chapter twenty four

1.2K 81 5
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

24

Porthacourt...

farkon zuwansu Layla ba wani sakewa tayi a gidan ba...don ba wai tana zuwa sosae bane tinda su suna yawan zuwa Abuja...ga Kuma batun ta da Taheer da har yanxu take fatan wataran a tasheta ace mafarki tayi...amma daga baya ganin yanda duk suke kula da ita..kowa naji da ita...Mami..Abba..da siblings din nata..sai ta ware...ta shiga sabgoginta kmr ba abunda ya faru..dukda mgnr na nn cikin ranta but  ta dena bari ya dameta yanxu.

Idan tace bata missing Taheer kam tayi karya...she is really missing him and taki tayi admitting tana missing din nashi...tunda suke dashi bata taba tafiyan sati ba...snn ko ita tayi tafiyan ko shi yayi..always suna kan waya dashi..Amma yanxu 2 whole weeks ko massage babu daga gareshi...duk yanda suke nan nan da ita..gani take ba wani kulawa suke bata sosae ba...duk ba Wanda ya iya kula da ita kmr daddynta...shi kadai ne ya iya kula da ita sosae...duk dare haka zatazo ta samu Nafisa tace"Mami don Allah kimin addu'a zanyi bacci"..and Nafisa will be like"ke adduan ne baki iya da kanki ba dole sai anyi maki...ko kannenki ba Wanda bai iyama kanshi addu'a ba sai ke...tsabar sangarta"...Layla saidai ta turo baki kawai...ita ba haka daddy yake Mata ba..

Yau ma sun dawo daga outing gaba dayansu...kmr yanda suka saba duk weekend idan abbansu na gida...to zaice duk su shirya zasu fita yawo...yau ma tun safe suka fita sai yanxu suke dawowa.

Da dare bayan sun gama dinner Layla ta samu abbansu a parlor tace"Abba ni inaso in dawo nan da zama gaba daya...don Allah ka Kira ummi kawai kace mata ba sai na koma Abuja ba zanci gaba da zamana a nan"...abban nasu na kallonta da mamaki yace"meyasa kikace haka Layla...meyasa bakison zama dasu yanxu"...Layla ta turo baki tace"Abba ni kawai banason komawa ne"...abban yace"bazai yiwu ba..karatunki Kuma ya zaai dashi"..da sauri tace"Abba to ba sai a nema min wani school din in farayi a nn ba..ai bamu riga mun fara lectures ba dama"... strictly yace"kar in sakeji kinyi wnn mgr Layla...ko da da bakida aure bamu da ikon da zamu dakko ki muce ki dawo nan da zama...bare Kuma yanxu da kike matar aure..wnn ba hurumin mu bane"...Layla har ta fara hawaye tace"Abba to ba kune kuka haifeni b...bata karasa ba Nafisa dake zaune kusada minjin nata tana kallonsu ta make Mata bakin...tana Mata mugun kallo tace"kika sake cewa mune Muka haifeki sai naci ubanki wlh..wato duk mgnr da nake fada maki bakiji koh...Taheer din da babu abinda baiyi mikiba a rayuwa shi kikema wnn Wulakancin...sbd kinga Yana sonki koh"...Layla da har ta fara hawaye tace"Mami wai ya zaayi ace daddy ne zai aureni..wlh Mami ni ban tabamai kallon komai ba face mahaifi..ya zaai ace inyi zaman aure dashi bayan ni ba kallon haka nake mai ba"...Nafisa zatai mgn abbansu yace"kyaleta...tashi kije Layla kar Kuma in sakejin wnn mgnr a bakinki"...Layla bata sake mgn ba ta mike tareda barin parlon...Saida ta fita ya dubi Nafisa snn yace"bai zama lallai ta fahimci abunda kike nufi ba yanxu tunda ranta a bace yake..ki ringa binta a hankali kina Mata nasiha.. InshaAllah zata hakura..amma a yanxu tana bukatar space"...ajiyar zuciya kawai Nafisa ta sauke..tana tausayawa Dan uwantane sosae.

Abuja..

Tun da Taheer yazo office yau bai samu hutawa ba...kasancewar Monday ne so sunada lots of patients...yana zaune akai knocking office dinshi...a hankali yace"come in"...Sameera ta turo kofan ta shigo idonta a kanshi...Taheer na kallonta da mamaki yace"Sameera..meya kawoki office dina Kuma"... Sameera ta nemi wuri ta zauna tareda ajiye bag dinta kan table dake gabanshi tace"saboda Ina sonka doctor...bazan iya hakura da Kai ba wlh..Ina sonka har yanxu"...mamaki sosae ya sake kama Taheer still idonshi a kanta yace"amma na fada maki na riga nayi aure Sameera...bazan iya sake wani auren ba shiyasa ma nace na fasa aurenki"..yana rufe baki Sameera tace"meyasa bazaka iya Kara auren ba doctor..Haram ne idan ka auri Mata biyu"...Taheer ya dafe goshi..bai San ya zaiyi Mata bayani ta fahimta ba...ta sake cewa"mgn nakeyi fa doctor"...ya dago yana kallonta yace"sbd bazan iya adalci tsakininki da itaba shiyasa...koda na aureki Sameera bazakiji dadin zama dani ba tunda zuciyata ita takeso bake ba"...Sameera taji wani kishi ya lullubeta..idonta har sun ciko hawaye tace"wacece ita doctor..wace macen da kakeyima irin wnn so haka..me tafini dashi da bazaka iya daidaita soyayyata da tata ba"...Taheer ya runtse ido yanajin yanda tausayinta ke ratsashi..bazai ce yasan me takeji game dashi ba but yasan me akeji idan kanason mutum shi Kuma wnn mutumin baya sonka...Sameera ta taso daga inda take tareda durkusawa nan gabanshi...tana hawaye tace"na rokeka da girman Allah ka taimaka ka aureni doctor..can't you understand..I love you with all my heart"...da sauri Taheer ya mike itama ya kamata ya mikar da ita tsaye...idanunshi cikin nata yace"don Allah Sameera kiyi hakuri..mgnr so tsakanina dake a barta..kona aureki Sameera bazaki tabajin dadin zama Dani ba..kiyi hakuri idan mgnr Dana fada ya bata maki rai..akwai maza da yawa a duniya Sameera..Zaki iya auran duk Wanda kike so Amma Ni"...ya shiga girgiza Kai snn yace"kiyi hakuri kawai..I can't"...Sameera ta share tears dinta snn ta dauki bag dinta tana kallonshi tace"shknn doctor..na gode sosae"...bata jira jin abinda zai fadaba ta fice a office din tareda banging kofar...cikin ranta ta kudira koma wacece yakeso haka..bazata bari su zauna lfy ba..yanda yace bazai iya auranta ba to duk duniya babu macen da ta isa ta zauna dashi...dole tayi bincike ta tabbatar da matar daya aura din..zasu gane shayi ma ruwa ne.

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now