Da sauri ummi takaraso Inda suke  tana tmbyrsa lfy ?
ganin irin  kukan da nablah keyi.
DEENI  yayi shr kawai yaki cewa komai sai ma  cigaba da kallon nablah da yake  batare da ya amsa tmbyr da umminsa tayi masa ba .

Ahankali ummi ta dago nablah dake durkushe a kasa   .
tana tmbyrta lfy nablah make faruwa ? Me yayi miki ? Hk  ummi ta jera mata tmby .

shr kake jin  nabla dan  bbu bakin mgn  sai ma kukan da take risga da iyakacin karfinta  har da shesheka .

Ummi ta sake juyo inda deeni ke tsaye Wanda xuwa  lokacin ya sake gyara tsayuwarsa tare da cire hannushi a saman fadadden kirjinsa ya mai dasu 'cikin aljihun wandonsa yana ciciza lips dinsa .

Deeni....ummi   takira sunansa muryata  a kausashe. Kasa amsawa yayi  tsabar Haushi sai ma idanunshi daya dauke daga kan nablah ya maidasu gareta .
me yasame yarinyar mutane take kuka irin haka?
ko wani abu kayi mata ta jiho masa tmbyr a jere ..?

Kafin yace wani abu sai daya  numfasa tukun sannan ya sauke ajiyar zuciya" tare da   yatsina fuskashi" muryarsa a marairaice may cike da tsansar shagwaba kana   yace Gata nan a gabanki first love ta fada miki abinda akama mata .

ummi ta bata rai sosai tana dubansa sannan tace bafa nason rashin mutunci deeni ....

Kafita idona Na rufe  ...abinda kayiwa yarinyar mutane kawai  nake son sani ba wanin rainin hankalinka daka sabawa yiwa mutane ba .

Shima  hade rai yayi Sosai fiyye da dazu sannan yace haba  first lov ya a gaban yarinyar zaki dinga yimin hk  "salon kawai   ta raina mutane byn nima hk naganta bansan abinda ya sameta ba.

yana gama fadar hk ya cire hannushi daya cikin aljihun wandonsa" yabar daya ciki  tare da   juyawa ahankali yasoma daga kyawawan kafafunshi yasoma  takawa sannu ahankali 'cikin takun nan nasa  may matukar daukar hankali , Ya nufi bedroom dinsa  .. ummi tabi bayansa da kallon mamaki tana may  tabe bakinta  a ranta  tace rainin km Na nawa...

Yana shiga bedroom dinsa yaje ya zauna 'bakin gado yana fidda numfashi ahankali ahankali tare da tunanin matakin dayaka mata ya dauka akan kb da ita kanta yarinya.
a dazu daya gansu ji yake tamkar numfashinsa zai fuzge ne daga gangar jikinsa sbd wani irin radadin azabar daya shigesa ...

Zuwa lokacin tuni safeena ta kamo hannu nablah dake kusa da ummi  xuwa kan kujera tana tmbyrta abinda ya hadasu  da bros dinta. yayinda ita km nablah taki cewa komai sai kuka da take .

Ahankali  ummi takaraso kusa dasu ta zauna itama.
" tmbyr duniyar nan bbu irin Wanda ummi da safeena basuyi mata ba Amman Sam nablah  taki cewa Ga abinda aka mata sai hawaye ne kawai ke fita daga idanunta ..

tun tana kuka a zahirance har ta dawo kukan zuci .. yadda taga ummi duk ta damu ne.
Yasa duk  jikinta yayi tsanyi Sosai ta sausauta kukanta tare goge Hawayen idanunta .. jikinta a sanyaye  ta bude bakinta Da kyar tamkar may koyon mgn  takira sunnan ummi ...

ummi ta amsa tare da juyowa ahankali ta zuba mata idanun  kawai  tana kallonta hade da nazarinta ... sannan tace uhm nablah Ina sauraranki mekike son cewa ?
'cikin muryata may matukar sanyi da ban tausayi tace da Allah  ummi  Ina son zuwa gida naga mamana da sauran yan'uwana, takarasa fadar haka hawaye da yayi saura a idanunta yasamu nasarar silalowa  kan  kuncinta .

ummi tayi shr for the mean time   tana cigaba da nazarinta sannan daga baya tace shine daman  abinda Yasa ki kuka hk ?

Nablah ta girgirza kanta da sauri  tana duban kasa.

  to fada min meyye abinda yasaki kuka ? Ko km  waccen babban kobon ne  yayi miki wani abu?

  muryata a raunane tace a,a ummi bbu komai fa  Dan tasan koma ta fada mata  , abinda yayi mata ba komai za'a yi masa ba ya rigada yacita  bulus..

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now