1

17.6K 491 9
                                    

Bismillahir Rahmanir Rahim

          *DAMA TA*

           
               *Na*
               
         *Batul Adam jattko*

1...
    KAINUWA WRITES ASSOCIATAN🤝   

  Tuki yake a hankali  cikin wata katuwar jeep kiran  vence, Yana karewa garin nasu kallo kamar ba anan aka  rage ran dunbin al umma ba  sosai yake kallon mutane  wanda yasan badan bakin glass  ne ba bai isa yayi wannan tafiyan ba, anguwan gargar anguwa ne na masu karamin karfi amma cikin garine sosai dan  makota suke da shewuri.  
       
Wayan sa ce tayi ringing  yajawo yadauka  yace " Allah yatemaki  ummi na  daga ummi tace "kamal be gaya maka inason ganin kaba   
Ya "gayamin ina gidan abba musa ne gani akan hanyan dawowa, 'tom kazo gidan yafatime  nasa hanif ya yauko Hadim dinma gata nan kazo muna jiranka.
Yace "ummi lfy kuwa
tace "se kazo de
   "tom yace cikin jimami  dan dagajin yanayi muryan ummi yasan babu lfy,
Sauke wayan yayi dai dai da  hango wata mata da take  taku dakyar  dalilin tsinkewan takalmin ta  ga shijab dinta a yage tabaya sosai   duk da bayan ta yake gani yasan tana bukatan temako  sosai dan shi baya ganin irin wannan yawuce
Horn yayi tare da dan zuge glass din kadan yanda baza agane shiba  yaci gaba dayin horn din amma matar ko juyowa batayiba  yadan sake lekawa  yace "iya ba kyajin ranane g.......
Magan nan ne yamakale masa   ganin yarinya.     wanda bazata wuce  15 ko  16  dasauri yakarasa  parking      dan zaton sa tsohuwa ce
cikin harshen barbarci  yace" ke  ba kyajin rana ko bakiga shijab dinki ayage ba  har yazu bata juyo ba 
   yayi wani tunani 'azuciyar sa  yace ko de mahaukaciya ce dan ya manta da halin yan Nigeria masu wasar da maskinan su a titi  
Danshi dafarko  yadauka  tsohuwa ce  yatemaka mata yakaita inda zai siya mata takalmi  
  
     Amma ganin yanda take taku anise yasa ya gane ba alamun hauka atare da ita    yasake cewa  ke bakiga hijab dinki ayage yake ba tabaya  kuma kina tafe cikin rana  
  Sai  asan nan  ta  juyo
Cikin tsoron taja da baya 
Ganin  bature yana kanuri sak   shiko yazuba mata ido  yana kallon ta  sai a sannan yagane  tana da zanen bare bari a fuskanta amma kanana sosai   kuma bibbiyu ce akowane kumatunta  kawai  ba irin taran nan nacika fuska aka mata ba  amma bakace sosai  duk da harda kazanta  karin bakin nata  hancinta baida tsawo  amma baza akirashi Tami lelle ba sai amfkin  ido wan kam tana da shi masha Allah

    Kallon ta yake yana tattare fuska dan wani irin yawu da yake taruwa a bakin sa dan shi yana da tsantsani sosai 
Daurewa Yagi yasake cewa "tom tunda bazakiyi magana ba ina fatan de ba kurma bace dan tambaya zanmiki
Ahankali tsoron ya dan ragu   tunowa da tayi ana aikin titi a unguwan  turawa suna yawan wucewa ta dan matso tace mezaka tambaya?

Yace "ina zaki? Ta  daga hijab dinta tayi ta nuna masa allon da yake rungume a kirjinta     tace "karatu 

Yace "tom ya akayi kike yawo takalmi a tsinke?
Tace "bayan nafito ne ya tsinke. 
Yace tom  "shi kuma hijab dinfa,?  tace" malam yace karna kara zuwa da wannan yayi datti.
'Azuciyan shi yace wannan dinfa 
   Tom meyasa baki sa wani ba kallon sa tayi
"Tace banida wani
  
Yace "tom  ni idan kinaso zan temaka miki kisiya kinji  ko har da kayama kinga wannan duk yakode    kina Budurwan  idan kina wannan shigan waze soki   tace " ai damage bawanda ya taba cewa yana  sona  shima  shatiman  da baba yace yabashi ni ya karbane kawai dan dole  dan yafi kowa tsanata acikin almajiran baban   balle samarin anguwan mu ko kallo na basayi  mata sanne masuke cemin yanga acikin datti ko yanga acikin tsumma  yanzu haka da kawaye na muke  tafe suka wuce ni  wai  bana sauri ko menakewa yanga acikin sun har da yan gidan mu  ta kareshi maganan kamar zatashi kuka
Shiko zuba mata ido yayi yana  kallon ta kai daga karshe ma har wayan sa yaciro yana  mata video  zaikaiwa Hadim  dinsa tagani yasan  abin dariya baya mata kadan  dan yasan yana bata lbr zata ce ya mata bakin kici da bai dauko mata ba  
Ya kawar da tunanin
Yace   zai soki kina wanka kina Gyaran jikinki kinji  ko amma ahaka ai ba zai soki ba   tace "tom ai ni mamarmu  makauniya ce bata aikin abinci sukuwa sauran matan kudin cefanen gidan suke dauka su sayawa yaransu kaya  muko sede mujira na babanmu sai sallah sallah yake mana  surutan ta  ya ishesa dan  haka yada katar da ita  m yace "tom  shikenan zan baki kudin da katina idan kudin yakare kimin mana zan sa akawo miki se kibawa mamankin tasiya miki duk abin d yan mata suke siya na gayu

Zaro ido tayi tace "kai maman ai fada Za tayi sai de na boye  nasiyi kayana da kaina  adena renamin   gabuwan har ta aiyana yanda idan tasamu sutuura zatayiwa yan gidan su,

Bandir din yan dubu dubu yadauko guda ukku yahada da katin sa yasa aleda yabata  takarba  tana godiya   sai a san nan ta kare masa kallo ta sake kallon sa  tace "ni kamar nasan ka  ina ganin fuska ka awani waje amma nakasa tunowa amma nake ga kamar a TV ne ko
dariya yayi cikin mamaki yanzu dama a Duniya akwai inda ba asan shiba  abin  mamaki ma akasansa akasan nashima acikin garinsu  amma wannan bakaraman  bakauyiya bace yana da tabbacin bayar gari bace kawai bayan gashinan yana zaune nan ma yana hango wani saurayi da riga me dake da photon sa ajikin sa yanzu wani ma yawuce da hulan me dauke da fuskan sa  murmushi yayi yace dan bani ledan nayi man tuwa  tana meka masa  ya bude yadauko  katin ya yaga wajen sunan shi ya bar wajen number kawai yameka mata  yace idan kina da matsalan kikira yaja glass yazuge ya tafi. 
Itakuma ko duba ledan bayayiba balle tasan meye aciki tafara sauri  dan tasan zata doku  awajen malam 
Adai dai gate din kofar gidan yayar  ummin kuma uwar matar sa  yayi horn megadi ya bude masa  yana daga maga hannu dan yane  waye  yayi parking yafito  yana daga wa megadi hannu  kai tsaye  babba falon gidan yashiga  gaban sane ya fara faduwa idan kunnuwan wansa ba yaudaran sa sukayiba sautin kukan  matar sa abin kaunar  sa ya bashi,
ai dasauri yakara sa shiga  itama  tana hangoshi da gudu ta karasa jikinsa habibi yawwa  kazo kagaya musu wllh  ba kason kowa seni kaji abinda su  mama da ummi suke cewa kuwa  kafada musu wllh bamu sara rayuwarmu  akan zamu zauna da wata ba kace musu nima zan iya haihuwa kamar yanda likita yace  karsu mana haka kace musu bana son kishiya zaku rasani  wllh zan kashe kaina  
Shi abin ma dariya yabashi 
Dan bai fahimceta ba 
Ahankali ummi ta taso takara sa gaban su  ta ja hannun su suka zauna tace  haba  Hadim dita  namiki bayani tunkafin yanzo naso ki fashinta ki nusu muyi shawara yanda zamu bullo wa al amarin  ni da uwarki ciki daya muka fito  yanda bazan so ace anyiwa jidda  da nabila da na haifa kishiya ba bazan so  amiki ba  se  dan dole  ki  daure ki fahimta kamar yanda mahaifiyar ki tafahimta  
Yayar mijin na bata son zaman lfy ita ta hada wannan abin tun farko bake taso  nabill ya aura ba  ZAINABU taso bashi acewarta mu shuwa muna mallake miji ni nagama da kanin ta dan ma bazan bar musu ba zan aura masa yar yar uwata mu mallake nabill din da shine karfin gidan  da ker alh yada ge akayi abin amma kinga wannan karon alhjn da muke samun  daurin gindinsa hardashi acikin bamu zabi  agabanki akayi komai 
Sun bamu wata shida idan baki samu ciki ba ko  yayi aure ko yasakeki ko muga
hukuncin da zasu yanke  ni nasan dama suna cike dani hukuncin da zasu yanke bazai mana dadi ba gwara muyankewa  kanmu kafin  suyanke mana ki daure ya,ta kishiya bazata miki komai ba da gani har mahaifiyarki muna dasu me suka rage mana
Kan uba se yanzu  Nabill yagane me ake nufi  cak yameke yana  kada kai sam ummi wllh ba a haifi uwar matar da  zan yiwa matata kishiya ba  kai ko mutuwa ta yi  ina kishin yi bata kishiya  ummi kubar wannan mgn dan harkun sa na tsaneta tunkafin  ace na aurenta   dan duk matar da  za ta zo gidan mu a matsayan kishiya ga Hadim ummi abin tausayice  kuma ai.....
"Kai dakata inji ya fatime  uwar hadim din ta katsehi 
                 *By*
          *Batul* 
*Muje jezuwa*
DAnba da shawara ko ne man karin bayani 08062383027

DAMA TA COMPLETE Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin