ya Mike ya rikota yana mata sannu ya kwantar daita ya akan bed ya lullubeta da bargo jikinta sai rawa yake .

A ranshi yace abu fa ya km  samu  manya iyayen son jiki da raki ,

Yayinda ita  km take  maganar zuci kardai ciki gareta alhalin bata shiryawa hakan ba.
    " wani mora rayuwarta tayi da har zata km daukar wani ciki yanzu ta  rufe idanunta tare da jan tsaki a ranta  . Yaka barinta har sai dayaga alamun bacci yasoma daukarta

Kallonta yacigaba dayi tana bacci wanda dagani bana jin dadi bane dan  Sai juyi take tana girgiza kai . Ya cire wayar yana neman doctor saira amman sam takishiga.

ya Mike ya fice daga dakin mukulin motarsa ya dauka ya sauko parlour kasa yacikaro da rahma tana gyran parlour suna hada ido ya sakar mata harara ya fice .

A sukwane tabi bayansa da kallo tana mugun    son kallon ogan madam dinsu.
yana da tsarin jiki may kya
,ita dai tana matukar son shi  da aure dazai aureta  Amman tasan bazata taba samun miji kmr sa ba.
,gashi sai bata kudinta take abanza ko kallon arziki bata samu daga gurinsa .
AHankali ta saki ajiyar zuciya . Tarasa yadda  zatayi tasamu ya Amince datai .
Ko   shanawa sudingayi  , kyauta ma sai  ta mallaka masa jikinta batare ko sisinsa ba  .

tayi kwafa ta shige dakinsu tana may  ayyanawa ranta muddin tana cikin  gidan sai takashewa kanta kishirruwansa dake makale da makoshinta .

Yashiga motarsa sai asibiti doctor saira dan yanata neman layinta bata dauka ba  bai damu da masu gaishe shi dashi ba ya haura samanta kawai ya wuce office dinta  ya same zaune tana rubuce rubuce   idannuta manne da medical glass tana ganinsa ta sakar masa fuska suka gaisa fine  ta nuna masa gurin zama tana tmbyrsa madam .

Ya danyi murmushin ai saboda ita ma naxo  dan gabadaya bangane kanta ba yau .

Meyasa meta inji cewar doctor  ?

Nidai nashigo dakin naga  ,sai amai take kwarawa ni dai je ki duba minta dan Allah .
Dan  nasa bai wuce ciki gareta ba .
Amman ki riko kayan aiki.

, Tayi murmushi ta Mike tashiga hada  kayan aiki ta dauki ruwan allura guda daya ta rufe glass din da  magunguna da abin awo .

Tace suna  iya wucewa suka fito ta kulle office dinta .
suka sauko kasa zuwa inda yayi parking din motarsa yana shiga gidan ya iske  rahma kwance a parlour tana kallo TV ranshi yayi mugun bacci da  iskanci datake masa acikin gida  azubure ta Mike ta zauna tana kallonsa Dan  taji dadin  ganinta da yayi cikin mini siket.
duk   da  bata yi tunani.  dawowar sa ba .
ta dauka ya wuce aiki kennan  .

Ta tabisa  da kallo .
Har ya haura sama shida doctor saira . Sannan ta sauke idanunta akansa .

tana maganar zuci lallai yakamata ta sake Mikewa tsaye  akan yadda take  dan gaskiya muradin kasancewa tare dashi .

Tayi murmushin mugunta ta shige dakinsu ,ta iske moris kwance tana karatun Bible ,dan ita Tunda madam tanuna  bata son zaman su a parlour ta kiyaye kanta.
iya karta kitchen da deaning wanda duk akwai kofar shiga ta cikin  dakinsu  dazata kaita  kai tsaye .

Fitowarta kennan daga bayi byn tagama kwarara amai suka shigo dakin  sai rawar sanyi take ganinsa da doctor saira yayi matukar bata mamaki ,ta zauna tana gaida likitar ,,ta amsa tana mata yajiki tare da mata wasu en  tambayoyi .

ta Mika mata wata  Yar karamar kwallaba tayo fitsari aciki .


Byn kmr minti goma doctor saira tagama yiwa zeenat  test tagane tana da shigar ciki wanda batasan iya kwanakinsa ba , ta Ciro  drip tayi alura aciki ta daura mata ,tare da magani .Ta nuna masa yadda zai cire mata idan ruwan yakare .

AUREN SIRRI COMPLETE Où les histoires vivent. Découvrez maintenant