chapter fifty four

1.5K 76 5
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

54

Ana gobe suna su Al'ameen suka iso Abuja...murna a wurinsu baa mgn da sukaga baby..har rigima akeyi wnn yana shi zai dauka wnn Yana shi zai dauka...a ranar Kuma da yawa daga cikin family dinsu na kano sun iso...mutanen Dutse ma mota kusan biyar sukayi suka taho suna...Ta ko Ina Yan iwa da abokan arziki sai zuwa sukeyi..

Shirye shirye sukeyi sosae sai kace taron biki ne ba na suna ba...umma ce ta dauki nauyin komai na suna hatta hall da zaayi taron a ciki ita ta kama..babu yanda ummi dashi kanshi Taheer din basuyi da ita kan ta bari ba amma Sam tace wnn taron nata ne tunda ita akayima takwara...har mawaki ta gayyato all the way from Kano..ga kuma cards da aketa bi ana rabawa mutane sai kace biki...

Washegari...

Tun safe dama aka yanka raguna kmr yanda al'ada ta tanadar...duk inda ka kalla a gidan zakaga cike yake da jama'a...tun safen Kuma masu kidan kwarya sukazo suketa faman kidi suna wakokinsu..sai wake Aysha Nawal suke mutane nata musu liki...umma Kam har rawa Saida ta taka itada Ramla..su ummi ma sun fito sunata likin kudi...mai jego kuwa tana ciki itada babyn da sauran mates dinta...taci kwalliya har ta gaji da haduwa itada baby Nawal.

Karfe biyu daidai make up artist ta iso gidan don yima mai jego kwalliya...a part din mahaifin Taheer aka sauketa don nan ne ba jama'a..basu bata lokaci na Kuma suna fara..suna tareda Hanna dake gidan itama tun safe...

Acan cikin gidan kuwa su ummi ankon lace sukayi Sea green..gaba daya sunyi dinkin bou bou iri daya...Ummi..Umma..Ramla..Nafee da Kuma Hibba..sunyi kyau MashaAllah har baa mgn...bayan sallahn asr aka fara diban mutane ana kaiwa hall din da zaayi sunan...Su ummi sune kusan na karshe a tafiya..

5:30 daidai aka gama ma Layla make up dinta...tana sanye cikin Lace dinta Blue Black..mayafi da Kuma head dinta suma blue black...sai diamond necklace dinta silver..purse da takalminta ma duk silver ne...Ni kaina dana kalleta sai dana furta Tubarakallah MashaAllah sbd tsabar kyan da tayi...Aysha Nawal kuwa tana sanye cikin dan gown dinta blue black da fari...ansa mata dan band dinta mai kyau a Kai shima white..sai showel da aka nadeta ciki shima white...kallo daya zakayi musu kaji sun shiga ranka matuka sbd tsabar haduwan da sukayi...Saida aka gama ma Hanna light make up dinta snn suka fito don tafiya wurin taron...

Angon karni kuwa tun safe ya wuce gidan Yusuf...Yusuf din nata tsokanarshi wai baban baby da baby amma kobi ta kanshi baiyi ba...sai karfe hudu snn shima ya shirya cikin Shadda sky blue snn suka nufi hall din shida Yusuf da some of friends dinshi...Allah ya sani da anbi ta nashi ba wani party da zaayi organising..shi ba son wnn harkan yakeba kwata kwata..don dai babu yanda zaiyi da Umma ne shiyasa zaije amma shi baa son ranshi zaa sa matarshi taci uban kwalliya ta shiga cikin Arrijaalu kowa ya kalle mai itaba...

Isowansu wurin yayi daidai da isowan su Layla ma...tunda ya dora idanunshi a kansu yaji tamkar ya Dora hannu bisa kai yace wayyo Allah sbd tsabar kyawun da yaga sunyi..they look absolutely breathtaking...wani irin so da kaunar su na sake mamaye ilahirin jinin jikinshi...kawai sai ya lumshe ido tareda jingina jikin mota yana dafe saitin heart dinshi da hannu...shi kadai yasan abinda yakeji cikin zuciyarshi...shi har yanxu bai yadda da ake cewa wai idan anyi aure soyayya na raguwa ba..coz kullum son baby karuwa yake cikin zuciyarshi bai tabajin ya ragu ba..ga kuma little Umma da yakejin sonta itama har cikin jininshi...yana sonta fiyeda komai...Yusuf ne ya jashi suka karasa inda suke...umma ta fito daga cikin hall din ta amsa Nawal dake hanun Layla snn suka jera tareda few mutanen da aka jera zasu shiga dasu ciki..

DJ najin zasu shigo ya sakar musu waqar Gimbiya Aisha ta Ali Jita...wai ya sadaukar da ita ga hajia Aisha uwar taro..da Kuma takawararta Aisha Nawal..

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now