Zeenat nabarin gurin Shima deeni ya Mike ahankali yana kakkabe jikinsa  ranshi watse da marin da zeenat  tayi mata  , murna fal cikinsa yayi hanyar step ...
Ko rabi baiyi ba .
ummi takira sunanshi  deeni ...Ya dan  tsaya tare da juyowa yana duban ummi. kaje dakina ganin nan  zuwa yanzu .


Deeni zaune a parlour ummi akan doguwar kujera ,yayinda ummi ke zaune a gefeshi ,tace tunda kadawo daga gidansu yarinyar nan nablah banji kace dani  komai ba?

idan  kasan da cewa bazaka iya bi zabina   bane ka fito kasanar min . Ba wai ka dinga min yawo da hankali ba kmr wata abokiyar wasanka..deeni ya marairaice murya haba first love  meyye kawo wannan  mgnr ?
Wlh  naje gidan nasu km har  ,nagana  da mahaifinta  km har angama komai .

Bangane angama komai ba ummi ta tmby ?
ya juyo sosai yana fuskantar ummi da kyau sannan  yasoma mata bayanin duk yadda sukayi da mahaifin nablah har zuwa inda aka daura musu aure  tare da fito da wayarsa yana Nuna mata video dayasa sule yayi lokacin da'ake daurin ,auren . Yanagama nunawa ummi yakira number  sule tare da saka wayar a handsfree ,muryar sule direba ta bayyana raudau ,shima dai Karin bayani yayi mata  akan yadda daurin auren yakasance sannan deeni yayi hanging din kiran .

ummi naga jin yadda komai ya tafi 'cikin tsari Yasa ta saki ranta sosai ba kmr tun farkon shigowarta dakin  ba tace yauwa Haka nake son ji alhamdulilllahi
,Dan har Na  dauka ko bazaka bi zabina bane ?

'Cikin sarkewar murya yace a koda yaushe banida zabin daya wuce na ummina duk abinda kike so shi nima nake so akan wannan baza mu taba samun sabani ra'ayin ba.
farincikina shine nakasace may biyayya a gareki.
dan Haka banida yadda zanyi  auren yarinyar shine mafuta kawai  atare dani..
  Ni km hk tawa kaddarar auren yake zuwa min zuciya bazata taba samun zabinta ba .

Tsananin tausayi furunci deeni din ne yakama ummi  Amman km bata jin zata iya canza ra,ayinta akan  qudirinta .

Parlour ya dauki shr koina yayi tsit tamkar ba masu numfashi aciki. baka jin motsin komai Sai Na sautin TV.
ummi ta nufasawa tare da kokari kawo karshen shirun nasu ta hanyar  cewa Allah yayi maka albarka deeni duk abinda kake nema a duniya da lahira Allah yabaka. biyayyar da kake min kaima Allah yabaka ya'ya shiryayyu da zasu maka fiyye da hakan .

Ameen first love ya fada tare da Mikewa kan kujera ya daura kansa akan cinyarta tamkar dai yadda kananun yara  sukeyi  , tare da lumshe rikitattun idanunshi .

Ahankali ummu takai hannuta kan sumar kanshi dake kwance luf..luf Sai sheki suke da daukar hankali 'cikin tautausar lafazi may tsanyi ta Kira  sunanshi...NASURULDEENI ....kwata kwata bashida niyyar amsawa Amman yadda umminsa takira complete name dinshi ne yasa dole ya amsa mata da  Na,am first love a kasalance  domin yasan duk abinda yasa umminsa kiran ainihin sunan haka abu ne may mahimmanci .
dan Haka ya tattara duka hankalinsa gareta .

Banason abin nan ya dau lokaci sbd da Haka ka hanzarta raba masu kwana kmr yadda addinin Muslinci yatanadar. kwana biyu biyu ko day day ,tunda ummi tasoma mgnr raba kwana numfashinsa ya nemi daukewa cak.. ko motsi  bai yi ba  har ummi ta dasa aya.

idanushi a lumshe suke , zuciyarsa ke mishi radadi da suya tare da takaicin mgnr ummi .
dan Haka muryarsa a dan zafafe yace kina nufi dakinta zan dinga zuwa ? Itama ummi a zafafe tace
Kwarai kuwa  ko bazaka iya bane?

Ganin yadda ummi tayi ne Yasa shi cewa Ni Na isa nace bazan iya zuwa ba  Sai dai wlh Ni  kunya nakeji  yakarasa  fadar  Haka cike da shagwaba tare da yatsina fuska.

Ummi tacigaba da shafa sumar kanshi ahankali daga karshe tace daurewa zakayi kaje gareta badan ta isaba Sai dan bukatar mu .
Deeni dake kwance ya sake yatsina fuska alamun Yashiga sarkarkiyya da kyar ya iya bude baki yace shikennan first love zan ware lokaci da zanje gareta .
Ummi tace wani irin zaka ware lokaci zuwa gareta ?

Kawai yau zuwa gobe ya Isa ka tsara komai dan bamuda wani  ishashen lokaci batawa .

A kidime deeni ya Mike zaune yace haba haba first love karki min hk man  wani irin yau zuwa gobe gsky ni gobe  yayi min wuri  dan ban shirya zuwa gareta a gobe gobe nan ba .
  Amman I promise nest week  inshallahu .

Nest week Yayi nisa deeni kayi kokari kaje gareta zuwa jibi .
Tamkar may shirin rushewa da kuka yace uhmmmm alamun yaji kawai  ummi tayi murmushi jin dadi hade shafa gefen fuskarshi da tafin hannuta duk kabi ka wani  rikice tamkar may jin  tsoron yarinyar .

deeni ya zaro idanun waje yana wa ummi wani irin kallon shi din ne yake jin tsoron yarinyar da loma daya zaiyi ya gama daita.

haba first love .. yau km nine matsoraci yana may Nuna kansa da yatsansa sannan yacigaba  tsorona ma  ya rasa inda zai kare Sai akan mace ...mace ma housemaid dina.. ummi tayi saurin daga   masa hannuta ok yaisa to Ai  kai din ne naga duk kayi wani irin tamkar kana jin tsoronta .

Alhalin nina san yarona jarumin jarumai ne..
  sadaukin nmj abin sha, awar kowace macce.
,kaga yarinyar nan bata da wani aibu uwa uba  tana da kyau sosai .
idan  Allah Yasa ma akaci sa'a bbys din duk sukayo kama daita .
Kaga zamu samu    kyawawan bbys  daga gareta.

duk maganganun ummi bbu wanda yaji yafi bata masa rai kmr wai yana jin tsoron yarinyar da wai tana da kyau.
dan Haka ranshi a bace yace Ni first love ki daina wani  cemin tana kyau .kyawunta Na banza ... tunda nasan ko kama kafar mamata batayi ba a kyau  ballanantana Ni .

banason ma ya,yana su wani  yi kama daita zanje dai gareta ne kawai sbd cika ummirniki badan wani kyawunta ko me ko me....kawai ya Mike tsaye   dan yaraba kanshi da sake jin zance yarinyar da ummi tasaka shi gaba dashi .
dan zamansa agurin zai iya hadasawa zuciyarsa kamuwa da wani ciwo may tsanani  .

Zuciyarsa cike da Haushi ya nufi dakinsa ya murda handle yashiga bedroom tare da fadawa kan makeken royal bed dinshi da jan tsaki yayinda bakinsa ke fidda wani irin iska may zafi. hannuwanshi duka ya daura yayi pillow dashi Tare da kurawa celling daki ido tamkar may karanta wani abu..
,bbu abinda yake Banda tunanin yadda zuwansa gurin yarinyar zai kasance tsawon lokaci ya dauka kwance yana kallon celling dakin kafin daga baya ya sauke naunauyen ajiye zuciya may karfi gaske ..
yafara zance zuci ta Ina zan fara ?
A zahirance zanje mata ko badinance ?
Zuciyarsa tabashi amsa kaje mata kawai a dakenka sak .... a,a kada kayi Haka ka tsaya dai ka natsu tukun kasan ta Inda yadace kaje mata..
ya sake furzar da iska tare da jan tsaki mtssss ko ma a ya'ya naje mata dolenta ta saurareni km  Hakan  bazai hanani cin ubanta ba da wannan sabon  iskanci data tsiro min dashi ..
, har kmr Ni ya Nuna kanshi da dan yatsansa wata diya macce zatace Ina  damun rayuwarta ina shiga lamarinta .
shi deeni da kanshi ya girgirza kanshi kawai yana sake jin haushinta ...


Ranar Wednesday yakama rana da ummi ta umarce shi da zuwa gurin yarinya.

dan Haka tun a safeyar ranar yagama shurinsa tsab  ta yadda zai isa Gare   a saukake .

Zaune yake a dakinsa ya tasa CCTV camera dinsa ...



MMN SUDAIS CE

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now