Zumbar zeenat ta Mike tsaye tana dubansa ranta  abace ta nuna inda nablah ke tsaye da yatsansa hannunta Kana tace akan wannan yar iskar karuwar Kake son wulakantani da nunawa duniya ni din bawata tsiya bace agurinka?
A harzuke  muryasa na rawa jikinsa na tsuma yace karki sake ce mata Karuwa...... ummi tayi tsalle takaraso gareshi ta katse shi ta hanyar ce masa karka sake kace komai deeni. ......ban baka umarnin cewa komi ba deeni....
a fusace yajuyo zuciyarsa na dokawa da sauri yace enough is enough  ummi ....the game is over Now & nobody will  stop me to tell  the truth ....ba karuwa bace  ya fuskanci zeenat da kyau kirjinshi na wani irin bugawa *MATATA CE* Ta sunnah kmr yadda kike matata. yadda kike agurina haka take agurina koma ince har tafiki........ jikin ummi ya tsananta rawa kar karrr ta koma ta zauna jagwab kan kujerar mutun daya hade da dafe kanta ta hannuwanta duka tana kuka sharrrrr sharrrrr.
yayinda shi km deeni yacigaba da facing din zeenat yana mgn ransa a matukar bace... wayan nan ya'ya dakike ganin *haidar* *Anan da *junior* duk ya'yanane na halak malak Wanda ko yanzu inda babu ni a duniya sune magadana  sannan uwarsu tana da kima da mutunci a idanuna Wanda har duniya tane bazan daina ganinta da wannan darajar ba .
ita da mahafinta wanda shine ya Aura min ita batare da sanin koni waye ba da matsayin dana taka a fadin duniyar nan sannan da kafafuna na taka har zuwa gurin mahaifinta na roki aurenta agurinsa km ya amincemin ya Aura Min ita.
ummi tun haihuwar yaran nan yakamata ace an fito da sirrin boye....amman nake ta mike biyayya ummi zaki Kaini wuta km babu biyayya gurin sabawa ubangiji ga abokin halitarsa  nablah *Mamata ce* kmr yadda zeenat take Matata gabadayansu daya ne agurina....babu wani bambamci.. bansan meyasa kike son tauye Hakin nablah akan zeenat ba....Wani irin gigitaccen ihu zeenat tasaka ta fixge dan kwalin kanta dayagama karkacewa tayi cilli  dashi gefe tana karkada gashin kanta.. wallahi wallahi baka isa ba *DEENI* wannan  zance banza ne da daji ma ansan karyar ne wlh ta ina haka zata kasance kace dai kabi dare kabi duhu ka dirkawa wannan yar iskar karuwar ciki Amman ba dai wani aure ba wlh.. Ta zabura ta dauki glass cup din dake ajiye a saman center table ta cilawa nablah dake tsaye wace jinta da ganinta ya dauke sai idanunta dake tsaye kyam akan deeni .Tana kallonsa..
Deeni yayi saurin cafke glass cup din..tacigaba da ihu tana kururuwa wlh wlh karya ne  wannan abar tazama kishiyata .
amatukar razane takira Sunan ummi da karfin gaske ...ummi... ummi kina jin abinda yake cewa wanda ni nasan karya ne hakan baxai taba faruwa ba agidana.
Kishiya a gidana never in history tanakarasa fadar hk tayi hanyar kitchen da gudu.. ummi ta zabura ta Mike tsaye tabi bynta da gudu itama tana kiran sunanta. wanda sai lokacin nablah ta dawo cikin natsuwarta da kyau sannan km farat wani matsanamcin tsoro yashigeta jikinta yakama rawa ta rude tana neman hanyar tsira ..
ummi ta kwalla kara ta biyo zeenat tana kokarin kwace wukar hannuta Amman ina takasa tana fitowa nablah ta saki Kara itama wanda ya sake frigita yaran sukayo gurinta tare da rungumeta... deeni ya tsurawa zeena  ido yana kallonta rike da wuka sannan kausashe yace meyye hk ko kina hauka ne?
  Kai ne dai mahaukaci tunda gashin nan brain dinka ya juye kana fadar abinda bazai taba yiwu ba.
ke kuwa zaki ci kashi binshin kutumar ubanki yau ta nuna tsatin cikin nablah da wukar
Jikinta na wani irin tsuma. Wallahi yau sai kinga kudi kince kashine dan bazan barki ba sai naga bayanki gobe ma bazaki km zama karuwar wani ba MA ba mijina ba.zeenat zan mugun saba miki zan shuka miki ranshin mutunci zan baki mamaki wlh idan kika km cema yarinyar nan karuwa .
ummi  kina ji kina gani kiyi Mata mgn zan canzawa zeenat kamanin wlh idan bata gyara furuncinta bakinta akan yarinyar nan ba haba wannan irin maseefa ce hk ba aure na aureta.?dan ita kadai Allah ya haliceni?
jikin Ummi na tsuma tace yiwa hakuri karka mata komai dan girman Allah.  Allah Yayi maka albarka... Ya tabe baki kawai yana kallonsu yana girgiza kai.

Nablah tayi tsuru tsuru tana kallonta atsorace sannan muryata a raunane tace please aunty ki kiyi hakuri ki dawo cikin haiyaciki dan Allah ta yaya ma zaa yi mijinki ya zama nawa  wlh ba mijina bane km Nisan Allah duk abinda ya fada miki karyane ba gskiya bane kutumar ubanki ina mgn kina maidamin.
da mijina nake mgn badake bakar Karya munafuka maciya amana ta nufota ummi ta Saki kara tana kuka yau ME zangani ni fadeela Dan girman Allah zeenat ki ajiye wukar nan kada kiyi kisa kisa zuciyata ta buga.. Kada Allah yasa ta ajiye wukar ummi tana ganin idan ta illata yar mutane zaa kwaleta ne .
wlh da kaina zan hada da hukuma ahukuntata yarinyar nan Matata ce fine banga wani abun boye boye aciki ba ummi .
Muryar nabla na shake tace dan Allah mlm ka daina cewa  matakar ceni. wannan ma ai rainin hankaline tayaya ma hkn Zai kasance?
. Ta yadda ya'yanki ke Kama Dani kadai ya isa yasa ki fahimce komai km kisan hakan ma yagama kasancewa inji cewar deeni ya fada yana watsa mata kallon rainin hankali . Ko ki yarda ko karki yarda ni mijinkine km uban ya'yanki.

Zeenat tace Karyane bazata taba zama matarka ba sai dai Karu...ya daga hannu zai sauke mata wani gigitaccen Mari ummi ta katseshi ta hanyar buga masa tsawa kamin shr dan ubanka km wlh karka  sake kataba min lfyr yarinyar  da ME zataji?
da wannan maseefar data kunno Kai ko me? Wlh idan kayi sanadiyar da zeenat dina tashiga cikin wani Hali ko wani Abu yasameta nima bazan yarda ba.
ummi kinsani nasani nablah Matata ce ta sunan wace kece silar komai to meyasa kike nuna kmr bakisan komai ba ? Kodan banida gata bani kowa komai sai ki dinga nuna son kai akan zeenat........
Jin hk yasa zeenat yin cilli da wukar hannuta tare da ja da baya dafe da tsaitin zuciyarta tana kallon ummi wasu sabbin hawaye na tsiyayo mata bisa kuncinta ummi tarasa yadda zatayi da rayuwarta.. kawai tashiga girgizawa zeenat Kai zeenat ta zubara ta Kalli deeni  muryarta na rawa cike da in.. Inna tace karya ne wlh  badai ummina ba ummina bazata min hk ba ...Kai ban  ma yarda kayi wani aure ba ..nasan ko aure zakayi bazaka taba auran wannan yarinyar ba yar talakawa kaskantaciya Mara galihu wace tazo aikata domin Rashi da talauci ... ummi ta fashe da kuka tana kokarin Kamo hanun zeenat cikin nata.
deeni ya rigata ya damki hannun zeenat cikin nashi ya nufi hanyar step daita ta tokare taki mov ka sake maci amana wlh sai Allah yasaka min nasoka arayuwata. Numfashina ne kawai bazan iya fixge shi nabaka ba Amman karasa sakayar da Zaka min sai wannan tana kuka takarasa mgnrta tare da son fixge hannuta daga nashi Amman takasa sbd bakaramin riko yayi mata ba. Bai daita komai ba kawai  Cigaba da tafiya yayi da ita har yayi taku uku ya Dan tsayawa ya juyo yace  nablah ta biyoshi itama.
Da sauri ta girgiza masa kanta alamun bata zuwa tasoma neman hanyar guduwa batare yaranta ba.
Ya dawo ahankali ransa a bace ya kule Duka kofofin parlour gabadaya wanda zasu sada mutun zuwa waje gudun kada nablah ta gudu .
sannan ya nufi dakinsa da zeenat itama sbd tsaro ya tafi daita dan yasan kafin yaje ya dawo ta illata nablah. ya je ya dauko wayarsa wanda akayi video dauren aurensa da nablah ya dawo parlour km duk lokacin still zeenat na rike cikin hannushi gam jikinsa a  sanyaye ya hada wayar da makeken TV dake manne da jikin bangon parlour'n ya tsaita komai ya kunna gabadaya daga zeenat har nablah babu wace kirjinta bai buga ba Dan tsabar frigicin abinda zai  biyo baya.
gabadaya idanunsu nakan TV yayinda zuciyar ummi ta dinga tsalle tana tafarfasa jikinta na rawa rawa tana juya Kai tana uhmmmmm uhmmmmm deeni karkayi hk please tayo  inda TV yake da niyyar kashewa Amman ina aikin gama ya rigada ya gama dan Kafin ta karaso har mutanen ciki sun soma bayyana .
cak taja  tsaya tana salallami da ambato Sunan Allah gabadaya babu inda bai dauki rawa ba ajikinta .
daga zeenat har  da nablah zuciyoyinsu ke bugawa tmkr ana buga musu guduma.
deeni kuwa kamo   yaransa yayi ya zaunar dasu sai faman ajiyar zuciya suke ja suna fitarwa tsabar kukan da sukayi gabadayansu suka kwanto jikinsa . Sosai nablah ke kallon mahaifinta yana murmurshi tare da wasu daga cikin makwatansu na uguwarsu Take  jikinta ya dauki wani irin rawa karrrr..... karrrrr ....karrrr ta sake kurawa TV idanuta tana kallon komai azahirance.

A matukar frigice itama zeenat ke kallon tsirarrun mutane dake zaune suna gabatar da daurin aure har sanda taji an ambaci sunan mijinta km an daura auren dashi  Tana Gama jin hk ta saki wata razananniyar kara wanda gabadaya gidan ya amsa tare da  zubewa kasa sumammiya....................


Mmn sudais ce

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now