*DAMA TA*
*NA*
*BATUL ADAM JAJJKO**Zainab*
*Zeee*
*Na gaisheki kyuta*🌈Kainuwa writers Association 🤝
22
Kai kai meya yamutsu gadon haka?
Ai Nabil cikin zafin sa irin nayin ball yayi sauri ya dure inda yabacin dan yaga idon ta bai jenan ba yafara yamutsa wajen cikin dabara yana cewa "ai nena yamutsa saboda murna dan burina yakusa cika na rabu da wannan me idon cimolan
Yana yi yana jan hankalin ta tsaf ya mutsuke wajen.
Ita kuma kanta kaman ya fashe dan murna mijin ta ita ya keso "tace muyi addua Allah yasa ta aiho yan 2 namiji da macce kaga atake zamu sallame ta ko tunda kaga idan ta haife macce ni bazan yarda ba dole sai tayi zaman haihuwan namiji kaima idan ta haifi namiji kace baka yar daba.
Yace "wannan haka yake Allah yasa ta haiho 2 kawaiFandau duk taji me suke cewa azuciyar ta tace niko ai narabu da mutum nakama Allah dan shi yasan yadda zaiyi dani
Wani dogon rigan data hanya a bandakin shita sa tafito da sauri Hadim ta tashi ta kama hannun ta tazo da ita bakin gadon tana cewa mekike jine ajikin ki ba inda yake miki ciwo
Mekike sonci
Fandau da dama haka take so dan jitake idan bata shan kunun tsamiyan nan ba baza man lfy tace "kunun tsamiya
Dakuma kwakwa da dabino nakeso
Hadim tace "kai zaki samu kwakwa da dabinon de amma mu ina zamuga wani garin balle wani tsamiya
Nabil ya katse ta dacewa za asamu awajin Zahran Usman dan suna kawowa sosai.
Hadim da sauri tadauki wayanta takira Zahra take cemata tana son garin kunun tsamiya "toke kuma yau
Acewa Zahra
Hadim tace "eh Wllh akwai albishr me girma amma se kinzo da kanki dan baza ki sameshi a araha ba
Zahara tace "haba yar uwa dan Allah gayamin bama yar haka fa
"to tuda kince Allah meyake sa mata jin yana yin su yacan za kamar tashin zuciya amai kwadayi da sauran su
Zahra "tace ciki mana
Hadim tace "tom shine albishir din
Zahra tace "dan ALLAH gayamin Gaskiya
Hadim tace "nataba shimiki irin wannan wasan ne?
Zahra tace " a ah
Hadim tace to kiyar da wllh inada ciki one month
Wani ihu Zahra tayi tare da kashe wayan Hadim ta sauke wayan tana dariya bayan ta daukowa Fandau kwakwa da dabino tace"kiyi manager dawannan kafin akawo meyawan na aika asiyo
Itade Fandau kwakwa da dabino ta karba bakin har wani yawune yake sinkewa tafara ci
Nabil yace "yanzu waza afara gayawa a gida?
Hadim tace kai ma kasani ai iya rigima mana inna amma nafison nagaya mata da kaina ta fara danna wayan ta yi calling din nombar inna Zainabu tana dagawa Hadim tace "inna ina kwana.
Inna tace "mun wuni lfy dan munan darene Hadim tace "lfy
Inna tace maganan zuwan yaran nan huto modu da baso yake ba saida yasan yanda yayi basu samu viser bako dan nasan kede ba zaki hana ba
Hadim da ita tayi kutun kutun yaran basu samu zuwa ba acewar ta idan sunzo zasu iya sanin zaman Fandau a gidan
Amma sabar iya issa
Tace "Ayyya inna aishine nima naji shiru amma suyi hakuri ai mun kusa zuwa ma saura wata 3 sai muzo dasu tare
Inna tace "ai shikena sai kuyi zaman ku acikin wannan mahaukacin gidan naku
Danma kun kusa zama ku ukku dan bazan fasa gaya muku idan kunzo sai Modu yayi aure zaku koma ba.Dariya Hadim tayi azuciyar ta ' tace bade niba inde kishiya ce akan yaran ki da jikokin ki zaki yita gani.
Afili kuma tace "inna dama fa yatsmin?
Inna tace "gatanan
Dan Hadim ita kanta sai taji tana jin kunyan bude baki ta cewa Innan tana da ciki tayi danhaka take son tabata yatsmin din ta gaya mata.
Tana cikin wannan tunani taji muryan yatsmin kamar zai fasa mata dodon kune tana cewan
ALLAH kabar mana matar Big brother wllh anty Hadim nayi messing nake sosai.
Hadim tace "kwantar da hankalin ki yar uwa zan zomiki da alkairi
Yatsmin ce ta katse da cewa Hajiya anty sabon mota ne yafito kome idan mota kin san kalata ai fari tas dan ni banason wani kala idan kuma laptop
Nekin....
Hadim ta katse sa dacewa dallah dakata duk bawan nan bane yafisu wannan yafi komai na duniyan nan.
Yatsmin tace "meye anty
Hadim tace abinda kuka dade kuna jira ne nan watanni 8 zanba ku baby
Yatsmin tace "wai da gaske anty
Hadim tace "nata ba miki irin wannan wasan kuma kozan miki ai bazan kira a wayan inna ba itana kira naga yawa na kasa dan Allah kigaya mata
Yatsmin tace Wllh tunda kikace agayawa inna na yarda itama yatsmin ihun tasa ta fara
Tsalle tana cewa Wayyyo anty Hadim sunan dan ki yaki yan uba wllh kamar yanda muma bamaso amiki kishiya haka dan ma bayaso tana ta ihun haka Hadim ta kashe wayan
Haka suka dinka kiran mutane suna fada shima Nabil yana gayawa abokan sa kusan wuni guda suna abu daya duk wani abin da sukeyi hankalin su yana kan Fandau ko motsi tayi se sunce yaya
Ahaka har doc yazo da iyalen sa kan dole suka sauka a part din Fandau
DU LIEST GERADE
DAMA TA COMPLETE
RomantikLabari ne da baku tab'a jin irin sa ba, matarsa ce bata haihuwa mahaifarta tana da matsana, sai ta sashi ya auri wata yarinya a b'oye babu wanda ya sani daga shi sai ita, akan yarinyar ta haifa musu yara sai ya sake ta, da yarinyar tayi ciki, itama...