chapter thirty five

1.4K 88 2
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

35

Suna fitowa Hanna ta wuce don already Habibinta na waje yana jiranta...Layla ta rakata suka gaisa dashi snn ta samu wuri ta zauna nn parking lot din tana jiran Taheer...zuwa yanxu maranta ciwo yakeyi sosae...bata taba tunanin she is this strong ba sai yau...bata dade zaune a wurin ba ta hangoshi yazo...ta wani kauda Kai ita a dole yayi mata ba daidai ba...tun kafin ya gama parking dama ya hangota..so yana yin parking din ya nufi inda take...Yana isa ya kama hanunta ta mike tsaye..still bata kalleshi ba...shi Kuma yai murmushi snn ya shiga janta har zuwa inda motanshi yake..ya bude tareda sata ciki snn shima ya zagaya ya shiga...bayan sun fara tafiya ya dubeta har yanxu bai dena smiling ba yace"come on talk to me mana baby..sorry for keeping you waiting"...yana rufe baki ta juyo tana kallonshi da idonta daya cika da hawaye tace"bani da lfy..tun daxu nake jiranka baka zoba"...ya kamo hanunta ya rike yace"to kiyi hakuri ki yafemin kinji...wasu mutane aka kawo emergency wlh..I can't leave ba tareda na dubasu ba"...batace komai ba sai kifa kanta da tayi kan laps dinta tana cigaba da kuka don ciwo yake Mata sosae...Taheer na rikeda hanunta har suka karasa gida...ko parking din kirki baiyi ba ya bude motan ya fita...ya zagaya side dinda take ya dauketa cak yai cikin gidan da ita...Saida ya haura sama har dakinshi snn ya ajiyeta kan gado..ya lalabo injection da zaiyi Mata da sauri ya shiga withdrawing dinshi..yana gamawa ya karasa inda take ya dagota..yana share Mata hawaye shima kmr zaiyi kukan yace mata"baby kukan ya isa haka don Allah..bari inyi maki alluran..kinci abinci dai koh"...tana hawaye ta daga kanta alamar taci..shi Kuma Taheer ya mikar da ita tsaye snn a hankali yayi Mata alluran...Yana gamawa ta sake rushewa da kuka tana kokarin durkushewa a wurin ya kamota jikinshi da sauri...ya kwantar da ita kan gadon shima ya zauna gefe...hanunta cikin nashi yace"baby dan girman Allah kibar kukan nn haka..you have no idea of what am feeling right now..da ciwon naki zanji ko da kukan da kikeyi..or do you also want me to cry?.."ta girgiza mishi kai da sauri..ta sake rike hanunshi dake rikeda nata tace"to na dena daddy..amma fa ciwo yakemun inaji kmr zan mutu ne dad...tun kafin ta karasa ya katseta ta hanyar rufe Mata baki da hanunshi...ya janyota ya dora kan laps dinshi..yana kallonta da idanunshi da sukai jaa sosae kmr zaisa kukan shima yace"ki dena cewa zaki mutu don Allah baby..bakijin tausayina koh"...Layla ta sake lafewa a jikinshi tana sauke numfashi...shima ya gyara mata kwanciyan a jikinshi yana goge Mata hawayen yace"InshaAllah Zaki samu lfy kinji koh..bazaki mutu ki barni ba Bi'iznillah"...

Daren nn dai basu samu isashshen bacci ba...sai wurin karfe 3 ciwon ya lafa Mata shine ta samu bacci...shikam ji yayi bazai ma iya baccin ba...jiki a sanyaye ya mike zuwa bathroom ya dauro alwala snn ya fito ya fara sallah.

Da safe data tashi ta samu sauki sosae...ya dauketa da kanshi zuwa toilet din dakinta...ya hada mata ruwan wanka tayi..ya taimaka mata ta shirya snn yace bari ya siyo musu breakfast ya dawo..kememe Layla ta hanashi fita wai ita lallai bazai sake zuwa eatry siyan abinci ba..gashi Kuma ita bazata iya yin girkin ba..haka nn ya hakura ya dafa musu tea da kanshi snn ya soya kwai..ya dauko bread da jam..ya hada komai kan tray snn ya dauka zuwa sama..ya ajiyesu nan dinning din dake parlon snn ya shiga dakinta ya fito da ita...sai mita takeyi wai ita zata iya zuwa school ta samu sauki amma ya hanata...yace Sam bazai yadda ta bar gida ba sai ya tabbatar da she's alright.

Bayan sun gama Breakfast din suka cigaba da zama nn parlon..ya kunna musu wani movie a system dinshi sunata kallo..tana lafe a jikinshi bacci ya dauketa...ya maidata zuwa dakinta ganin time din sallah yayi...yana fitowa ya daura alwala snn ya tafi masallaci...bai wani jima a masallacin ba ya dawo..don hankalinshi gaba daya yana kanta..baiso ta tashi daga baccin bai dawoba..yana haurawa sama sai yaga har yanxu bata tashi a baccin ba...ya zauna knn zai cigaba da kallon da yakeyi yaji ana danna doorbell...ya ajiye system din ya sauka kasa..yana tunanin wane bako sukayi ya isa kofan ya bude...sai ya zare idanu ganin Ummi da Umma tsaye a bakin kofan...ummi tace"ko mu koma ne naga ka wani tsatstsaremu da ido"...Taheer ya saki smile snn ya matsa daga hanyar suka shigo...yace"ummi ai banyi expecting dinku bane shiyasa..sannunku da zuwa"...bata amsa mai ba suka karaso parlon suka zauna...shima ya zauna kusada umma...bayan sun gaisa ya mike zuwa kitchen tareda dauko musu drinks da ruwa ya kawo parlon..bayan ya zauna sai ya kamo hanun umma cikin nashi yace"nayi missing dinki sosae ummata"...umma tai murmushi tareda shafa kanshi tace"and I missed you more"...ummi dake zaune gefe tana dubansu tace"Ina matar gidan takene wai..ko an tafi makarantan ne"...Taheer yace"yau bata samu zuwa makarantan bama ummi..batada lfy"...ummi ta zaro idanuwa tace"batada lfy Kuma..meya sameta ni Maryama"... maimakon ya amsa mata sai ya mike yace"muje ku ganta tana sama..bacci takeyi"...gaba dayansu suka mike tareda bin bayanshi zuwa upstairs...har dakin Layla suka shiga..tana kwance kan gado tana baccinta hankali kwance...ummi ta karasa kan gadon da sauri ta zauna..har ta Kai hanu zata tashi Laylan sai ta fasa..snn ta dawo da kallonta ga Taheer tace"kai kodai ciki garta ne..inba hakaba to wnn baccin dun na meye"...Taheer ya zare idanu yana kallon ummin kmr zaisa kuka yace"haba ummi ciki Kuma ana zaune qlou"...ummi bata sakebi ta kanshi ba ta shiga tashin Layla daga baccin...a hankali ya fara bude idanunta har ta saukesu kan ummin...sai ta mike zaune da sauri tana fadin"ummi yaushe kukazo"...maimakon ummi ta amsa mata sai tace"ke me yake damunki ne haka..ciwon me kikeyi"...a hankali Layla tace"marana ke ciwo ummi..jiya ko bacci banyiba kmr zan mutu wlh"...ummi tace"tooh ciwon mara Kuma..Kai ba ance ana dainawa idan anyi aure ba"...ta karasa mgnr idonta kan Taheer da har yanxu ke tsaye...ya dan dukar da Kai snn yace"ana denawa mana..itama zata nasan zata Dena kawai lokaci ne baiyiba"...umma dake zaune gefen gadon itama tace Mata"sannu Layla..Allah dai ya rabaki da wnn wahalan"...ummi tace"Ameen"..sai Kuma ta mike ta shiga bin dakin da kallo tace"to har yanxu dai banga datti cikin gidan naku ba...Ina sane nace Aisha kar ta sanar daku zamuzo don inaso inga wainar da kuke soyawa"...babu Wanda ya tanka ta acikinsu...suna gani ta bude bayi ta leqa snn ta sake fitowa ta fita daga dakin...umma girgiza kai tace"Hajia Yaya ikon Allah"...sai Kuma ta dawo da kallonta kan Taheer tace"zafa muyi mgn son"...Taheer na dubansta shima yace"to muje dakina umma"...bata sake mgn ba ta mike..shi Kuma ya karasa inda Layla take..yai kasa da murya yana ce Mata"koma kicigaba da baccinki baby..yanxun nn zamu dawo"...ba musu kuwa ta koma ta sake kwanciya..shi kuma hadda rufeta da duvet snn yabi bayan umma da har ta riga ta fita daga dakin...suna shiga dakinshi in a serious tone umma tace"fadamin tsakaninka da Allah.. yarinyar nn ajiyeta kawai kayi kana kallonta koh..har yanxu bakayi hankali ka dena cutar kanka ba koh"...dan murmushi ya saki yana shafa Kai..yasan dama da kyar idan umma bata ganoba...a hankali yace"umma ni tausayinta nakeji wlh..she's too young for that..ko 18 fa bata karasa b..."tun bai karasa ba umma ta katseshi da fadin"rufemin baki da Allah..da can baka San she's too young dinba sai yanxu..haka zaka ajiyeta kana kallo knn kai bazaka tausayama kanka ba..idan Kuma da gaske bakada lfyn sai ka fada a nema maka magani"...da sauri yace"wlh lfyna qlou umma..kawai banso tasha wahala ne"...this time muryan umma a hankali tace"ka gwammace Kai kayita Shan wahalan knn...wane irin so kakema yarinyar nn ne Taheer da baka ganin komai sai ita...ko kanka baka dubawa sai ita..wane irin abune wnn fisabilillahi sai kace shanyayye"...jiki a sanyaye ya Dora kanshi kan kafadan umma...murya can kasa yace"wlh umma ni kaina ban san irin son da nake Mata ba...inajin zuciyata kmr babu komai a ciki sai ita..duk wani abu da zai dameta yana daga mun hankali fiyeda yanda zakiyi tunani..shiyasa nake hakuri sbd bazan iya jure ganin tana Shan wahala ba umma"...ajiyar zuciya mai karfi umma ta sauke kafin a hankali tace"nidai duk da haka bai kamata ka ringa cutar da kanka ba Taheer..she is your wife afterall..ba wanda zaiyi questioning dinka kan duk abunda zai faru tsakaninku"...ya dago kanshi zaiyi mgn sai ga Layla ta shigo dakin...ya mike da sauri ya rikota yana fadin"meya fito dake baby..bakijin mgn koh"...ta lagabe kai tana cewa"naji sauki fa daddy..ummi ce take nemanku"...umma najin haka ta mike suka fita daga dakin...Taheer na rikeda hanun Layla suka sauka kasa...ummi dake zaune parlor tace"Allah ya taimakeku banga wani abun da ba daidai ba a gidan..yau da naci mutuncinku wlh"...Taheer na murmushi bayan sun zauna yace"baby fa yanxu har girki takeyi ummi"...wata harara ummi ta maka mai tace"yause ka maidani kakar ka ban saniba"...Layla ma dariya tace"Allah da gske yake ummi..ko jiya ma ni nayi girki na da kaina"..dan tabe baki ummi tayi tace"da yake girkin lokaci daya ake koyanshi ba"...Taheer yace"vidoes take downloading a YouTube tana gani ummi..Kuma sunayin online classes"...cikeda fara'a ummi ta kalli Layla tace"Dan Allah da gaske"... Layla ta daga kai itama tana murmushi...umma ma murmushin tayi kafin tace"to ko ku fa..amma ace mace ta zauna bata iya girki ba Kuma bazata koyaba ai da matsala"...tana rufe baki ummi tace"gane min hanya dai Aisha..da duk tasan da wnn din ta ringa yi mana iskanci..da kin zauna baki koya dinba kanki Zaki cuta ai..Allah na tuba mazan nn na yanxu da ba shedan su akeyi ba..kina zaune zaije ya dankaro maki kishiya tazo ta kwace maki shi"...Taheer ya rausaya kai yace"Kai ummi..yanxu hadda ni cikin Wanda bazaa sheda din ba"..."hadda Kai Mana..ko kai sunanka mace ne ba namiji ba..duk mazan yanxu halinsu daya ai..sai dai wani yafi wani amma gabaki dayanku ba tabbas garesku ba"...Layla taji gabanta ya Fadi da furucin ummi...idan bata manta ba irin mgnr da Hanna ma ta fada knn...kenan da gaske ne maza basuda tabbas din..ita kuwa idan daddy ya dena sonta ko ya Kara auren wata ai ta gama yawo..tasan har ta rasu bazata samu Wanda zaiyi Mata irin son da yake Mata ba..

🤍Dr.TAHEER🤍Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon