ahankali km ta daga idanunta sama Tana kallon sararin samaniya alamun son tuno wani abu dangane da rayuwarta .. sai lokacin komai ya dawo mata.... tashiga tunani tabbas last three weeks tayi zazzabi km deeni ne yakaita hospital da kanshi byn Sun fito take tambayarshi abinda doctor yace ke damunta. yace mata babu komai malaria ce.

Wani irin mahaukacin kuka ta saki tayi jefa itama da takarda hannuta tare da daura hannuta duka bisa kanta tana ihu da kururuwa tace wayyo Allah wayyo ni nabeelah na shiga uku ni km wannan itace *K'ADDARA TAH  na hauwa A usman jiddarh* sosai nablah ke kuka tana dubansu yayinda yaran suma  ke Kara volume din  kukansu abin gwaninsu ban tausayi. Deeni ya matso inda take tsaye tana zai ta bata tayi saurin gocewa  karkar tabani .....ta dakatar dashi afrigice gashin kanta dake xube abayanta suka hargitse  ta dawo tamkar wata zautauciyar makauciya . ita kuka yaran kuka. Ummi km sai rawar jiki take tana kiran sunan zeenat... Zeenat mushiga cikin gida meyasa kika Yi hk?
Meyasa baki gayamin ba...Kalli yadda idanun mutane ke kanmu.

Itama zeenat kuka take sosai tana girgizawa ummi Kai domin zuwa lokacin  gabadaya jikinta da brain dinta ya gama bata yaran da km cikin dake  jikin nablah na mijinta ne.
tabbas ta cuci kanta da kanta ta illata rayuwarta da rayuwar aurenta sai a lokacin abubuwa da dama suka shiga dawo mata daki daki tundaga muguwar kamar da yaran keyi da mijinta har zuwa yadda deeni kafkaf daita da yaran .
Da lokacin dayake yin kwana biyu kawai a dakinta sauran kwana biyu din baya zuwa gurinta km baya yarda tazo masa muddin bashine yaso hkn da kanshi ba.

lallai Tacika mahaukaciya mara hankali da tunani arayuwata ....wani irin mahaukacin ihu ta km sawa tayi kan nablah gadan gadan. Zata cafkota wuyanta .

deeni yayi kukan kura ya fizgo nablah jikinsa ya rungumeta tsam tsam ajikinshi ita da yaranta.... duk wanda ya Kalli fuskar Deeni yasan yakai kolowar bacin rai da tashin hankali.
Rikitattun idanun nan nashi sunyi jawur dasu tamkar an zuba masa barkono ciki .
gaban fuskarsa sun canza suma sunyi jawur..
ba zeenat ba har ummi sai data  tsorata da ganin yanayin da deeni yashiga bbu abinda yafi kona masa rai da taba zuciyarsa irin yadda zeenat ke kokarin hankada nablah waje babu kaya ajikinta ga kukan da yaran ke faman Yi fuskarsu tayi ja. Nablah na rungume ajikinsa da yaran ya nufi hanyar cikin gidan dasu zeenat tayi saurin tare hanyar tana jifansa da wani irin matsiyacin kallon....
Muryarta a matukar hassale tace bafa zata km taka kafarta da sunan shiga gidan nan ba.
Ummi tayi saurin janye zeenat da iyakancin karfinta daga bakin kofar Sbd  ganin yadda deeni ke aikomata da kallon tashiga cikin hankalinta dashi . Tasan shi , tasan halinsa, tasan tashin hankalin dake saurin haukatashi da wuri har ya autsina tunaninsa.. Yasa gabadaya arasa gane kanshi..
Ahankali yasoma takawa zuwa cikin gidan nablah na rabe da jikinsa suka shiga cikin parlour 'n .
ahankali ya zaunar daita akan kujera zuciyarsa na dokawa ya zauna yana facing dinta tare da tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da tausayawa... yayinda kaunarta ke  sake karuwa acikin zuciyarsa Tare da bin kowane part na jikinsa....tsawon lokaci yana zaune yana kallonta yarasa takamaimain abinda zai ce mata..

kukan kura zeenat tayi,tashigo cikin parlour 'n bata tsaya wata wata ba tayi kan nablah ta shako wuyanta  ta hada da yaran ta janyosu...... yaran suka sake sakin wata uwar kara duk suka frigice cikin kuka tace wlh baki isa kiyi Zina kina yin cikin shege kina kawo min gida ba .
mazinaciyar banza kawai gyaran muryar deeni yayi yana kallon tsaitin da ummi ke tsaye tana rawar jiki alamun tayi wani Abu akan haukan da zeenat keyi Amman sam ummi takasa aikata komai gabadaya tsaye kawai take bisa kafafunta komai yagama cakude mata waje daya Dan  kusan duk ummi tafi kowa tsurewa da shiga tashin hankali Mara misaltuwa banda rawa babu abinda Jikinta keyi takasa tabuka komai .

Baka jin komai a parlour'n sai hargagin ihun zeenat wallahi sai Sun bar min gidana daga ita har wadan nan shegun yaran tsinannu tabbbbbbbbb  wani irin yunkurawa deeni yayi a matukar fusace ya janyo zeenat  yayi wurgi daita gefe daya yana aika mata da wani irin kallo da jajayen idanunshi dasuka gama rikedewa suka canza kala yana fidda wani irin numfashin tamkr wani zaki  .....

AUREN SIRRI COMPLETE Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu