chapter five

1.3K 79 1
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf✨

Wattpad@ummuashraf22

05

WAIWAYE...

Taheer Ibraheem Jakada shine cikakken sunanshi,mahaifinshi haifaffen garin kano ne hakama mahaifiyarshi mai suna Hajia Maryama.Lokacin da sukayi aure sun kwashi tsahon shekaru Allah bai basu haihuwa ba sai daga baya Allah ya kawo aka samu namiji aka Sanya mai suna Taheer bayanshi Kuma Allah bai sake basu wani ba.
Mahaifiyarshi wato maryama tana da qanwa wadda ke aure cikin garin kano itama mai suna Aisha.Su kadai iyayensu suka mutu suka bari hakan yasa suka matukar son junansu.
Taheer nada shekaru biyu a duniya itama Aisha ta haifo 'yarta mace aka sa Mata suna Nafeesa.Kasancewar gidajen su na kusa yasa Nafeesa kusan kullum gidan yayar mahaifiyarta take wuni wanda hakan ya haifar da soyayya mai karfi tsakaninsu da Nafeesan,suna sonta sosae snn suna kulawa da ita.
Nafeesa nada shekara daya Taheer Kuma nada uku a duniya mahaifinshi ya samu sauyin wurin aiki daga nn kano zuwa Abuja,wnn shine dalilin daya Sanya suka koma Abuja da zama saidai suna tsananin kewar nafeesa sbd sabon dake tsakaninsu,hakan yasa lokacinda ta isa yaye Aisha da mijinta suka yanke shawaran baiwa maryama ita hakan Kuma akayi domin da kanta taje har can Abuja ta Kai musu ita tareda alqawarin sun bar musu ita har abada,wannan shine dalilin dawowar nafisa hanun maryama wadda suke kirada ummi,nafisa bata taba neman wani abu ta rasa ba,daga ummi har abie suna sonta matuka hakama Taheer,dukda cewa suna yawan yin fada Amma hakan bai hanasu son junansu ba,tare sukeyin komai hatta boko da islamiyya tare aka sanyasu saidai Taheer yafita aji sbd ya Dan girme Mata.
Wannan kenan..
Bayan haihuwan Nafeesa Aisha ta sake haihuwan yara biyu,Sadiq da Kuma autarta Ramla,haka nn suna cigaba da zumunchi da yar uwarta duk da nisan dake tsakaninsu.

Lokacinda nafeesa ta kammala secondary school wani cousin dinta ta bangaren mahaifinta mai suna Awwal ya fito yana sonta,itama bata qishi ba ta amince,koda labarin soyayyar ya iske iyayensu sunyi farin ciki sosae domin da mahaifita da mahaifin shi Awwal din uwa daya uba daya suke.
Bayan shekara daya akayi aurensu lokacin tanada shekaru 20 cif a duniya Taheer Kuma yanada 22.Aka gama biki snn aka mika amarya nafeesa gidanta dake Lagos kasancewar mijin nata soja ne a can yake aiki.Bayan auren bata samu daman cigaba da karatu kmr yanda aka tsara ba sbd cikinda ta samu.Cikin nata nada 8 months aka tura Awwal wani course na watanni shidda a qasar Ukraine daga wurin aikinsu,wnn dalilin ya Sanya Nafeesa komawa Abuja har zuwa lokacinda zai dawo don bazai yiwu ya tafi da ita da tsohon cikiba.Ummi na kulawa da ita sosae hakama abie,suna bata kulawan da duk mai tsohon ciki take bukata,hakama Taheer,lokacin yana 300 level a university,yanada Kuma shekaru 23 a duniya nafeesa Kuma 21.
Watannin cikinta tara daidai ta haifi yarinyarta kyakywa son kowa kin Wanda ya rasa,tunda Taheer ya Dora idanu kan yarinyar yaji Yana sonta sosae.Bayan an sanar da Awwal haihuwan yayi farin ciki sosae snn yace ya wakilta abie yayi mata huduba da sunan ummi wato Maryam,ummi tayi farin ciki sosae da wnn Kara da aka Mata,hakan kuwa akayi ranar suna aka Sanya Mata suna Maryam ummi tace sai dinga kiranta da Layla.
Layla ta kasance yarinya lafiyayya hakan yasa takeda farin jini da Kuma shiga ran mutane,Taheer bai tabajin soyayya irin Wanda yakema yarinyar nn ba yanajinta tamkar 'yar da ya Haifa a cikinshi,wani lokacin har missing lectures dinshi yakeyi sbd ita,kawai ya zauna gida yayita wasa da ita,hakan yasa Layla ta saba dashi sosae har ta ganeshi don Yana zuwa wuri zata fara dariya tana miko mai hannu wato ya dauketa,,Saida Layla tayi wata biyar a duniya snn mahaifinta ya dawo,ba karamin bacin rai sukayi da komawan nafeesa gidanta ba sbd sunyi missing Layla sosae,ita kanta ummi ynxu kusan duk son da takema nafeesan ne ya dawo kan laylan.

A gurguje plss...

Layla nada shekara daya Allah ya karbi ran abie wato mahaifin Taheer,sunji mutuwanshi sosae,amma kmr yanda Allah ke Sanya mantuwa irin wnn a zukatan mutane haka suka fara rage damuwa har suka warware gaba daya.

Layla nada watanni 20 aka kawota yaye Abuja,daga ummi har Taheer sai aka kasa gane wanda yafi farin cikin zuwan nata,shi kanshi mahaifin Layla ya tabbatarda soyayyan da sukema Layla is real musamman Taheer da yakega ko Dan da ya Haifa iyakan soyayyan da zaiyi mai knn.
Bayan watanni biyu aka sake tura Awwal wani course din a China na tsahon shekaru shidda,,wnn al'amari ba karamin daga hankulansu yayi ba sbd suna ganin kmr bazasu iya rabuwa da Layla har na tsahon 6 years ba Amma ga mamakinsu lokacinda sukazo yi mus sallama sai Awwal yace bazasu tafi da Layla ba sbd sunga irin kaunan da suke Mata,don haka ya bar musu ita halak malak snn har abada bazai taba nuna kanshi matsayin wai shi ya haifi Layla ba,ya bar ma Taheer har abada,sunyi farin ciki sosae musamman Taheer da bai iya cikakken 3 hours ba tareda Layla ba,wnn dalilin ya sake  karfafa zumunchi a tsakaninsu,hatta iyayen Awwal basu nuna rashin amincewansu ga hakan ba,daga nan Abuja suka je kano sukayi sallama dasu umma snn suka je Dutse inda mahaifin shi Awwal din yake suka musu sallama bayan dawowansu da sati daya suka tafi zuwa qasar China.

Layla na samun kulawa sosae,ta sake sabawa da Taheer snn tayi mishi farin sani da ko bacci takeyi tanajin muryanshi zata tashi,wani lokacin in suna wasansu ummi saidai taita kallonsu tana ayyana irin sonda Taheer keyima laylan,sai takega kmr ma yafita sonta,sau tari sai tayi da gske snn zai tafi sch Yana dawowa Kuma zasu Dora inda suka tsaya,tun tana hanshi idan yace Layla zata kwana tareda shi harta hakura,ya zamana tare suke kwana da ita,shike Mata komai,ya Mata wanka ya shiryata ya bata abinci har goyata yakeyi ya sata tayi bacci,duk ta fara rashin lfy kuwa tamkar tare suke jinyan don shima komai nashi tsayawa yake cak har sai yaga ta warke ta koma normal,koda ta fara mgn da sunanshi ta fara,shi ya koya mata ta ringa kiranshi daddy hakn kuma take Kiran nashi.
Shekaranta ukku ya sanyata makaranta kasancewar tanada wayo da Kuma surutu sosae,lokacin shima ya kammala first degree dinshi fannin medicine,ko a makarantan da sunanshi take amfani"Maryam Taheer Jakada"shi ke kaita school kullum snn time din tashi nayi zaije ya daukota wani lokacin ya maidata gida wani lokacin kuma su tafi yawo abunsu.
Bayan shekara uku nafeesa tazo hutu Nigeria,lokacin Kuma tana goyon yaronta kyakyawa mai suna Al'ameen,watanta daya ta koma China sbd ta fara karatu a Chan har ma ta kusa kammalawa.

Soyayya da Kuma shakuwa mai karfin gaske suka shiga tsakanin Taheer da Layla har zuwa ynxu soyayyan da uba zaima 'yarshi haka yake Mata,Yana sonta fiyeda tunanin mai karatu,haka itama tana sonshi fiyeda komai a duniya,tana damuwa duk al'amuranshi tun tana karamarta kmr yanda shima yake damuwa da nata.

Bayan wasu shekaru ukkun Nafeesa suka dawo Nigeria,lokacin ta sake haifan wani yaron bayan Al'ameen,mai suna Ramadhan,wnn karon maimakon Lagos sai suka koma porthacourt sakamakon transfer da akamai.bayan wasu shekaru ta sake haifan mace aka sa mata sunan Maman mahaifinta ake kiranta da Hibba.

Wannan kenan

Bayan shekaru Sha daya,abubuwan da dama sun faru ciki hadda auren Ramla 'yar autan umma tana nn zaune a abuja da Kuma sadiq shi Kuma Yana kano,sai kuma rasuwan mahaifinsu Nafeesa,da kammala secondary school din Layla lokacin she's 17 years old.Sai kammala first and second degree din Taheer duk fannin medicine ynxu haka yanada clinc nashi na kanshi nan cikin Abuja snn akwai different hospitals da yake visiting Har zuwa wnn lokacin kuma baiyi aure ba bai Kuma San lokacinda soyayyan da yakema Layla ya rikide ya koma so irin na aure ba bayan bashida hope at all.

Follow n vote on Wattpad@ummuashraf22

Mum Ashraf ✨

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now