chapter twenty two

1.1K 79 4
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

22

The following day Layla ta tashida zazzabi mai zafi...ummi duk ta rikice ta rasa yanda zatayi da ita...dama duk take rashin lfy to Taheer ne mai jinya...shi zaiyi Mata komai ita ummi saidai dan abinda baa rasaba...gashi sai kuka take Mata anyi anyi tayi shiru taki...dama shi kadai ne ya iya handling dinta gashi kuma yanxu wnn abun ya shigo tsakani...tun dare take ayyana ko kiranshi zatayi ya dubata sai wata zuciyar Kuma ta hanata...ganin dashi ta kwana ummi ta yanke hukunci suje asibiti kawai...ta riko hanun Layla suka fito daga dakinta...Nafisa na tsaye tana jiransu...hanunta rikeda car key..sai umma dake parlor itama tana jiransu...ummi na rikeda ita suka fita daga parlon.. Mama hawwa kadai suka Bari a gidan zata kulada yara...

Suna fita Taheer na fitowa daga part dinshi...ya bisu da kallo ganin zasu shiga mota..cikin ranshi yana tunanin Ina zasuje haka...bai San lokacinda ya nufi inda suke da sauri ba har Yana dan hadawa da gudu...ganin yanda ummi ke rikeda Layla kadai ya san cewa something is wrong...daidai ummi ta sata a mota..tana kokarin shiga itama kawai ta ganshi a gabanta...yana shafa kai yace"am...umm..me..me yake...damunta..ummi?...wani kallo ummi ta zabga mai tareda jan tsaki tace"bani wuri in wuce"...ya rausayar da kai tamkar zai Mata kuka yace"ummi don Allah me yake damunta...kawai fadamin zakiyi sai in baki drugs ki bata"...ummi murmushin takaici ta saki tana kallonshi tace"you have some nerves...bazaka bani wuri in wuce ba saina gaura maka mari a wurin...waye ya ja Mata ciwon idan ba Kai ba..ka saurari haduwa na dakai  bazaiyi maka kyau ba wlh...now bani hanya in wuce"...a hankali ya sake cewa"ummi to at least ko hijabi a bata tasa mana..bai kamata taje wani wurin da wadan nn kayan ba"...ganin kallonda ummin kemai bai sake cewa komai ba ya matsa Mata ta bude motan ta shiga...Yana tsaye yana kallo Nafisa taja motar suka fita daga gidan...da sauri ya nufi tashi motar shima ya shiga..yai Mata key snn ya bi bayansu.

A hankali yake tafiya don baiso sugane yana binsu...gaba daya he's worried about her..meyasa ummi zata hanashi dubata...snn meyasa zaa barta ta fita da mayafi kadai..ko hula fa babu a kanta..almost rabin gashinta duk a waje.

Tafiyan almost 13 mins sukayi yaga sun shiga wani private hospital...yai kasake kawai Yana kallon motarsu daya shiga ciki...yanzu ummi ta gwammace ta kawota wani katon banza ya dubata a kan shi ya dubata...laifi ne don yace yanson Layla ko laifinshi ne don an daura musu aure bata saniba...gaba daya he's becoming more angry than before...bai shiga da motan ciki ba yai parking nan waje snn ya fita ya shiga cikin clinic din...ya sauke ajiyar zuciya daya tuna mai clinic din is his colleague..so at least zai nemi alfarmar a barshi ya dubata and zai samu.

Suna shiga reception ummi ta nemi wuri ta zauna tareda rike Layla a jikinta...umma da Nafisa Kuma suka tafi don bude Mata file...Taheer kam cikin wasu mutane da yaga zasu shiga ciki ya shiga..Yana tsakiyarsu suka shiga wurin...Allah ya taimaka dai ba Wanda ya ganshi a cikinsu... Kai tsaye ya wuce office din abokin nashi...yana kokarin yin knocking sai ga abokin nashi ya fito daga office din...ya wara ido yana kallon Taheer din yace"what a suprise..yau Dr.Taheer ne a clinic dina"... Taheer yai murmushi yace"wlh nine Dr.Umar...wani alfarma nake nema wurinka plss"...Dr.Umar yace"ok mu shiga daga ciki"..
Saida suka shiga suka zauna snn Taheer yace"you know..matata ce aka kawota clinic din nn yanzu..batada lfy and ummi na fushi dani..taki bari in dubata..shine nakeso plss ka Bari in dubata da kaina"...Dr.umar ya daga Kai snn yace"bakada problem Dr...yanzu dama fita zanyi so In na fita zan turo maka ita..saika dubata a nan"...da sauri Taheer yace"yawwa friend...na gode sosae"...Dr.Umar na murmushi ya fita daga office din....ya samu su ummi a reception ko file din ma basu bude ba yace"ummi kece a clinic Dina yau"...ummi na kallonshi tace"wlh nice Dan nn..kaga yarinyace ba lfy wlh"...Dr.umar yace"ba matsala ummi taje office dina ta jirani..yanxu zan dawo sai in dubata...abokin Taheer ne ni ai"...ummi na murmushi tace"Allah sarki..bari muje office din toh"..da sauri dr.umar yace"No ummi ita kadai zataje ai...kinsan yanda yanayin aikin namu yake..in ana bukatar wani abu sai a kiraki"...ummi ba don taso ba ta koma ta zauna snn tace"to shknn"..dr.umar na murmushi ya kalli Layla yace"yawwa baby muje koh"...ba musu Layla ta shiga gaba yana binta a baya..da kyar take tafiya..saida sukaje har kofar office dinshi snn yace"ki shiga ciki ki jirani..ynxu zan dawo"...ba tareda ta kawo komai a ranta ba bude kofar ta shiga...tana cin karo da Taheer ta juya a rikice ta shiga kokarin bude kofar zata fita...ya karaso inda take da sauri yasama kofar key...sai ta durkushe a wurin tareda sakin kuka...Taheer ya risina ya kamota da sauri...yasa hanu ya toshe Mata bakin...ganin zata tara mai jama'a...ta runtse idanunta gam..kirjinta sai sama da kasa yakeyi...Taheer yai tsai yana kallon yanda ta zabura daga ganinshi...duk sai yaji he hates himself daya furta cewar yana sonta...da bai fadaba duk da bazaayi hakan ba...ya kama hanunta a hankali ya zaunar da ita kan kujera...shima ya zauna Yana kallonta da kyau yace"baby am very sorry plss...ki yafemin dn Allah..nasan I was too selfish but wlh sonda nake maki ne duk ya janyo haka...kiyi hakuri ki dena kukan nn..I promise zan sawwake maki tunda baki Sona...i don't want to be seeing you like this...don Allah stop crying and tell me abunda ke damunki"...Layla dai bata bar kukan da takeyi ba..Kuma bata bude idanunta ba...yana kallon gashinta da rabinshi ke waje yace"why did you come out like this...Ina hijab dinki"...Layla kukanta kawai take batace komai ba...a hankali ya durkusa nan gabanta..ya kamo hannayenta ya rike cikin nashi...murya a raunane yace"zaki fasamin zuciya baby...don Allah ki dena kuka...you are making me feel guilty"...ta tsaida kukan nata tareda zare hanunta dake cikin nashi...ta goge tears din dake idonta Kuma har yanxu bata bude idon ba...Taheer ya mike tareda komawa inda yake ya zauna idonshi a kanta yace"yanxu Ina ke maki ciwo"..."Kai na"ta fada a takaice...yace"bayanshi Kuma sai me"...ta sake cewa"zazzabi"...Taheer yai shiru kawai...Yana kallon yanda take mgn without looking at him...bai taba tunanin akwai rana da zatazo..wai baby taji batason ganinshi ba...lokaci daya zuciyarshi ta sake karyewa...sai yaji kmr ya rushe da kuka...itama da yake so kmr zai mutu ba sonshi takeyi ba..inaga su ummi Kuma..shi dama yasan wnn abune mai kmr wuya...he thinks he's going to divorce her kawai if that will make he r happy...he always wants to see her happy...ya daure ya kakalo murmushi snn yace"shknn inda ke maki ciwo"...ta daga mai Kai kawai...yace"alright don Allah ki jirani a nan..zanje in siyo drugs in kawo maki"...ta sake daga kai...shi Kuma ya juya ya fita..Saida yai locking dinta ta waje snn ya tafi..don bai yadda da itaba...Yana zuwa pharmacy ya siya drugs din da yakeso snn ya koma office din a gaggauce...ya bude kofar ya shiga...tana nn zaune inda ya barta..ko idanun bata bude ba..da gaske ko ganinshi bata sonyi...jiki a sanyaye ya karasa tareda daukan pen kan table...ya zana Mata prescription na drugs din a jiki snn a hankali ya Mika Mata ledan yace"take"...ta miko hannu ya Dora Mata ledan a Kai snn ta mike tsaye...har takai bakin kofa taji yace"don Allah kar ki cema ummi ni na dubaki...and kar ki kara fita without wearing hijab pls "...ta daga Kai kawai alaman toh snn ta fice daga office din...Taheer ya koma ya zauna tareda dafa kanshi da hannayenshi...wnn shi ake Kira tsaka mai wuya...gaba daya duniyar yaji ta fice mai a rai...komai ya denajin dadinshi.

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now