chapter fourty four

1.6K 116 5
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

44

Suna isa gida yaran suka bude mota suka shiga ciki a guje..Taheer ya fito tareda zagayawa ya budema Layla itama ta fito...Nafeesa dake kallon abinda yakeyi tai murmushi kawai tana girgiza Kai..wai yarinya karama yakema wnn abun sai kace wata babba.. ta bude itama ta fito..tare suka nufi entrance din gidan..

Su ummi na zaune parlor da alama dama suna jiran zuwan nasu ne...yaran ne suka fara shiga snn suma suka shigo..Kai tsaye Nafeesa ta karasa inda ummi take ta bata kyakykyawar runguma tana fadin"fatan mun sameku lfy ummina"...itama ummi ta rungumeta tana cewa"lfy Lou muke Nafee"..sai Kuma ta saketa ta shiga dube dube tace"ina wnn mara mutuncin take"... Al'ameen ne yace"gata can a bayan daddy"...ummi tasa hanu ta janyo Hibba dake boye bayan Taheer tace"zo nan don gidanku..ke baki iya gaida mutane bane..duk yayyenki sun gaisheni kece mara kunya koh"...gaba daya suka sa dariya...bayan sun zauna gaba daya suka shiga gaisawa dasu ummin...Taheer ya mike ya fita tareda su Al'ameen suka shigo musu da kayansu ciki...daga nn Kuma suka nufi dinning sukayi dinner tare..sunayi suna dan taba hira..shikam Taheer kacokam hankalinshi na kan babynshi...kawai tunanin yanda yau zai kwana ba tareda itaba yakeyi...Anya kuwa zai iya..tunda akai bikinsu zuwa yanxu in ka cire case dinsu da AY bai taba kwana ba tareda itaba..ko a wancan karon ma yaji jiki balle yanxu da suka riga suka zama daya..duk sai yaji abincin ma ya fita a ranshi..Sam bai wani ci sosae ba ya mike tareda komawa parlor..
Bayan sun gama suma duk parlon suka koma..nan Kuma aka sake dasa sabon hira kmr irin sun shekara basu hadu ba...umma ce ta lurada yanda Taheer duk baida walwala sai tace"kai lafiyanka kuwa"..maimakon yayi mgn sai ya karyar mata da kai kmr karamin yaro.. exactly yanda yake mata idan yanaso ta tausaya mishi... murmushi kawai ummi tayi don tasan da kyar idan ba kan tafiyansu da Layla yake wnn abun ba...sai ta mike tareda kama hanunshi shima ya mike..tace"muje ka fadamin menene matsalanka"...haka Taheer ya shiga binta a baya kmr bindi...ummi da Nafee suka bisu da kallo..ummi na tabe baki tace"ai ko me zakayi saidai kayi wlh..baka isa ka hana yarinyar nn zuwa bikin 'yar uwarta ba"...Nafee tace"ummi hanata zuwa yayi"... still bakin ummi a tabe tace"yo meye banbancin abinda yake shirinyi da hanata zuwa din..wani wai bazamu tafi da itaba saidai in zaizo daurin aure ran asabar ya tafi da ita..ranan lahadi kuma ya sake dauko kafa ya dawo da ita..sbd ance mai na farajin tsoronshi"...Nafeesa dariya ta danyi kafin tace"Ummi da kin barshi Mana..matarshi ce fa"...itama harara ta samu daga wurin ummi tareda fadin"bai isaba wlh..ko zai mutu sai mun tafi da ita gobe"

Suna shiga daki umma ta zaunar dashi itama ta zauna snn tace mai"to inajinka..menene matsalan"...Saida ya narkar da murya kafin yace"umma dan Allah kicema ummi ba sai kun tafida baby ba..tsakani da Allah umma har tsawon kwana nawa akeso inyi ba tareda itaba..ni bazan iyaba wlh.. dn Allah kuje ku kadai abinku.. inyaso mu sai mu taho ranan Friday"...dariya umma ta saki dama tatsuniyar gizo ai baya wuce koki...ta kama kunnenshi da kyau snn tace"wato ko kunyana bakaji koh"...Taheer ya kama hanunta dake rikeda kunnen nashi yace"auchh umma akwai zafi"..."zafin nakeso kaji dama ai"umma ta fada tana sakin kunnen nashi...shiko yana shafa kunnen ya sake cewa"Allah umma da gaske nakeyi..yanxu gobe Wednesday ni kuma bazan zo bafa sai ranan Saturday.. seriously bazan iya spending 3 whole days without seeing her ba..do something plss"...da mamaki sosae umma ke dubanshi tace"ban san yaushe ka zama mara kunya haka ba wlh..ynxu kwana ukun kakema wnn abun sai kace shekara uku"...cikin zuciyarshi yace"umma bazaki gane bane"..a fili Kuma yace"nidai umma do something plss..ki taimaka kima ummi bayani"...umma ba tace komai ba Saida ta mike..tana kokarin fita daga dakin tace"to tashi muje ka fada Mata da bakinka"...Taheer ya zaro idanu waje yace"kema kinsan rufeni da fada zatayi"...umma tace"to shawaran da zan baka shine kawai kayi hakuri..tun jiya nace mata ta bari ku taho tareda ita amma taki yadda..Kuma kasan halin Yaya da kafiya..so gara ma ka sama ranka dangana tun yanxu"...tana gama mgn bata jira me zai ce ba ta fita daga dakin...Taheer ya shiga hargitsa gashin kanshi yayinda ya bita da ido har ta fita....da kyar ya mike shima ya fita daga dakin...Yana isa parlor ummi tace"Kai wai sai yaushe zaka tafi gida ne..dare na karayi fa"...tana rufe baki yace"a nan zan kwana ummi"...tana binshi da kallon mamaki yace"a nan zaka kwana Kuma"...Taheer ya daga mata Kai..ummi kmr zata sake mgn sai kuma ta fasa ta cigaba da hiran da sukeyi itada Nafeesa...shiko Taheer idonshi na kan Layla dake nunama su Al'ameen abu a wayanta ya fita daga parlon...Kai tsaye part dinshi ya nufa don da gaske bazai iya komawa yaje ya kwana gidanshi while ita Kuma tana nn gidan ba...da zaa mai adalci sai a turo mai ita ace suje su kwana tare amma yasan ba Wanda zaiyi hakan..Saida yaje part din nashi ya tuna bai amso key a wurin umma ba...dan tsaki yaja snn ya sake juyawa ya nufi part dinsu...wnn karon Al'ameen da Ramadhan kadai ya samu a parlor... yana dubansu yace"Ina baby take"...Ramadhan yace"ynxu ta shiga dakinta"...tun kafin Ramadhan ya rufe baki ya kama hanyar dakin nata da sauri...Yana budewa kuwa ya ganta a ciki ita kadai..tana kokarin cire kayan jikinta..."am one lucky man"ya fada yayinda yake karasawa kusa da ita...Layla na ganinshi ta zo inda yake tareda juya bayanta tace"daddy budemin zip dina plss"...baiyi mgn ba yasa hannu ya bude mata zip din..ta juya zata koma inda kayan nata suke kawai taji ya kamo waist dinta da both hands dinshi...ta juyo tana kallonshi a marairaice tace"daddy plss..kayana fa nakeso in cire"...still baice komai ba yasa hannu ya shiga cire mata rigan nata a hankali..ya zare both hands dinta daga ciki snn ya cire rigan gaba daya daga jikin nata..ya zama daga ita sai bra..sai Kuma skirt dinta...ya sake sunkuyawa a hankali ya bude zip din skirt din shima ya shiga janyeshi daga jikinta a nutse..saida ya saukeshi har kasa snn yasa hannu ya dagata sama cak..skirt din ya fita daga kafafunta snn ya ajiyeta gefe..ya risina tareda dauko skirt din sai ya karasa gefen gado dasu a hannunshi..ya zauna snn ya fara ninke Mata kayan..yana gamawa ya ajiyesu nn gefe snn ya maido da idanunshi kanta...tana nn tsaye kmr gunki daga ita sai pant da bra a jikinta tana binshi da idanu kawai..ita kanta tunanin yanda zata debi tsawon kwanaki haka ba tareda Shiba takeyi..ya riga ya sabar mata da kwanciya a jikinshi always...ta saba da yanda yake kulawa da ita kmr baby..ta saba tayita mai shagwaba yana biye mata..tasan definitely ba karamin missing dinshi zatayi ba...tana tsaka da tunanin kawai taji yayi sama da ita..Saida ya koma gefen gadon ya zauna snn ya dorata kan laps dinshi tareda rungumeta tsam a kirjinshi... idanuwanshi lumshe yana shaqan daddadan kamshin da gashinta ke fitarwa muryanshi a shake yace"baby plss..kar ki tafi ki barni don Allah..i can't live without you..kiyi wani abu plss"...muryanta very low itama tace"nima ban San me zanyiba daddy..am going to miss you too"...Taheer ya dago idanunshi da suka kada sukai jajir sbd wata wutar fitina dake cinshi...ya kamo fuskanta ya hada da tashi...still muryanshi can kasa ya sake cewa"kawai cewa zakiyi bazaki bisu ba shknn..kina fadan haka nasan ummi zata kyaleki..ko kinaso kije ki barni ni kadai ne"...ta girgiza mai kai a hankali...yace"then do something..kiyi wani abu indai ba so kike inyi sabuwar budurwa ba idan kin tafi"...da sauri ta bude idanunta tana kallonshi..ta tsuke baki kmr zata sa kuka tace"Allah ban yadda ba..kuma wlh kanayin budurwa na dena kulaka infact kwaso kayana ma zanyi in dawo nn gidan"...ta karasa mgnr tareda murguda dan bakinta da tun dazu Taheer yai kurii yana kallonshi..ya lumshe ido tareda dora lips dinshi kan nata..itama lumshe idanun nata tayi luf as tanajin dadin yanda yake sarrafa bakin nata..har ga Allah bata isa tace daddy is not romantic ba..he is extra romantic.. kawai dai tanajin zafin abinda yakeyi Mata kuma ga tsoro shiyasa bata cika sakin jiki har da zataji dadin abin da yakeyi din ba...sun dauki almost 10-12mins suna abu daya...da kyar Taheer ya raba bakinshi da nata gudun kar yakai limit dinda bazai iya controlling kanshi ba Kuma..yasan wani na iya shigowa dakin at any time so yayi stopping kanshi ba don yaso ba...rungumeta ya sakeyi a jikinshi yana sauke numfashi da sauri da sauri...idanuwanshi rufe yanajin tamkar ya zubar da hawaye yace"bazan iya spending almost a week ba tareda keba baby..I just can't..do something dn Allah"...Layla ta zame jikinta daga nashi..tana goge tears dake fitowa idonta tace"badai cewa kayi zaka sake budurwa ba..dena kulaka zanyi wlh"...ta karasa mgnr tana kokarin mikewa daga jikin nashi ya dawo da ita da sauri..ya sake matseta sosae..dukda he's emotional hakan bai hanashi dariya ba..duk tace ta dena kulashin nn dariya take bashi wlh..but he's happy she's jealous..at least yanxu yasan bashi kadai yake kishinta ba..itama tana kishinshi and he's happy to know that...Layla ta shiga mutsu mutsu tanason barin jikinshi..tana kuka tace"let go of me daddy..ka sakeni inyi tafiyana ni"... maimakon ya saketa sai ya sake Rungumeta gam...still yana smiling yace"ohk ohk naji..am sorry da wasa nake maki..kema dai kinsan bazan taba kallon wata mace da sunan so ba baby..not after inada kamarki..so stop crying kinji"...bata sake yin mgn ba..ta dai dena kukan da takeyi..a hankali tace"to ka sakeni insa Kaya kar wani yazo ya sameni a haka"...baiyi musu ba ya saketa snn ya mike zuwa inda kayanta suke...cotton dogon riga ya dauko mata armless mara nauyi..ya dawo inda take tareda kamota ya shiga sa mata rigan da kanshi..tayi shiru tana binshi da kallo har ya gama sa Mata..ya kamota tareda manna Mata kiss a forehead dinta yana fadin"you look gorgeous my baby..I love you"...Layla ta saki kasaitaccen murmushi itama tace"I love you more..yanxu kazo ka tafi daddy kaga ummi zata iya shigowa"...ya kama hanunta suka fita dakin yana cewa"baby muje ki tayani bacci dn Allah kinji"...ta zaro idanu tana dariya tace"Tabb..kanaso ummi tayi min kaca kaca knn"...shima dan dariyan ya saki jin abinda ta fada..wai kaca kaca...suna zuwa parlon suka samu duk sun dawo..su Al'ameen ne dai duka tafi daki suka kwanta...hanunta cikin nashi suka karasa ciki...ummi tabi hannayensu dake sarke da kallo kafin tace"ikon Allah..kai Kuma daga Ina..ba munyi sallama dakai ka tafi ka kwanta ba..me Kuma ya dawo dakai nn"...Taheer ya shafa goshi jin tambayoyin da ummi ke jero mai..sai kace ba ita ta rike mai matarshi ba...a zuciya yace"ki bani matata mana kiga bazaki sake ganin keyana ba sai garin Allah ya waye"..a zahiri Kuma ya nuna Layla da hanunshi cewa yai"Kaya na bata ta canza ummi..zamuje mu kwanta"...ummi ta zaro ido tace"la'ilaha illallahu muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasallam..kai wai meke damunka ne..meya shiga kanka haka..yanxu Taheer ko kunya babu kake duban tsabar idonmu kana wani cewa zakuje ku kwanta..to ka saketa snn ka wuce ka bar min parlor tun ban gaggala maka mari ba wlh..fitsararre kawai"...a hankali Taheer ya saki hannun Layla dake cikin nashi snn ya fita daga dakin..ko key din ma bai karba ba aka koroshi...saiya Kira umma a waya yace ta bada key din a kawo mai.
Bayan fitanshi Nafeesa da taji kunyan abinda ummi tayi mai...tana duban ummi tace"ummi da baki mai haka ba wlh..ni tausayi yake bani..kuma meye amfanin ajiyeta a nn tunda gashi yana gidan"...ummi tace"ni rashin kunya ne banso..dubi fa ya ketare mu yabi yarinyar nn har daki sbd bashida ta ido"...sai ta maida kallonta ga Layla dakejin kmr tasa kuka sbd abinda ummin tayi mai..tace"kema kuma kika biye mai sbd ba kunyan ne ya isheki ba koh"...batace komai ba sai ma mikewa da tayi ta koma daki abunta... ummi ta rakata da harara tana tabe baki tace"ba laifinki bane wlh..duk shi ya lalata ki da dabi'unshi..duk halayen Taheer ba wanda ta mance bata dauka ba..Allah ya shiryeku"...Nafeesa shiru kawai tayi hadda su tagumi tana kallon ummi da karfin hali...ita kuwa umma mikewa tayi tana dariya kasa kasa..ta tafi daki don dauko mai key din.

Washegari suna idar da sallahn asuba suka fara Shirin tafiya..Taheer ma tunda ya dawo daga masjid bai koma part dinshi ba..yanata kallonsu sunata shiryawa..saidai tunda ya zauna baiga Layla ba...su Al'ameen suka fita da kayayyakinsu suka Sanya a mota snn suka dawo..daidai lokacin Kuma ummi da Nafee suka fito cikin Shirin su..can saiga umma ma ta fito daga dakinta...yanata baza ido ya hangota ta fito daga dakinta..tana kokarin gyarama Hibba hulan dake kanta so bata kula dashi ba...Taheer yai shiru yana kallonta..tayi mai kyau sosae as always...lace ne a jikinta riga da skirt..ta yafa mayafinta golden yellow daya shiga da lace din nata...lokaci daya ya lumshe idonshi ya bude..yanajin kmr ya dauketa su gudu inda ba mai takura musu..sam bai son kowa ya kalleta a yanda tayi kyau din nn..wani kishi yaji ya tokareshi daya tuna gidan biki zataje..and Allah kadai yasan adadin mutanen da zasu kalleta...at this point sai yaji kmr ya sa kuka...a hankali ya juya ya fice daga dakin ba tareda sunyi notcing dinshi ba.

Yana nn zaune cikin motanshi ya rasa inda zaisa kanshi sbd bacin Rai suka fito...bai yi yunkurin tashi ba yaci gaba da zamanshi nn ciki...su Kuma suka karasa gaban motan da zasu tafi dashi..suka fara shiga..da yake family car ne so ta daukesu gaba daya...ummi..umma da Nafee suna baya..tsakiya Kuma Layla ce da Hibba sai Ramla da zasu tsaya gidanta su dauketa.. Al'ameen da Ramadhan kuma suna gaba...Layla sai wara idanu take tanason ganin ta inda zai bullo amma bashi ba alamarshi...gaba daya ta damu so take kawai ta sashi a idonta kafin su wuce...shiko yana cikin motanshi yana kallonsu..duk zuciyarshi a jagule yake..yaji kowa da komai ma na bashi haushi...a hankali ya fito daga motan tareda nufowa inda suke...

A cikin motan kuwa umma sai tambayanshi take amma ba Wanda ya ganshi..Saida ya karaso inda suke snn ya shiga gaida su umman fuska ba walwala.. Nafeesa taji tausayinshi ya sake kamata kwarai..wnn wane irin punishment ne ummi take mai haka...a hankali ya matsa inda Layla ke zaune itada Hibba...tunda yazo wurin take satan kallonshi tana mamakin meya bata mishi rai haka...shiko Taheer kallonta yake yanaso ya dan kakalo murmushi ko na karya ne amma kmr fuskan ne yake daurewa da kanshi..tsabar kishi duk ya rufeshi ita kanta yaji yana jin haushinta kan wnn dressing da tayi..gashi bai isa yayi mgn ba ummi ta haushi da fada...a hankali Layla tace"daddy ina kwana"...daga kanshi kawai yayi da kyar yace"lfy"..sai Kuma ya juya ga su ummi yace"Allah ya saukeku lfy"...bai jira jin me zasu fada ba ya bar wurin da sauri...Layla ta bishi da kallo tanajin yanda hawaye yake kokarin zubowa a face dinta...wnn fushin nashi definitely tasan akwai abinda ya faru..haka nn bazai dauki fushi ba tareda reason ba..to ko sbd ummi ta dage sai sunje da ita ne..Ummi ce tacema driver yaja mota su tafi...maigadi na bude musu gate suka fita daga gidan..

Haka Layla tayita sake sake har suka isa gidan Ramla suka dauketa snn suka kama hanya...har yanxu bata bar tunanin sudden change din nn nashi ba..why is he upset..duk sai taji tafiyan ma ya fita kanta gaba daya..Allah ya sani tanajin tsoro yayi sabuwar budurwa kmr yanda ya fada Mata.




Gsky Taheer nada Fans da yawa..kowa Dr kowa Dr..ko Laylan ma bata da Fans kmrshi..yace yana godia snn Yana gaida Fans dinshi na ko ina
a kasar nn🥰One Love❤️🌹



Mum Ashraf ✨

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now