chapter ten

1.3K 77 0
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf✨

Wattpad@ummuashraf22

10

Washegari Monday da wuri yai Shirin office as usual ya shiga part din ummi ba kowa parlor don haka ya wuce bedroom din ummi...tana  zaune kan dadduma tana lazimi Layla Kuma na kudundune cikin blanket a kan gado...ya karaso cikin dakin ya zauna yana mamakin ganin Layla....a nan kenan ta kwana baa dakin nata ba...Ummi ta shafa adduanta snn ta juyo tana kallonshi"ummi Ina kwana"ya fada yana Mata murmushi...ta amsa da"lfy Lou Taheer ya jikinka..jiya Layla tacemin wai kanka ke ciwo..ya Dan shafa Kai yace"naji sauki ummi...sai ya kalli Layla dake kan gadon yace ummi a nan ta kwana ne?..ummi ta ninke daddumarta snn tadanja siririn tsaki tace"ai Layla dai Allah ya nunamin ranar nutsuwarta..kawai sai farkawa nai naji mace a bayana ta wani makaleni kmr zata koma ciki..Taheer ya danyi murmushi ganin yanda unmin ke mgn snn yace "ummi to mene a ciki donta makaleki ummi... dadi ma ya kamata kiji baby ta kwanta a jikinki...tun bai rufe baki ba ummi tace"Allah ya sawake..mudai Layla Kuma ai sedai Allah ya fiddamu kunya a gurin mijinda zata aura...yarinya sai son jiki kmr kyanwa..ta wani makaleni ta hanani bacci kmr jaririya...haka zaayi Mata aure taje tana makale miji ta hanashi bacci knn...dukda yanda mgnr ummin ta sokeshi jin ta ambaci mijin Layla saidaya danyi murmushi jin abinda ta fada din..yasa hanu ya yaye bargon data lulluba dashi don yasan tana jinsu Sarai ba bacci takeba...ta juya baya da sauri tana turo baki...yai murmushi yace"yau ni din ake juyama baya baby...batace komai ba sai kawai ji tayi ya janyota zuwa jikinshi...cikeda takaici ummi tace kaidai Allah ya shiryeka wlh..ya yarinya zata aikata laifi ina fada maka maimakon ka mata fada sai ka wani janyota zuwa jikinka...Kai har yanxu kallon jaririya kakema Layla koh...bazaka dinga tsawatar Mata akan laifi ba saidai ka ringa sangarta ta koh...yai murmushi yasa hanu ya manne Layla daketa mustu mustsu a jikinshi gam snn ya kalli ummin yace"laifi nayi mata fa shine zan bata hakuri...ummi ta saki salati tace"to kuwa abun naku ya zama innalillahi wainna ilaihi rajiun.... wlh tun wuri ma kayi ka fito da matarka...kayi aurenka ka tafi can ka barni inyiwa yarinyar nn tarbiyyan daya Dace...don wnn halin da kake koya Mata Sam ba halin zaman gidan miji bane...tana karasa fada ta fice daga dakin tanata bambami.
Bayan fitanta ya Kai dubanshi ga Layla da tayi luff a jikinshi kmr ba ita ce ke kokawa dashi ba dazu...yasa hanu ya janyeta yanajin yanda abubuwa da dama ke Kai kawo a cikin jini da tsokarshi game da ita...Sam baima ji abinda ummi ke fada da kyau ba cox his heart has gone so far da babu abinda yake tunawa sai ita sai Kuma muradin kasancewar tareda ita har mutuwa...ganin zata fara mai kuka ya girgiza Kai tareda janyota jikinshi yace"baby mana...don't cry plss...am sorry for sending you away last night hakan bazai sake faruwaba kinji"...ta dago tana kallonshi snn ta jijjiga mai Kai...yai murmushi yace kin hakura?nanma Kai ta sake dagawa...ya manna Mata kiss a forehead dinta snn ya mike yace "alright ki koma baccinki baby na tafi aiki...tace sai ka dawo snn ta koma ta kwanta shi kuma ya fice a dakin...ya samu ummi da Mama hawwa a kitchen yai musu sallama ya tafi ummi nata fadan don me bazai tsaya yayi breakfast ba.

Koda yaje clinic ayyuka sunmai yawa sosae amma duk da haka batun auren Layla na nan makale a zuciyarshi he wish zuciyanshi na iya mantawa da batun son Layla ya cigaba da rayuwarshi kmr yanda yakeso Amma inaa...ya kasa gane wane irin abune wnn...wane irin jarabawane wnn...why Allah zai jarabceshi da son Layla bayan bazai sameta ba...yai saurin istigfari jin zai fara kauce hanya ya cigaba da aikinshi.
Around 5 sai ga Yusuf yazo...bayan sun gaisa Yusuf ke tambayanshi abunda ke damunshi...yai shiru kmr bazai fada ba sai Kuma daga karshe yaima Yusuf bayanin komai...ya Dora mai da fadin shawaran daya yanke na zai amince da auren matukar Layla ta amince...shawarwari sosae Yusuf ya bashi tareda bashi kwarin guiwa kan abinda yake Shirin yi...snn ya bashi shawaran ya samu ya fidda mata shima yayi aurenshi if possible kafin ayi na Layla don hakan zai taimaka wajen mancewa da son Layla snn zai faranta ran umminshi... Taheer yayi naam da wnn shawara ya Kuma tabbatarwa Yusuf hakan zaayi Amma zai fara mgn da ummi...sai da sukai sallar magrib snn Yusuf ya tafi gida shima Taheer din ya nufi gida feeling exhausted.

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now