThrillerMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan